← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 171

Sashe 50

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Anty Dije ranan da maigidanta yabugo mata yana fada mata,
Jin maganar tayi kamar a mafarki, alokacin,wani irin ihun murna tayi tana cewa Alhamdullaha, Alhamdullah,
Allah mun gode ma,
Joseph ya musulunta, maryam wace har takawo kofan falo alijacin taja tai tsaye,
Musuluntafa Anty, kikace,
Wanan kasurgumin Arne ai yayi nisa ko,
Subbahanallah Maryam bari mana, musulmi ne fa yanzu shima

Yau ba yawa kuyi hakkuri pls,👏👏👏👏👏

ZEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
3⃣2⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,

Abu, kamar wasa magana tafara zagaye gari, cewa Joseph ya musulunta,
Duk inda dan IBO yake cikin garin kwantagora da kewaye hankalin su ya tashi sosai,
Don su agare su wanan mugun labari don in, su na son mutuwar su to suna son jin irin wanan labarin,
Hakalin yan church din su Joseph yai matukar tashi sosai,,
Meeting suka hada duk wani elder dake a church din ya halarci wanan taron,
Batare da sanin Mr Ema ba wanda, sam baiyar da cewa dan shi na ita wanan abin ba,
Saboda su kaf tarahin su basu da yan uwa, musulmai, balle ace danshi ya shiga islama,
Sun wakilta wasu daga cikin su da zasu tafi har gurin Joseph din su samay shi face to face suji ta bakin shi,
Saidai sun sha bam,bam da Joseph din don yau yabar Abuja zuwa Lagos gurin kakar shi,
Sun yi kokarin bincike gurin maigadin shi amma basu gane komai ba don haka suka dawo da mamarai a ran su,
Shiko Yusuf ya isa Lagos lafiya da yake tafiyan jirgine,
Barci yayi sosai bayan isar shi sai musalin sha, biyu da rabi yafarka,
Inda yashiga bayi yai wanka tare da dauro alwala don sallah azuhur,
Key din motar shi ya dauka zuwa wani massalaci dake cikin unguwar na su,
Tare da shi aka gabatar da sallah azuhur, na wanan ranan,
Ibrahim wanda sai yamma yake dawo,wa daga gurin koyon computer da yake zuwa,
Yadawo cike da murnan ganin Joseph a yazo gari don yasan cewa ganin shi alheri ne babba,
Amma sai yaji Joseph cikkn yaren IBO yana ce mai yatashi su tafi masallaci kada su rasa jam,i,
Kamar a farki yaji zancen Joseph din don bai taba tsan manin haka ba daga gare shi,
Dashi akai jam,i Ibrahim wanda duk imani da,mamaki ya kashe,shi
Saida yakasa tambaya don bai san ta ina zai bullo mai ba,
Yusuf nagama addu,an da yadaga hannuwan shi biyu sama yana,roko tun bayan sallamay sallar ta,su,
Ya,shafa a fuskan shi da gangar jikin shi baki daya,
Sai a lokacin, yadan waigo inda Ibrahim yai mutuwar zaune,
Hannu ya mika mai tankar yadda sunna ta tanadar wa musullumi yai wa dan uwanshi musulmi,
A, lokacin ne ya mike tare da jawo hannun Ibrahim suka fito daga cikin massalacin,
Cikin wani irin murya maikama da wanda kasala takama ya fara magana,
Ibrahim katayani gode ma ubangiji na daya nufe ni da bani ikon gane gaskiya,
Ibrahim baisan lokacin da ya,rungumay Yusuf ba zuwa jikin shi sai she,shekar kuka yafara,
Bayan shi Yusuf yadan fara bubugawa shima, yana dan fidda kwalla masu zafi a idon shi,
Murna yakamata kai min Ibrahim ba kuka ba a wanan lokacin,
Ibrahim cikin dasashiyar murya irin ta mai kuka yace mai Dad yasani kuwa,
Murmushi mai daci Yusuf, yayi wanda baikai ciki ba yace bai sani ba tukun, yai yar ajiyar zuciya, yace,
Amma ,zai sani soon insha Allah,
Ibrahim zan tafi da kaina in tunkari mahaifina da zance,,
Duk da nasan hakan zai shafi rayuwar shi ta fan,ni daban,daban,
Amma hakan ba zaisa in daina abinda nai niyad yiba don kaina,
Musuluntata bata, jeka nayika bace, Ibrahim,
Nayita ne don ra,ayin kaina daganin dacewar hakan,
Yanzu ma na fara zurfafa acikin ta har sai ranan da naji cewa banda sauran numfashi a duniya,
Don haka na shirya tunkarar duk wani kalubalin da zan samu dayin hakan
Kara rungumay shi Ibrahim din yayi yana mai cewa masha Allah Allah mungode ma ubangiji Allah ka karawa Annabi daraja da daukaka,
Yusuf din yakarba da fadin Ameen, tare da hannun Ibrahim don su shiga gida,
Saidai yaiwa Ibrahim kashedin fada ma su mama yace sai ya fara fada wa, mahaifin shi tukun,
Ibrahim yace ina mai baka goyon baya brother har zuwa lokacin da zasu gane gaskiyan ka akan hakan
Ibrahim ya matse hawayen da ya cika mai ido,, yadan kalli Yusuf yace komai ukuba ko tsanani brother kada kabar addinin ka,
Babana yadade yana maka fatan kasancewa a hakan saiga shi yau Allah ya karba masu addu,an su a cikin sauki,
Kayi irin musuluntar da ake fatan yin shi domin Allah badon ra,ayin wani abuba,
Bayan sun shiga cikin gidane maman Choima da har yanzu bata kaunar ganin Ibrahim atare da su, tai mai wani irin kallo na kaidin wa,
Saboda lokacin da Yusuf baya gari sam baya shiga gidan saboda ita,
A, tare sukaci abinci shida Ibrahim ranan ibrahim wanda bai damu da yadda maman Ejoma ke mai ba.
Chapter 50 · 0% Book details