← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 171

Sashe 81

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zaune yake a falon gidan shi yana kokarin balle bottom din rigar ta wuya,
A hankali yadauki kafar shi guda zuwa sama wani dan stol, din katako dake falon,
Bayan shi yamar a makatin kujerar a hankali yana mai sauke numfashi kamar wanda yagaji
Idon shi yadan lumshe a hankali, yana mai tunanen inda yafito,
Shidai yasan cewa yanzu musulmi yake mai sallah farilla biyar a kowace rana
Amma kuma ga yadda yaga al,adar bahaushe ko musulmi zai ce bai mai ba,
Saboda wanda bai tuba ba kafiri arne zasu ce mai suna mai nuna kyamar shi
Sai kuma gashi wani bakon al,amari da yake fuskan ta yanzu nuni da cewa, da ake mai wai tubabbe,
Murmushin bakin ciki yayi ido arufe wani irin mugun bacin rai yaji,
May ya rasa ? may ye bai yi daga fannin addini ?
May za,a iya gwada mashi a yanzu ?
Amma sai ga shi a cikn taro ba ko boyo ko kawaici, ake cewa ashe shine tubabben nan,
May kuma illar wanda ya tuba kawai, ya shiga cikin ku,
Shin may amfanin nunawa mutane hanyar tuba, da ake yi,
Sai kayi kuma adinga kyamar ka kamar wani mugun abu,
Karar wayar shi ce ta katse mai tunane Grandma ce ke magana dashi,
Bayan sun gai sun danyi hira kadan take tambayar shi ko yaushe zai dawo saboda wai, tana son suje gida gurin festival,
A fili ce mata yayi zai dawo zuwa weekend insha Allah sai su fara plan din tafiya,
Amna suna gama waya sai yai yar tsuki don in akwai abin da yai hating tun farko shine irin wanan bukin festival din,
Inda mata da maza zasu hadu adinga yin abubuwa tankar tsafi, a gaban wani halitta,
A gurin ake hada wasu aurataiyan inda nan samari da dama suke ganin yan matan da suke so, sai a kulla alakar aure,
Nocking din kofar shigowa yaji ana yi a lokacin abinda ya sa,shi mantawa da komai ke nan
Ya mike don yadiba yaga ko waye, ?
Aisha ce tare da Amina ,ko,wacen su tasha kwalliya cikin material dinkin buje da riga sun dane masu jiki,
Ga gashin kari sun kara sai kace, wasu diyan kafiran da suke cewa,
Hannun su duk an painte shi da ja kumba, ga wani eyelashes sun zuba,
Haka kawai sai yaji wani haushin ganin su a hakan,
Bakaramin godewa Allah yake yi duk ya tuna cewa wani abu bai taba shiga tsakanin shi da Aishan ba,
Kirjin su duk yawani bultso tagaban rigar su kusan duk rabin nonon su a fili yake
Sai dan gyalen da suka yarfa a wuyar su kamar sarka,
Takalmin su ba,a maganar tsinin shi saboda tsawon shi,
Kokarin shigowa da takalma suke yi amma sai ya dakatar da su da cewa,
Haba sai kace wa yanda basu san darajan gidan musulmi ba cewa sallah zata iya riskan ka,ako ina acikin gidan ka,
Ya cew Amina ki daina biyewa wanan pls yana mai nuna Aisha da hannu
Yace ita ta riga ta kuna bata gudun yin kauri sam,
Darita tai mashi a lokacin da take kokarin cire takalman ta, daga kofar,
Kokarin rungumashi takeyi
Amma sai yadan ture ta baya kadan yana mai ce mata baki da kunya fa ke,
Yanzu fa nagane cewa baka son inadan taba ka inji dumin jikin ka
Tafadi tana kokarin zama saman kujera dake fuskantar inda taga yana son zama,
Yaushe rabon da indan yi hugging din ka sai kawai jayewa,?
Cikin mamakin irin bushe fitilar ta yake kallon ta,
Sai dai bai iya ce mata komai ba yadan yi murmushi kawai, kamar yadda ya saba yi,
Mun,zo jiya baka nan na san cewa kana can gidan wanan munafukar sister karyan ka,
Ciki dakewar murya ce mata look bana son wanan halin sam wallahi may tai maki,
Ita warinki ce da zaki dinga yi mata haka,
Jifa maganar ta kawai nayi yanzu amma kana kokarin cimin mutunci akan ta,
Ai nasan duk plan din ta akan ka wallahi so take ta mallake ka ta aura maka wanan kaunar nata mai kama da bafullatanar Niger,
Kai, inji Amina wace maganar kawar nata yasa ta jin kunya a takaice,
Duk kallon inda Aminan take sukayi cikin wani irin magana take cewa aiko yarinyar nan kaunar Dijen Illita costume tana da kyau,
Ba ita bace, A,A ke nema saidai uwar shi ta hana shi, tace zata hada shi da yar uwar shi,
Yusuf wanda ya nuna bai wani damu da hiran da sukeyi ba don wayar shi ya hau latsa
Amma sai maganar cewa ba za,a bar A,A ya auri Maryam ya tsaya mai a rai,
Ba zai aure ta ba to may yake zuwa yi gurin ta ko yaushe
Gaskiya wanan maganar abin bincike ne sosai,
Kwance Aisha take sama kujerar tawani yi dai,daya da kafar ta,
Aisha ya ce cikin murya da tankar a tashi ba yau don yadda ya furta ta,
Look bana son irin wanan dabi,u sam wallahi hakan baida wani amfani a gare ki a matsayin ki na diya mace,
Bana son kina zuwa wanan gidan idan nazo kina min irn wanan rashin kamun kai, pls ?
Da yar mamaki ta mike zaune da niyar yi mai magana amma sai yadakatar da ita da hannu
Alamar bai son jin komai daga gareta again don tun da tazo batwi wani abin alheti ba,
Ganin yadda fuskan shi ta nuna ne yasa Amina cewa Aisha,
Ke ko gaskiya Aisha haka fa baida kyau wallahi,
Ita sister tawa da kike cewa ta karya tafi min ke sau dubu wallahi
Domin zama da ita alheri ne a gare ni sosai ba kadan ba
Ki fada min zama dake abin amfanin da na samu akai,
Tamike zaune da kyau dan yau jin maganar shi takwyi ba taushi,
Tai wani far da ido tace mai laifin waye idan baka samu karuwa daga gare ni ba,
Yawani kada kai ya ce, Allah yai min tsari da irin taimakon ki,
Zance wai za,a hafani fa kaunar anty kuma ki sani cewa zancen aure na ya kawoni wanan garin ganzu haka,
Daga haka bai kara magana ba yasa kai ya bar falon cike da kunar rai,
Kallon mamaki suke mashi don basu taba tunanen cewa zai iya rufe ido haka ba,
Maigadin shi tare da body guard din shi suka shi go falon suna ce masu zamu kulle gida kufita pls,
Ikon Allah inji Amina tace yanzu dan Allah har ma korar mu akeyi haka, ?

Yau kimanin wata biyu ke nan inda zancen Yusuf da Sadiya sai kara girma yakeyi,
Bayan har Aisha ta sa an binciko mata ko wace yarinya ce Yusuf ke shirin aure,
Tayi mamaki kwarai don jin abinda ta tuhuma gurin anty ba gaskiya bace,
Wanan shigowar don shirin azumi dake tafe yayi wa garin ,
Amma sai kuma ya samu cewa mahaifin shi baida lafiya
A gurin makwacin su yake ji wanda kusan ko yaushe yana fada mai abinda gidan suke aciki,
Gidan nasu ya tafi kai tsaye bayan ya iso inda ya samu duk mahaifin nashi ya,ramay tankar wanda ya
Duk yadda yaso yaiwa dan nashi cin fuska sai ya kasa saboda kwar jin da yai mai a idon shi so,sai,
Yusuf din ya murje ya zama wani matashi hamshaki, dagani basai an fada ma ba,
Da kanshi ya kai shi gurin likita don yadiba shi aga ko may ke damun shi,
Tsumu, tsumu ya na rike da hannun Yusuf din har gurin likita
Inda a karshe aka tabbatar masu cewa yana dauke hawan ji, ne,,
Sosai Yusuf yai ta mai magana cewa,ya daina wanan yawan tunanen, da yake yi kada yai mai illa,
Sai da ya tabbatar da cewa yasha duk wani da likita ya bashi kuma yai ma wa yan da ke a tare dashi magana akan su kula dashi, so,sai
Sai bayan tafiyar shi ne yan church din sukazo cikin fada,suna cewa wai may ya kawo shi, gurin mahaifin shi,
A gaskiya su sam ba, su yarda da wanan ba, tunda yace ba ya tare da su,
Don haka wai sai ya daina zuwa gidan nasu,
Chapter 81 · 0% Book details