← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 171

Sashe 63

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yusuf yanisa ya waiga inda yake tsaye a bakin window,
Yace a ranshi kida Dad zai kwace mai duk wani abu da ya mallaka bazai fita cikin addinin islama ba,
Shi yanzu yasan cewa yafi karfin duk wani barazana da mahaifin shi zai mai akan dukiya,
Kwana biyu kawai yayi da hutawa, ya shirya don zuwa ya dibo, kakarshi wace bai san halin da take ciki ba a yanzu,
Ba karamin tausayi matar yake ji ba a matsayin ta na wanda, ta rage mai yake gani kamar uwar shi,
Tana zaune ta mike kafa a saman wani tabarman roba, a gefen da dan inwa yakai acikin gidan nata ,
Sai ganin shi tayi kamar a mafarki don sam batayi tsan manin cewa zata kara ganin shi arayuwar taba ,
Tadade rungumay dashi a jikin ta tana kuka tana wani gwalanci irin na yare,
Sai kuma komay ta tuna tasake shi da sauri tana ta tatabashi kamar tana tuhumar ko ba shi bane a gabanta,
My child are still in that religion ?
Mumushi yayi ya jawo goshinta ya man,na da nashi yace mata
Even you mama you will joined me, very soon
Dan tura shi tayi baya yawuce tangal, tangal kamar zai fadi,
Dariya tabashi a yadda yaga tanayi don daga hannun ta tayi tana wani kewaya shi a saman kanta tana cewa over my death body,
Komawa tayi ta zauna tana wani bubuga kafa wai ita tayi fushi,
Direct wuce yayi zuwa cikin dan falon ta na ginar kasa wanda saboda tsufa har yana batun zubewa,
Photo mahaifiyar shi ce yai tozali da shi, wace ke saye da wani zanin irin na matan IBO,ta daura wani dankwali daurin gwagwaro,
Murmushi takeyi da aka dauke ta kamar zatai magana
Yadade yana kallon photo yana maiji dama ace ta musulunta ka fin ta mutu,
Shigowar grandmother, yasa,shi barin gurin zuwa saman tsofin kujerun dake falon,
Itama zama tayi saman kujerar dake gab dashi, tana mai mai kallo cikin da muwa,
Shine yafara magana yana mai tambayar ta may yasa ta dawo kauye da zama,
Bayan tasan cewa babu wani wanda zai kula da ita anan yanzu,
Yace ga gidan shi can abirni babu kowa aciki mai yai hana taje can ta zauna,
Saida mama tadan waiga kamar akwai wani gidan wanda zai ji abin da zata fadi alokacin,
Tadan kara gyarazaman ta har kusa dashi tace,
That your father is very wicked,
He can killed person, woo
Nan take sheda mai cewa bayan tafiyan shi taji mahaifin nashi na waya da wasu cewa a kama Joseph ai masa duk wani horo da ya dace dashi don yadawo cikin Christianity,
Murmushi yai mata don dama yasan cewa shine ke turowa ai mai wanan wulakancin,
A ranan Yusuf bai yarda ya kwana wanan dan kauyen da yar tsohuwar ba dawowa sukayi tare,
Inda taga duk gidan ya canza mata saboda gyare,gyaren da akayi wa gidan,
Sosai gidan ya canza mata cikin dan lokaci har ta rasa gane ko ina ne part din ta na da,,
Ganin Ejoma da tayi tazo taron ta yasa ta gane cewa lalai agidan shi suke,

Wanan karon sosai ya shirya ma shiga garin na kwantagora
Badon komai ba sai don ya tunkari mahaifin shi wanda ke ta yi mashi bita da kulli,
Motorcine har guda uku yatanada don wanan tafiyan,da yake son yi kafin ya fara harkokin gaban shi,
Saidai wanan karon ba,a gidan mahaifin shi zai saukaba kamar yadda ya saba,
Hotel lafiyayye aka kama masu tun kafin su iso garin,
Har abincin da zasu ci an tanadar masu shi, KB ne yai wanan hidimar,

Zaune take tana kwalliya a bakin mirror saboda tana expecting din zuwan A,Adin ta,
Muryarda taji yana sallama tuni zuciyar ta, ta tsinke
Zabura tayi saye a dan tsorace, tadan saurara ko kunnuwar take mata karya,
Bashi bane a zahiri don sam ba su tsan manin cewa zai zo a wanan lokacin ba,
Muryam Anty Dije ce ya kara tabbatar mata da cewa shi din dai ya shigo,
Inda taji Anty na tacewa sannu da zuwa Yusuf
Kaine tafe babu ko labari, zuwa balle a shirya ma,zuwan naka,
Wani murmushi yayi mai sauti yace bana son ku wahala ne ai shiya sa ban fada maki ba,
Sigar dayake magana kawai zai tabbatar ma da ya kara samun canji a rayuwa,
A,hankali yake karasowa zuwa inda anty take dauke da Abubakar a hannun ta,
Ya saye da wani yadi mai laushi baki ajikin shi sai wata yar jar hular dara dayasa wa kanshi,
Gadan gadan yanu yau,fi inda take da yaron dagani duk hankalin shi na gurin yaron, wanda bai taba gani ba, sai
Cak yadauki Abubakar yafara dan wasa dashi ,daidai gitowar Maryam wace kamshin ta kawai kawai, zai saka gane tafito,
A hankali ta iya furta mai sannu da zuwa,daga haka tasa kai da niyar fita kawai,
Gabantane yafadi saboda ganin yadda Yusuf ya canza gabadaya cikin lokaci guda,,,,,,,

ZEEE. MAKAWA
[3/7, 1:14 PM] ‪+234 803 381 3188‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
4⃣1⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA,

Yusuf ya canza gaba daya ya wani murje yayi fari sosai da yar jiki daidai shi,
Wasa ya keyiwa Abubakar yana cewa wanan little friend din bai sanni ba , ama baka kai abokina kyau ba,,
Muryan ta na rawa ta iya furtawa Anty ta cewa zata dan fita,
Sai,dai kuma Yusuf din yadan tare hanya ta daidai inda zata dan wuce, zuwa waje,
Yaro nai yai sallama yace wai ana sallama da Maryam a waje,
Maryam da ke shirin fita hanya kawai take nema takumaji muryan Anty ta nacewa dan Allah maryam dan dauko wa Yusuf kujerar roba a waje,
Maryam wace dama a cike take don tasan cewa A,A yagajine har ya turo yaro,
Don yana zaton ko ta manta dashi a waje saboda motocin da yagani a kofar gidan su yasa,shi, zaton baki sun masu yawa ne,
Batare da tai magana ta juya tanufi inda kujeru suke aje a,dan wani kwanar da fridge din su na waje yake,
Kanta ta kawar gefe har ta isa gaban shi,ta ajiye mai kujerar, cike da jin haushi ta aje mai daidai inda yake tsaye,
Yana yawan dagula mata kwanciyar hankalin ta idan ya na a gari,
Ya zauna a hankali yana mai cewa bissimillahi, azu,bikalamatillah tammah
Kafin Anty ta takara sata yin wani abin da saurin ta tabar, gurin,
Tana shan kwana suka hada ido da Yusuf yasakar mata wani tsadadden murmushi wanda duk duniya ba mai mata irin shi, sai Yusuf amma ta kasa gane ko ta may ye,
Saidai da yake tasan cewa, murmushi wani part ne na rayuwar shi sai kawai ta share zancen
Kanta kawai takawar gefe cike da kara jin haushin shi,
Kafin ta karasa ficewa sai ga muryan Anty Dije na cewa,
Ki dauko mai ko ruwa mana maryam kinsan cewa, ba wuta falon da zafi,
Murmushi da yafitar wanan karon mai sauti ce don har Anty taji shi,
Komawa tayi cikin wani irn bata rai kamar bata taba dariya ba arayuwar ta,
A cikin tire ta jero, kayan shan har da da su cup,
A gaban shi ta ajiye kayan, shan tasan cewa idan bata zuba mai ba Anty zata kara kwafsa mata dole badon taso ba ta dan duka don ta zuba mai,
Kamshin turaren BUSSHIRAH da ta shafa ya gauraye ma hanci har saida ya yar ajiyar zuciya,
Muryan yaron dazu ne ya ratso kunnen su, yakara sallama yana cewa wai yace tazo don ba dadewa zai yi ba,
A lokacin Maryam tai yunkurin ta mikewa, sai ji tayi yana cewa ta karbi Abubakar daga hannun shi, pls
Sosai suka shaki numfashin juna tare da hada idon su a lokaci guda,
Maryam ce tai saurin kauda kanta gefe tana mai jin wani irin abinda bata taba jin shi ba arayuwar ta,,
Babu shiri tabar gurin da sauri daga haka tafita zuwa kiran da A,A ke mata,
Chapter 63 · 0% Book details