← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 171

Sashe 69

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sai kusan bayan la,asar sosai A,A yazo asibiti cikin shigar shirt sky colour, da wando baki sai tie da yasa a wuyan shi kawai,
Maganar shi a gadarance yake yin shi yana mai nuna cewa shi din wani ne,
Tambayar mujin mama takeyi yasukabar har ciwo ya ci ta haka gasu ba wani nisa suke dashi ba da gari,
Yace ai yanzu ba,a wasa da ciwo komai kan,kantar shi,
Sai mijin mama yace to ko muna son zuwa asubiti da may zamu zo,
Ko yanzu aida taimakon Alhajin nan ne muka samu mukazo in bashi ba ai da saidai yadda Allah yayi kawai,
Kagashi nan da nan yagane cewa sai munzo asibiti ba na gida bane yanzuma gashi tasamu sauki,
Da har zamu koma sai shi Alhajin tace mu bari har gobe sai ta dan kara samun sauki,,
Lokacin jin tana ta cewa Alhaji Alhaji yasa shi waigawa gurin maryam wace ke dan rakube a gefen bango,
Yace waye yake magana halan sai cewa maryam tayi a hankali,
Yusuf ne, yakawo ta,
Nanata sunan yayi yace Yusuf,
Wani Yusuf ke nan, wai halan, ?
Tace mai Yusuf wanda ya musulunta mana, maizuwa gidan mu,
Ok Joseph ?
Kai kawai ta gyada mai alamar eh,
Mijin mama yace a,a a daba musulumi bane shi din,?
AA yace kafiri ne yazo ya musulun ta koda yake har yanzu bawai an yarda da musuluntar nashi ba ne ai,
Sai a lokacin maryam tadaga kai ta kalle shi saboda kalamin da ya fadi,
Sai mijin mama yace a,a kai ko may za,aiwa shakka aciki tunda dai yariga ya musulunta,
Mikewa yayi tsaye da kyau daga rankwafawar da yayi saman karfen gadon da mama take a kwance,
Yace Arne fa ko ya mysulunta ai ba abin yarda bane,
Jin kalamai da yakewa Yusuf ne sai taji kawai bataji dadin su ba sam,
Don haka sai, tadan duka ta dauko wani leda tana kokarin fita daga dakin
Ina zaki tsata mu tafi don gida nake son zuwa indan watsa ruwa wallahi duk nagaji,
A tare suka fita daga dakin inda ta takai mai zuwa gurin motar shi,
A nan suka dan tsaya suna hira a gagauce saboda ita ranan gata nan dai ne kawai,
Shigowar motar suce tare da su jibrin da wasu abokan shi yasa su duka kallon inda suka tsaida motocin su,.
Dakin suka shige gaba dayan su don su diba maijiki,
A,A bai kara wani lokaci ba ya ja motarshi yabar gurin tare da Alkawarin zai dawo ya kara diba ta,
Ba ai wani dadewa ba su jibrin suka fito amma ba da, Yusuf ba,
Tana son taje dakin amma, sai tana jiran su fito saboda duk mazane acikin dakin,

Kan ta na saman ciyar ta, ta dan duka tana tunane,
Bakomai take tunawa ba sai mutumin ta watau A,A
Wai shi wani irin mutum ne, hakana, ta kasa fahintar shi har yanzu,
Gashi a fuska zakace ai baida matsala, sam,
Kafin ta karasa sai jin muryan mijin mama tayi yana cewa,
Maryam aida kinzo ya sauke ki gida ki dan huta tunda gamu nan da yawa ai,
Kamar tace a barta kawai sai taga musu da babba baida dadi,
Kuma ko banza tana da bukatar son watsa ruwa ajikinta, don tadan ji sanyi,
Tafe suke su biyu a motar, a hankali yake tuki don marance ya fara abin hawa sunyi yawa a hanyoyin,
Wani irin sanyi AC da kamshi ya gauraye motar, sai Qira,an dake tashi na Ahmed Suleiman kano,
Kamar daga sama taji muryan shi yana cewa,
Kiyiwa saurayin ki magana yadaina kirana da tubabbe pls,
Batare da ya kalleta ba yake magana, zaka zata mako bada ita yake magana ba,
Da,sauri Maryam, ta dan dube shi tankar zatai magana sai kuma ta fasa kawai tai shiru,,,
Idan kasa zai tsage zata shiga don kunya wanan maganar,
Wai ma ta ya ya ji wanan zancen, da akayi,, don dai baya nan a,lokacin,
A rau,nane ya, yace ban san may guy din nan ke ji dani ba wallahi,
Maryam dai har zuwa yanzu kala batace mai ba,
Sai dai jin da tayi, ya furzar da iska har sautin shi ya iso inda take,
Sai,dai,dai kofar gidan su,ya tsaya da motar shi, a yadda tagani duk rayuwar shi ya baci matuka,
Dan Allah kayi hakkuri ban san lokacin da ya fada ba,
Shima bai yi mata magana ba saidai ko karin Parker motar da yake yi,,
A hankali ta bude, kofar batare da kara kalon inda yake ba,,

ZEEE MAKAWA,,,

[3/12, 10:47 PM] ‪+234 813 139 5577‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
4⃣5⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,

Assalamu Alaikum yan uwa musulmai tare da fatan kuna liya,
Da plsn girman Allah yan uwa marubuta da makaranta kubani, dan hankalin ku dan pls
Wallahi muji tsoron Allah musan cewa wata rana zamu gammu a gaban shi,
In yanzu in anjima in gobe,
Anytime kwanan mu yakare,
Wallahi littafan batsa sunyi yawa yanzu sai mun kula mun gyara kada barna yai wa a sanadin rubutun mu,,, Amma idan maganata akwai laifi aciki ku yafe min pls,,,,👏👏👏👏👏

Alhamdullahi washegari mama tasamu sauki sosai don haka ta samu sallama daga likita amma zata dawo bayan kwana hudu,
Sam Yusuf bai nuna gajiyar shi ba sai ma kokarin nuna tankar shi dan gida ne cikin su,
Duk da bawai magana mai tsawo yake yi da su sosai ba amma zuwa yanzu sun dan fahinci halin shi,
Idan ka gan shi zaka dauka wulakanci ne sai ka dan zauna dashi zaka gane miskilanci ne,
Baban su maryam ne ya umarci Anty Dije da ta bar maryam ta, tafi ta kula da mahaifiyar ta tunda suna hutu, yanzu,
Don haka maryam wace, suke wasan boya da Yusuf tun jiya da ce tafadawa saurayin ta yafita harkan shi,
Sun isa kamfanin Bobi ana, shirin yin sallah azahar ,
Sai fitar su a cikin motar ne maryam taga, ashe duk kayan nan da yasaiya masu na amfani a asibiti suk sun kwaso abinsu sun zo da shi gida,
Sosai ta jin,jina mai saboda bakaramin namijin kokari yayi ba gurin ceto mata mahaifiya daga halaka
Da sauri maryam tashiga don ta gyara dakin mahaifiyar nata, inda sauran matan gidan ke ta mata sannu ya jiki,
Saidai may turus maryam taja ta tsaya saboda ganin wani irin dindimay,may katifa sabo fil a cikin ledar shi,
Da mamaki takarasa gurin inda daya dafa cikin matan ke sheda mata cewa, ai daga can kwantagora akazo da shi ance na mamantace,
Ga sabon randar roba ta ruwa, ga kujerun roba farare guda uku, da filolin su,
Jiki ba kwari zuciya fam da tunane maryam ke aikin dakin,
Ko ba, a tambaya ba tasan cewa aikin Yusuf din ne haka,
Kafin wani lokaci dakin mama yakoma kamar wata yar birni, can,
Sai zuwa dare maryam ta samu dan hutu bayan ta tabbatar cewa mahaifiyar ta tadan yi,wanka tasha magani,
Washegari da safe maryam na idar da sallah, asuba bata zauna ba fitowa tayi don taimakawa kishiyar mama da wasu aiyuka,
Saida ta tabbatar tagama komai ta koma daki don ta taimakawa mahaifiyar ta,
Kafin gari ya karasa haske duk maryam ta kammala komai a nata fan,nin,
Matan kauyen sai shigowa sukeyi da sunan gaida mama da jiki,
Amma azahiri gulma ke kawo su don wasu basu ko iya boye gulman su sai su dinga latsa katifa ko taba wani abu ace irin na wance na wance ne,,,,,
Chapter 69 · 0% Book details