← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 171

Sashe 100

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cikin barci da sukeyi na safe mai dadi da shiga rai suke jin muryan Yusuf din sama, sama,
A hankali ta bude idon ta a dai,dai lokacin da takejin yana cewa anty yanzu zan tafi Abuja don an bugo min waya yau da safe cewa, Pipkin bai da lafiya,,
Kuma yaron bawai ya wani saba da sabuwar nani din shi ba,ne,
Don kusan zuwan Naimat, nan ne na dauko matar daga kauyen mu,daga haka sai,
A hankali kuma taji dan she,shekar kukan Naimat a bayan ta,
Cikin idon barci maryam ke kallon Naimat din inda a hankali tadan mike zaune,
Inda Naimat take zaune take kallon ta, wacce ke kokarin goge hawayen dake sin,tiri a idon ta,
Ganin maryam din ta farka,ne yasa ta juyowa inda take zaune suna fuskantar junan su,
Hannun maryam tariki a cikin kuka ta nace wa maryam din,
Maryam ina son yaron nan, bana son ya mutu wallahi,
Saboda na,sha wahala sosai akan shi zaman da, da ,ni akwai wasu muhinman abubuwa da nake tunawa, akai,
Maryam wace ido kwai ta kura mata a cikkin mamaki, take kallon, Naimat din don sam bata fahinci inda maganar ta ya dosa ba,
Sai kuma hankalin ta ya,koma falo su, inda taji Anty Dije na cewa bazan bari kabi hanya baka karya ba Yusuf kabari ko cooker,oth ne a, dan dama ma,ka
Daga Saman gadon tai ko,karin saukowa a lokacin kafin ta idda sauka taji muryan Anty cikin daga murya tana kiran ta,
Sam ta mance cewa kayan barci ne ajikin ta don haka ta nufo falon da sauri,
Riga da wandon kayan barci sabon kitson da akai mata na wevin "yan ritsi,ritsi, sunyi lub, lub a kanta , gwanin sha,awa,
Da sauri ta iso inda anty ke tsaye dauke da yaron ta,
Shi ko sarkin lakewa a jikin uwar shi, a hannnu, ta yake dauke yana son shan nono, yanzu
Itama Anty sai yanzu tasan cewa kiran da tai,ta kwadawa Maryam din yasa ta rudewa cikin barci ta fito a haka,
Zanin da ta jawo don ta dan daura a sama take kokarin daurawa akai tana fadin gani Anty,
Da sauri ya kara waro idon shi waje don sak kalan kayan da yaga mai cikin da yai mafarki ne dasu da asuba,
Don Allah hada heater ki dama wa Yusuf cookeroth da,sauri pls, inji Anty Dije,
Sai a lokacin maryam wace tagama daura zani saman kayan barci ta, ta kai kallon ta inda yake tsaye tace ,
Ina kwana a hankali,
Shima dai ansa mata yayi cikin rashin walwala da sauri maryam ta nufi hanyar zuwa kitchen, din
Wani irin mugun bugun zuciya yaji mafarkin ne ya fado mai a ran shi,
Kafin yan mintina har ta hado mai cikin wani bowl mai dan fadi tazubo mai saboda yai saurin shan iska,
Anty Dije ce tace dan juya mai ya sha iska don Allah kada ya makara,,
Fuskan shi a hade kamar wanda bai taba dariya ba a rayuwan shi,
Wai waye Pipkin din nan ta ke tambaya a cikin zuciyar ta,
Dukawa tayi daniyar tafara motsawa mai orth din,
Wani kamshi ya daki hancin shi wanda saida yadan kara kallon ta ta wutsiyar ido,
Mamaki yaji don yasan daga barci ta tashi tafito amma kuma take wanan kamshin haka ?
Kai wanan yariyar akwai tsabta da yawa idon shi ne ke kallon yadda har an gyara ko ina na gidan ko kamar ba,a bata ba,
Muryan maryan ce mai magana cikin sanyi take cewa
Ya Yusuf addu,an samun lafiya za ai mai kasan ciwo bautan Allah ne both babba da yaro,
Amma duk da haka akwai wasu magani da mukewa yara amfani da su sai ka tafi mai dasu adinga mai amfani dashi a gani,
Mikewa tayi don ganin kunun yai dan sanyi saboda tasan cewa baya shan abu mai sanyi shi,
Dakin Anty ta shiga sai gata tafito da kwalaben magani a hannun ta,
Kara durkusawa tayi gaban shi tana mai bayani guda guda yana dan kurba kunun dake a hannun shi vikin cup a hankali,
Idon shine suka sauka a gaban rigar barcin ta waiyazu ;billah
Da sauri yakau da kan shi gefe har takare mai bayanin cewa wanan man
Habbatussauda ce, wanan, Zaitun ne, sai kuma man Albasa a dinga hadawa da pure zuma,
Takare maganar nata da ce wa a hankali Allah ya bashi lafiya,
Ameen ya ce cikin jin dadi da irin nuna kulawar da tai mai,
Sai alokacin ta juya gurin da Anty Dije take zaune tana shayar da danta tace
Anty idan zan fita atuna min in sayo wasu a aje dan Allah,
Mamaki yaji cewa sayen maganin ma sukayi ashe,
Bai wani dauki lokaci ba ya mike yana kokarin gyara jikin shi inda yadan takure,
Naimat ce tafito, cikin damuwa duk da tayi na mijin kokari gurin saita kan ta saboda kada agane cewa tayi kuka,
Maryam wace ke tambayar Naimat a cikin kashe murya,
Pipkin din yaron waye shi ?
Murmushi kawai Naimat tai mata, batare da taba ta ansa ba,
Ànty Dije ce tace ke baki san yaron Naimat ba Abdulrahaman,
Wani irin kallon mamaki maryam kewa Naimat daga haka Yusuf yai masu sallama ya tafi,

Yusuf tuki yakeyi shi kadai a cikin mota sai sharara gudu ya ke yi,
A cikin nishadi yake tukin shi hankali kwance sai dai kuma zuciyar shi tana gurin da yake, tunane
Sai,dai a kai, akai, yana dan duba agogon hannun shi, sai kuma ya daga kai yadubi, hanya,

A gaskiya a yadda ya samu yaron yana jin jiki sosai,
Saboda duk da ya samu yana barci amma jikin shi gadau yake da zafi,
A hankali ya duka a gaban yaron yana mai dan taba mai jiki a hankali,,
Wayar shi ce tai kara alamar kira ya shigo mai, a lokacin,
Batare da ya mike ba daga inda yake yadauki wayan
MARYAM BLACK yagani a rubuce wani irin murmushi ne yadan subuce mai,
Assalamu Alaikum, tace cikin yar siririyar muryan ta,
Ansa mata yayi da wa,alaikissalam ,
Maryam na barku lafiya,
Ya Yusuf ya hanya ka kusa isa ko,
Ina gida Maryam,
Yana jin ta tana cewa yai har ya isa fa,?
Muryan anty yaji tana cewa Yusuf wallahi ka rage wanan yawan gudun naka fa,
Maryam ya ambaci sunan ta, cikin wani irin murya,
Naam ta ansa mai itama cikin rudewa da jin irin kiran da yai mata,
Ya maijikin tace mai cikin sanyin murya,
Nasamu yana barci, amma dai jikin shi da zafi sosai wallahi,
Ya Yusuf kasamu kyale ko towel, kasa a ruwa ka din ga tai maka mai, dashi kana dan goge mai jiki dashi,
Jikin zai mai sauki idan an gama saika bashi wanan man albasan da sauran su ya sha,
Sai kuma tai shiru bata kara cewa komai ba daga hakan jun shirun nasu yai yawa shiyasa yakatse da,cewa abashi Anty,
Zaune yake a bakin gadon da ruwa da wani farin towel,
A hankali ya ke matse ruwan da towel din ya kwaso,
Yana dan mannawa a jikin yaron dake kwance a saman gadon shi,
Nani Antonia ta na tsaye gefe guda ta dan rakube a bango tana kallon abin da yadace ace itace tayi amma sam rudewa ya hana ta yi tun farko, don da ace tayi da jikin yaron bai kai haka ba,

Sannu a hankalo ya bude idon shi ,ba su sauka ko ina ba sai a,saman fuskan Uncle din shi,
A hankali ya ce uncle, sai kuma yai dan murmushi,
Wani irin tausayin yaron nen ya kama shi yaro mai kyau ga wayo amma ace wai ya tashi babu uba,
Kai mutane ba su da tsoron Allah sam, ka haifi yaro sai kuma kaki shi,
Yanzu badon Allah ya nufi yaron da,zama gurin shi ba da haka zai tashi acikin addinin Christian,
Uncle yaron yace a lokacin da yake kokarin ganin cewa ya kai zaune,
Da sauri Yusuf yatare da hannun a haka yadan mike zaune yana dogare da bayan hannun Yusuf,din
Rugumay shi yayi a lokacin maman Choima ta shigo dakin da cikin tafiya irin na tsofi
Da harshen IBO take mai yadawo lafiya ya hanya,saboda bata san inda ya tafi ba,,
Nan take ce mai wai yaushe ne Ejoma zata dawo garin su da ta tafi,
Ita fa shiya sa tace, tun farko Ejoma taje da dan ta,
Gashi yanzun ta wuce tabar mutane da yaro ana mata wahala,
Kan shi na duke yana sauraren ta yana makale da yaron a jikin shi,
Yace Mama,aaa,,,,,mamaaaa will stop dis,
Abdul is my son pls,
Lokacin yaji dan yaron ya kara shige mai a jikin shi ,shima dai din kara rungumay yaron ya yi cikin jikin shi,
Sai da ya tab batar da cewa yaron yaci abinci ya koshi san nan yasa akai mai wanka ya kara bashi magani,
Zaune a bakin gadon shi yana kallon wayar shisai dai ji yakeyi kamar ya kira maryam a lokacin,
Saboda irin yadda yake jin kewar ganin ta a yau din,
A hankali ya maida idon shi ya lumshe ya fadi a fili she is beautiful,
And her skin is natural,
Kwance yakai ta baya saman mamakeken gadon shi yace
And very religious, wayan shi ce tai kara azaton shi maryam ce amma sai yaga Aisha, ce, ke kiran shi,
Aisha ya kara furtawa yau rabon da ta kira ahi tun lokacin da sukayi sa,in sa da ita akan sadiya,
Baikara kula ta ba ko yanzu kamar kada ya dauka amma sai ya daure yadauka,,
Sun yi gaisuwa na mutunci da shi sai kuma ta fara mai korafin wai ya shigo KG yaki neman ta har yadawo,
Zata ci gaba da magana yadakatar da ita da cewa Aisha na fada maki ba yauba cewa baza mu shirya ba,
Saboda duk halaiyan ki basuyi min ba san kwata,kwata bana son inga mace bata kamun kan ta,
Nayi dake ki daina amma kin kiya,,,,,,,,,,

SEENABU ZEEE MAKAWA
[3/28, 9:01 AM] 0mmer Farouk: .🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
6⃣2⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

IYA,KA, NA,ABBUD, WA IYA,KA,NAS,TA,INN
Chapter 100 · 0% Book details