← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 169 OF 171

Sashe 169

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sai bayan kwana biyu ne maryam taje gidan mahaifin ta don gaida matan uban ta,
Umma naganin irin yadda maryam ta koma a take wani kibiyan bakin ciki ya soki zuciyar ta
Kishin yadda yarinyar tawaye ta goge ta murje a lokaci guda,
Har saida takasa boye bacin ran ta alokacin don duk wanda ke gurin ya fahinci cewa rayuwan ta ya baci,
Safiya ta rako maryam din tazo gaida matan mahaifin ta din,
Tsaraban turamay da kudi dubu hamsin hamsi ta basu, su biyu,
Aiko kamar an kara tunzura umma ne a lokacin don irin yadda ta shiga wani hali,
A ranan bayan wucewan su maryam bayan baba yadawo ne rayuwan shi bai mai dadi ba,
Don masifa da jidali umma tasa mai wai dama don yai arziki da yarinya yadauke ta ya bayar gidan kafirai,
Irin suratan da tayi, wa mahaifin maryam a ranan saida dan dattijon yai kuka agaban iyalin shi,
Yadaga hannu sama yana cewa Ya Allah idan har na,bada wanan yarinyar don akan abinda duniyar ke zargina Ya Allah kai ne sheda akai Allah ka isar wa maryama da mahaifiyar ta,
Dayar matan baba ne tai karfin halin cewa assaha malam ai basai ka tsaya cewa hakana ba,
Don Allah yagani da kanshi kuma yasan dalilin ka na yin haka,
Don may har zaka damu da yan bakin ciki, Allah ne yai ma tashi irin baiwan ta wanan hanyan,
Aida mitum ya isa shi mai hassadane dasai yaki karban kyautan da akai mai yace bai so ,

Lokacin da maryam zasu koma ta tsaya garin mahaifiyar ta inda su ma akai masu kyauta ta musam man,
Anty Dije ta samawa maryam yan aiki mutum biyu da tsohuwa da yarinya,,
Yariyar diyar yar Uwale ce da mijin ta ya mutu yabar ta da yara bakwai shine uwale tai masu wanan hanyar,
Ita kuma tsohuwan bata taba haihuwa ba yar uwan dangin mahaifiyar maigidan Anty dije dinne,
Yarinyar zata zauna da maryam tankar yar uwan ta ne ita kuma matar yan aikin da yashafi maryam din kawai zatayi a gidan,
Sun tsaya garin minna gurin da suka ziyarci gidan su Suleiman,
Mahaifiyar shi taji dafi sosai inda take basu labarin irin kokarin dake ga Suleiman din
Dakuma irin karuwar da yasamu haduwan shi da Yusuf wanda a yanzu yake ji dashi tankar yayan shi,,,

Lafiya lau suka isa Abuja amma a cikin dare suka iso garin inda hurera da zinatu ke ta ware idon su gurin kallon wanan daular da Allah ya kawo su a ciki,,,,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA
[5/11, 3:29 PM] ‪+234 706 582 0685‬: Aa🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
1⃣0⃣0⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI

ALHAMDULLAHI RABBIL ALAMIN ARRAHAMANIN RAHIM👏👏👏👏👏👏
YA ALLAH NA GODEMA DAKA BANI IKON KAI WANAN LOKACIN DA HARNA KAI WANAN PAGES DIN,
KUSKUREN DA NAYI A CIKIN SA, YA ALLAH KA YAFE MUN 👏👏👏
NASADAUKAR DA WANAN LITTAFIN GA WAKALE FAMILY 212 KWANTAGORA, GABA DAYA SU,, YAN WANAN ZURIN ALLAH YA GAFARTAWA MAGABATAN MU WA YANDA SUKA SAURA ALLA KASAWA AL,AMARIN SU ALBARKA,,,,,👏👏👏👏

So, sai maryam din ke jin dadin zama da wayan nan yan rakiyan nata,
Furera da Zinatu maryam ta mai dasu tankar yan uwan ta na jini,
Hakan ne ya sasu jin dadi wurin uwar dakin nasu saboda sam shawaran ta da mama furera take yin shi,
Ita kuma zenatu tankar kaunar ta na ciki daya don komai cikin saukin kai maryam ke bin su,,
Bukin Safiya da umar sultan ya taso ga cikin Safiya yai mugun tsufa a lokacin don haka ba tasamu halartan bukin ba sai,dai dinner da akayi a Abuja ta samu zuwa,
Washegari da da yamma na kuda ya kama maryam din,
Zaman mama furere a gidan ya taimaki maryam don itace ta,gane cewa na kuda maryam keyi,
Yusuf takira da waya acikin cijewa take magana,
Yana zaune a office yaga kiran wayan maryam bai bata lokaci ba wurin daukan wayan,yana cewa,
Sweet maryam, ya dai, kina lafiya, ?
Uncle banda lafiya kawai ta iya cewa ta kashe wayan,
Hankalin yusuf yai mumunan tashi dajin yadda maryam tai magana,
Kamar yai tsuntsuwa ya taso a lokacin, maman choima duk ta rude saboda irin yadda taga yare suna yi,
Amma ga maryam sai in idan nakudan ya cije ta zata murde baki,
Addu,a takeyi a bakin ta irin yadda aka koya ma su a islamiyar su,
Kafin Yusuf yazo har driver ya kai su asibiti ko don bazasu iya jiran shi ba,
Allah ya sauketa lafiya ta haifi diyar ta mace mai kama da ubanta sak,
Yarinyar farace tas da ita ga hanci da suma baki wulk kamar na maryam sai dar,daran ido irin na maryam din,
Daidai fito da yarinyar Yusuf ya karaso asibitin cikin rudewa amma yana ganin ana mikawa mama furera yarinyar a hannun ta sai ya sake murmushi,
Hamdala da istigifar yake tayi a cikin bakin shi har ya karaso gurin cikin rudewa,
Maman Choima ta daga hannun ta sama tana cewa press the Lord,
Sai kuma ta hau rera wakan yabo da godiya irin nasu, Christian,
Yarinyar ya karba ya nufi inda maman Choima take yana cewa mama,mama see my blood today woo,
Kara runguma yarinyar yayi a jikin shi tankar wanda za a kwace wa ita,,
Kunnuwan ta yakai daidai baki shi yai mata ikama kamar yadda Sunna ta umur ta,
Sai a lokacin ne ya dago kai inda mama furera take yake duba sai dai bata gurin,
Hakan yasa zuciyar shi gane cewa tana cikin dakin da maryam take a cikki,
A hankali ya tura kofan dakin maryam din tana kwance a aaman gado asibiti,
Idan badon dan fadawan da tayi ba bazaka ce itace ta haifi wanan dirkekiyar yarinyar ba,
Murmushi suka sakarwa junan su yana kokarin karasawa bakin gadon ne wata nurse ta shigo dakin dauke da abin allura a hannun ta,
Ce masu tayi, da su dan fita daga waje kadan har su gama da ita tukun,
Chapter 169 · 0% Book details