← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 171

Sashe 13

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tsaye yake yana waya da kanin shi, Samuel wanda ke zaune tare da baban su a kwantagora inda Samuel ke fada ma Joseph meeting din da elders sukayi a kan shi,
Yai mamaki matuka da jin zancen Samuel din don yasan cewa yana ikar kokarin shigurin ganin cewa ya kyautata wa Church din na su,
Badon komai ba saidon kawai ya kare martaban gidan su daga alumar su,
Cike da mamaki yasake tambayar Samuel labarin mahaifin su,
Dan shiru Samuel din yayi kadan kafin can,yace yana nan saidai gaskiya maganar tadan tayar mai da hankali,shi,
Kai kawai ya girgiza yana mai shafan fusakan shi in akwai abinda ya tsana yanzu shine yaga bacin ran mahaifin shi,,
Sallama yayi wa Samuel din yana mai jin haushi elders din na su, akan jefa mai mahaifi cikin damuwa,
Shin ina ma ruwan su dashi dazasu sa mai ido a harkokin shi,
Yasan cewa koda ya kira mahaifin shi ba wani maganar da zai ji a gamay da elders din,
A karshe ma yana iya ganin laifin Samuel da ya fada mai, zancen,
Tun yana tuna zancen har ya share maganar, gurin fridge ya nufa yadauko goran ruwa, ya tutula ma cikin shi,har saida ya zuke gora guda gaba daya ya wurgat da rubo, a dustbin,
Kiran wani Michael ne ya shigo mai a lokacin inda yake sheda mai cewa yason su hadu saboda maganar man Gas dayake son suyi a lokacin,
Michael mutum ne mai iyali shi duk da bawani babban mutum bane sosai,
Yasamu Michael da yaran shi suna wasan basketball, agidan shi
Yaran naganin shi sukayo wajen shida gudu suna mai oyoyo,
Rungumay su yai cikin jikin shi ya na dan shafa masu kumatun su,
Sun san zuwan shi gidan su alherine don haka ledar Sweet din da ya riko masu ya mika masu,
Murna da ihu suka hau yi suka shige cikin gidanan su binsu yayi da kallo
Nan take alkawarin da yaiwa Assalam ya fado mai arai,
Don yasan cewa yaro baya man,ta alkawari duk lokacin da yaga wanda yai mai alkawari bai cika ba sai ya tuna,,
Don haka ya kudurta a ranshi cewa da yabar gidan mic zai wuce yaiwa Assalam sayayan shi ne,,,,,,

ZEEE. MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
9⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

Yau gidan Anty Dije baka jin komai sai kamshin girke, girke ke tashi kala,kala,
Duk wanan kamshin anayin shi a kan maigidan da zaidawo yau daga gurin aikin shi can garin Lagos,
Tun jiya ya bugo masu waya yana mai sheda masu cewa yau zai iso, sanin da sukayi cewa ysna saman hanya,
Yasa su wanan girke girke da kara gyara gida duk da dai gidan nasu ko yau she fes yake,bazakace akwai yara agidan ba,
Bayan sun kammala aiyuman su ne sun gyara guri sai kuma,suka shiga gyaran jikin su,
Duk da zaman Iliyasu ma,aikacin custom ne hakan bai sa ya wadatar da matar shi da komai ba,
Don dai da ka ganta kasan cewa zaman hakkuri takeyi kawai, don babu wani kama na nuna wadata atare da ita,
Allah yasa mata hakkuri da dauri sosai don sam baka taba gane halin da take ciki,
Cikin wanan halin hakkurin da takeyi bai hana yan uwan mijin ta,sata gaba ba da fitina
Don su gani sukeyi ai duk wani bida na Iliyasu yana gurin Anty Dije da yan uwanta,
Idan suna wanan zancen bata bata ranta saidai tayi murmushi kawai,
Don takan ji dafin rashin gane sirinta da basuyi ba har suke ganin cewa komai na hannunta,
Basu san cewa dan uwan su ne mai laifi ba,
Harkokin shi kawai yake yi a can bariki abin shi,

Maryan zaune tana kwalliya a gaban madubi da ke kuryan dakin anty Dije
Wanda har in tana son yin kwalliya mai tsayi dole sai ta shiga har kuryan dakin na anty Dije,
Sauri take yi ta tafi karbo ma anty Dije dinkun nan ta a uguwar Rimaye,
Waje wata yar uwar maman su Anty Dije din don matar ta iya dinkin zamani sosai,
Atamfar code,viore ne mai ruwan makuba da milk, ajikin ta,
Dinkin riga da zani ce tai daurin baya ta kulle shi a tsakiyar baya,
Turaren Anty Dije tadan fesa kadan
, Saida tagama hada komai tadauko dan wani karamin hijabin ta, ta sa sai takalman Bella, da tasa, a kafar ta,
Cikin yar muryan nan nata take sallamar Anty Dije a hankali don gudun Issalam kada taji ta tace zata bita,
Don ance tayi sauri ta dawo, dawuri saboda kila dasu anty zatayi amfani
A gidan mama Asabe tasa mu bata karasa hada dinkin ba don haka tabukaci mama Asabe ta bugawa Anty Dije ways ta sanar mata cewa da dan saura kadan kafin a karasa,
Tana zaune tana jiran dinkin saiga wata budurwa yar gayu ta shigo gidan
Daganin yadda sukeyi da mama Asabe kasan sun saba sosai,
Inda maryam take zaune budurwar takalla tace ma mama Asabe
Asabe ina kika samo wanan yar budurwan mai kyauwo haka,
Saida mama Asabe tadan kalli gefen da maryan take zaune tana mai ci gaba da dinkinta tace,
Diya tace, tazo karban dinkin su ne
Kanyan anty da ake dinkawa tadan taba sanan ta kai zaune saman kujerar roba fara dake dakin da mama Asaben take dinki a ciki,
Turamay zani tafitar guda biyu masu ba,lain kyau daga cikin bakar ledar da tashigo da shi a hannu,
Kai inji mama Asabe amma dai wanan zanin akwai kyau wallahi kamar su sukayi kan su,
Budurwan tana wani ya mutse fuska tace niko kinga Asabe zanin bai suyi min kyau ba
Kodon bani kawai akayi shiyasa ban ga kyaun shi ba,
Mama tana dinki ta ce kedai yar rainin wayo ce taya za,a baki abu kice kin raina,
Amina halinki sai ke wallahi,
Ai ma, mutum abin arziki irin wanan zukakan zanuwar haka ki ce wai ke basuyi maki ba,
Gyalen da ta yafa ta kwabe, ta koma, daga ita sai wata yar rigar t,shirt ajikin ta,
Ta mike ta bude fridge din mama Asabe ta dauko roban ruwan Goje water tadan fara kwakwada,
Maryam dake zaune gefe tana mamaki da kallon ikon Allah,
A, ranta tace wanan duk cikin wayewa ne haka kuma,
Ka cire hijab a gidan mutane, idan maigidan yafado fa ya zatayi,
Muryan Amina yadawo da ita daga tunanen da takeyi
Amina ke cewa mama Asabe bayan ta gama shan ruwan da tadauko a fridge,
Tsaraban Aisha ne fa Aisha mama Asabe, ta tambaya da mamaki,
Ita fa inji Amina kinsan ta da,kwashe kwashe, wani dan Arne ta samu yake kashe mata kudi haka,
Arne fa inji mama Asabe mai dinki, Amina tace wallahi ke dai,
Niko bayerabe ne musullumi ai ban iya zama da shi balle iyamuri kirsta,
Mama Asabe tace ke ko indai musullumi ne ai ba matsala, tunda Allah bai hana aure a tsakani ba
Amma ace kirsta gaskiya abin baiyi ba,
Amina tai wani irin turo baki tana mai daga kafada da watsar da hannayen ta alamar nuna oho ba ruwan ta,
Mama Asabe tace amma dai Amina nagane zancen ki har da kushi a ciki
Nan gardama ya kaule masu tsakanin ita da mama Asabe
Daidai lokacin da mama tagama hada dinki tana kokarin nikewa tasa a cikin leda ta miko ma maryan, din,
Tamike tana mai ce madu sai anjimar ku, mama tace ku rage min tsarabar Lagos in ankawo maku
Dariya maryam tayi kawai ta ce to mama zan fada mata in naje,
Ganin motar Ya Iliyasu a kofar gida ya tabbatar mata da isowan shi, gari,
Cikin nuna farin ciki da jin dadi ya iso duk daxtasan cewa ba wai wani abu zaizo masu da shi na marmari ba,
Amma dai tana murna Allah yakawo masu shi lafiya
Yana zaune saman kujera rungumay da yaran shi ta shigo dan matsakaicin falon nasu,
Har kasata kai tana mai sannu da zuwa yai yar dariya yace little mummy ance min an aike ki ,
Tai mai anzo lafiya da murnan ta shima a cikin fara,a yake ansa mata,
Iyalin iliyasu sun cewa ko ba komai indai har yana gari suna cikin farin ciki a ko yaushe
Don gidan su yacika da baki masu zuwa da yan bukatun su akai akai,
Kasan cewar zukatan mutane ya mutu yanzu don ba,a maida roko bakin komai ba,
Sai kaga mutum magidanci bai aikin komai sai bin gida,jen masu dan abin hannu ana rokon su, na cefane,
Chapter 13 · 0% Book details