← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 171

Sashe 160

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasar Italy suka fara sauka inda Yusuf din zai tsaya don wasu harkokin business din shi,
Don haka bai samu wani enough time din zama da yar amaryan tashi ba so sai,
Wanan shiga da ficen da Yusuf yake faman yi a kasar Italy din ya jawo mai gagarumin nasaran samun cigaban ckamfunan shi sosai don sun samu nasar sa hannun jari a,wasu kamfunar kasar,
Ana gobe zasu bar kasar Italy din ne yadawo gida agajiye saboda aikin da suka sha guraren sa hannu,
Rungumay yake da coth din shi a hannu sai hannayen shi da yazube su cikin aljihunshi,
Wanka ya fada inda yafito yasamu maryam din cikin wani dogon riga mai hula,
Abinci tagabatar mai sai yadan tsankwara kadan yace ya koshi don shi yanzu girki inba na maryam bane sai dai yaci kawai,
Kokarin lalabanta yakeyi a lokacin amma sai maryam din tana kokarin zulewa,
Tsayawa yayi da mamaki yana kallon ta sai ce mai tayi ai ya kamata ya huta don taga yagaji ne yau
Cikin mamaki yace maryam karda ace kina nufin bazaki iya daukan dawainiya naba,
No no no kada kizamo min haka pls ban da ra,ayin yin mata biyu kin wadace a rayuwata maryam kidaure da duk wani bukatana, pls,
Indan har kin min haka kin min komai pls kin mai dani dan gata ke nan,
Murmushi maryam din tayi tace cikin yar dariya baka da matsala anan uncle,
Yaji dadin maganar ta don haka yace idan har haka gaskiyane ina son yau atabbatar min da honey moon nazo,
Dariya tayi don ta gane wayon manya yake son yai mata kawai ,
Yau kan ba honey moon tana batun gudu yajawo ta zuwa jikin shi yana dariya
Nan ya nemo bakinta ya manne da nashi a guri daya
Can wata duniyar suka lula aciki irin duniyar da baka gane haske da duhu,
Daga italy suka wuce kasar Hong Kong nan ma dai sun morewa rayuwar su kamar ba gobe, kuma,
Wanan tafiya yasa maryam kara shiga farin ciki wanda yamantar da ita duk wani shakku da damuwa,
Saura kwana biyu subar kasan maryam ta, tashi da zazzabi amma kuma baidauki lokaciba tasamu sauki,
Amma duk da haka saida Yusuf yakaita asibiti don adiba lafiyan ta sun gane gajiyane kawai yadan damay ta,
Sun jima sosai a Hong Kong din don maryam ta watsake sosai kafin subar kasar,
Yusuf cikin wanan tafiyan ne yai ma maryam set, din funitures ga gidajen shi uku na kwantagora Abuja sai Lagos,
Batare da sanin maryam din ba ya turo su gida Nigeria ya sa agyara mata ko ina,
Gurin Sonny yake kokarin zuwa da ita don su dan ganshi amma bazasu dade ba acan don zasu wuce Dubai ne daga can,
Maryam ta zama babban mace ta goge takara wani kyau da haske ga hips da ya wani baje mata abaya,
Kiran ta na "ya mace ya fito tsab ta zama classic lady, yanzu don ko ina zata iya shiga don takai,
Sai dai daga maryam har Yusuf din su na jin dar din zuwa gurin Sonny din,
Amma kuma Yusuf yana da bukatan zuwa kasan don haka dole su tafi garin,

ZEEE MAKAWA YELWA,
[5/5, 10:20 PM] ‪+234 703 055 6607‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
9⃣5⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI

JAMA,ATUL MUSLIMI RAMADAN MUBARAK
👏👏👏👏👏👏👏

Sun bar kasan Hong Kong cikin jin dadi da,walwala,
Ga wani irun mugun shakuwa da yashiga tsakanin,
Don kowa naji da dan uwar shi sosai,,
Idan Yusuf yana gida tilas maryam tana manne a jikin shi idan kuma yana office ne ko wurin wani business to waya ne akai,akai a tsakanin su,
Hakan yasa farin cikkin su kullun yana karuwa ne akoda yaushe godiya sukewa Allah,
Matsalan maryam yanzu guda ne shine yan uwan Yusuf da suka sasu a gaba,
Duk da ba yaren IBO maryam ke ji ba tana fahintar wasu abu a wasu lokutan,
Saboda basu iya magana cif da yare zalla sai sun jefa English a ciki musan man ma shi dan gogan nata,

Sun sauka South Korea amma sai Yusuf bai sauka a gidan Sonny ba,
A hotel mai kyau da tsada suka,sauka shi da black beauty din shi,
Tun shiga shi kasan yake sa ido ga yar amaryan shi wace a yanzu tazama mai wani wani sashi na rayuwar shi,
Saida ya dan huta kwana biyu sannan ya nemi Sonny din,
Sun yi murna sosai da ganin junar su a wanan lokacin
Duk da Sonny yasan cewa Yusuf bai shangiya amma sai da yai mai tayi shi,
Wani irin harar ya watsa mai tare da daure fuska Yusuf yace kokai ina fatan ka bar wanan akidar very soon
Dariya yadan yi mai kama da yake yadan ka da kan shi alamar da wuya hakan,
Kurba guda ya shanye cup guda ya kara zuba wani ya aje a gaban shi,
Zagayowa Sonny din yayi zuwa gaban Yusuf inda ya hau saman table ya zauna gab da Yusuf din,
Yusuf hankalin shi na ga wani takarda da yake duba na,wani harkan business wanda zai iya kawo gida Nigeria har a samu karuwa,
Muryan Sonny ce ta katse yana tambayar shi labarin garin da Sonny ya kai shi, a Nigeria,
Murmushi Yusuf yadan yi yace suma suna kewan shi ai,
Ina wanan Baby din nawa take yanzu ne ?
Tambayar ta tsayawa Yusuf cak amma ba wani shayi ko wani dari yace mai ta na nan,
Da sauri Sonny din ya dan waiga kamar wanda zai iya ganin maryam din a lokacin,
Sai kuma yakai wa Yusuf dan duka acikin yaren su na IBO yace kafaye tsokana Yusuf,
Yusuf a cikin daure fuska ya ce, ba wasa aciki tare muke yanzu haka da ita,
We haven married six months ago,
What's cikin daga murya Sonny din ke tambaya,
"Yes, of course"
Yusuf ya bashi ansa da hakan,
Cikin mamaki Sonny din yace yanzu kayi aure Man shi banda ko labari ban jiba ko ga,wani,
Takardan dake hannun shi ya dire saman table din yace, You now how my sweet religion is,
Basai munyi wani bidi,a ba zamu iya yin auren mu a cikin mutunci bukata kawai shedu su sheda hakan,
Hannun shi ya tafa raf raf raf sau uku ya ce congratulations,
Sai ya duko kan shi gab da kunnen Yusuf din ya ce,
You are the most lucky man ,
I ever meet in the world,
Maganar Sonny taba wa Yusuf mamaki sosai
Sonny din ya ce gaskiya nai maka murnan samun wanan yariyar a rayuwan ka,
Duk da dai kai ba,wai kadamu da mata bane balle kasan irin abin da na hango ga wanan yarinyar,
Amma yanzu tun da ta na gurin ka ,a sannu zaka gane ko waye ita,
Nagode kawai Yusuf din ya furta cikin kaguwa irin yadda abokin nashi ke santin matar shi a gaban shi haka,
Yusuf ne kau da hiran matar tashi daga bakin Sonny,
Harkar business suke tataunawa akai ta yadda abubuwa za su zo mai da sauki,
Sun dauki dogon lokaci a office din Yusuf din suna tataunawa akai,
Sai lokacin da Yusuf zai wuce ne Sonny yake tambayar shi inda maryam take don yazo su gaisa
Tare da cewa shi a matsayin shi na babban aminin shi zai hadawa Yusuf da maryam yar party na aure don duniya ta sheda,
Mamata boye ta nakeyi don bani son maza yan duniya masu halin dan akuya su sa mata ido,
Hararan shi Sonny din yayi yace kada ka dauke ni haka inda dai baka aure ta da duk yadda zan rabaka da ita zan yi don in more mata,
Kaji mara mutunci inji Yusuf ya harari Sonny din yace ya kamata ace kadaina wanan irin akidar ka samu family hakana pls,,
Murmushi Sonny yayi tare da bubuga kafadar Yusuf din,, yadan girgiza kan shi,
Sai da yaba da baya ya ce zan di ba acikin addini ko zan samu wace tai daidai dani,
Saboda a gaskiya bazan iya shiga addinin ku ba don naga kuna da tsananin bauta har sau nawa kuke bauta in a day,
Abinda Yusuf yariga yasani ne dama Sonny bazai taba musulun ta,
Koda yaso musuluntar aminin nashi ne don yasan idan ya auri maryam zata kokarta a kan shi, don yayi addini,
Sai yazu yake godewa Allah na rashin cutawa yar mutane da bai yi ba dakuma cutawa rayuwan shi kan shi,
Don dai Sonny bazai iya musulunci ba gashi ya kasa tsayi a Christianity balle musulunci mai akidoji,
Har hotel din da suka sauka Sonny yakai Yusuf sai dai bai shiga ba don adan buge yake alokacin,
Amma yai alkawarin zai kawo ma su ziyara zuwa gobe indan ya fito,

Washe gari ganin da Sonny yaiwa maryam din sai da ya tsorata sosai,
Don maryam din ga kyau, ga iya dressing ga zubi daganin ta ka ga matar manya ce,
Fatan jikin ta yai mata wani lub lub, tankar irin mantan Pakistan din na dakr cikin daula,
Ga natsuwa da kamala don komai nata a natse takeyin shi ba garaje,
Wanda hakan ke wani kara mata aji da class, a idon mai kallon ta,,
Sonny yai masu murnan auren da sukayi inda ya ba maryam din kyautan wani dan kit da kuma wani dan karami box,
Duk kan su sun san cewa kyautan Sonny ta bajinta ce a ko da yaushe,
Chapter 160 · 0% Book details