← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 171

Sashe 158

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Falo shi na sama yake zaune bayan ya dawo daga massalaci, kira,a yasa wanda duk inda kake a gidan zaka iya jin sautin,shi,
Cikin wani dongon riga da Yusuf yasayo mata maryam take rigar mai adon duwatsu har kusan kasan shi da wasu hannaye shara,shara tadaura dan kwalin rigan akan ta,
Laptop din shi agaban shi dagani tasan aiki yake acikin shi
Cup ne a hannun ta dauke da milk a cikin shi mai sanyi tasa dan wani marfi ta rufe,
Falon nashi ba kowa ke shigowa cikin shiba in bashi da ita ba yanzu,
Kusan yaune ranan farko da maryam din tafara samun shi a falon saboda ta fahinci cewa guri kamar inda yake samun natsuwa agida,
Tunda ya hango tafe sai yaji ya kasa yin aikin dake agaban shi sai kallon shi ya koma gare ta
Maryam wace tafe take acikin rausaya kamar zata karye don rangwada, amma ita batasan tana yi ba,,,,
Yusuf a zuciya, shi sai hamdallah ya keyiwa Allah daya bashi maryam a matsayin matar shi,
Haban shi ya rike da hannunshi kaman mai mamaki,
Kafafuwan shi suna mike saidai ya harde daya cikin daya,
Isowan maryam gaban shi yai daidai da sauke ajiyan zuciyan shi,
Cup din milk din da takawo mai ta dan aje saman stol din da ke gefen kujerar,
Mastawa tayi gab dashi tasa hannun ta ta cire mai hannun da ya tallabo haban shi dashi
Idon shi ya zubo acikin fuskan ta cikin murya mai sanyi yace mata,
Maryam a kullun na kasance tare dake sai in rasa irin godiyan da zan ma ubangijina da ya mallaka min ke a matsayin matar sunna na,
Kalan shi maryam tayi cikin natsuwa ta sake mai wani irin lalausar murmushi,
Don kokarin ta na isar da maganar da tazo mai dashi,
Gashi tun agida tasha alwashin rike mijin ta da,zuciya daya akarkashin yina nayi bari na bari,
Badon komai ba sai don cikawa mahaifinta burin shi na wanda shi kadai yasan dalilin bata Yusuf a matsayin mijinta
Saman hannun kujerar da yake takai zaune tadan kwanto da jikin ta saman kujerar ,
Ta ce cikin wani murya hmmm uncle ni ban ce nagode ma Allah da ya nufeni da zama matar ka aduniya har nake fatan a lahiran mu ,
Cikin sauri yatare ta da cewa in sha Allah maryam in Allah ya yarda,
Ameen ta ansa mai dashi,
Uncle a yanzu fa kai ne mutum mafi daraja a wurina,
Banda wanda yakai daraja a guna domin aljanna ta tana akarkashin kafan ka ne,
Gashi a sannu ka koyar dani sonka acikin dan lokaci kankani,
Banda wanda nake ji dashi nake son shi face kai mijina uban diya na ayanzu ban damu da duk wani abinda mutane ke cewa akan ka ba,
Tunda maryam ta fara jero maganar ta bata tsaya ba sai da takai karshe, batare da ta tsaya jin may zai ce ba,
Rugumota yayi zuwa cikin jikin shi saboda bai taba tsanmanin jin ko makaman cin wanan maganar daga bakin ta ba,
Sai gashi yau ita maryam ce da kanta take fadamai da bakinta,
Don haka zancen ya shiga zuciyar Yusuf sosai har takai ga ya kasa cewa komai sai binta da lalaba yake yi,
Itako maryam dama abinda take jira kenan taga cewa ta birkita mai lissafin shi kafin ta fara aiwatar da plan din ta
"Maryam! ya fadi sunan nata cikin wani yanayi sai kuma yaja bakin shi yai shiru ya kasa furta ko mai akai,
Wata kila kuma don bai da kalman da zai iya fada ne a lokacin,
Kara noke kanta tayi saman kirjin shi tace I love you uncle Yusuf,
Tare da kai bakinta acikin kunnuwan shi ta furta mai hakan,
Nan da nan jikin Yusuf din yadauki rawa tankar yau yafara sanin maryam din,
Hakan yaba maryam daman yimai wasu abubuwan da bai ma san ta iya ba, saboda takara cusa kanta gare shi kamar yadda kowace mace ke kokarin yi don mallakan mijin ta gare ta,
Lokaci mai tsawo suka dauka ita dashi acikin wani irin yanayi da ba zai yiwu a fade shi ba ,
Sannu a hankali maryam din ta dan fara zamay jikinta a cikin nashi,
Ta koma gefe guda tana kokarin sauke numfashin ta,
Sai a lokacin hankalin su yadan dawo suka tuna da gurin da suke
Cikin sauri maryam din tafara mikewa tsaye tana kokarin gyara gaban riganta da ya bude,
Sannan takai dan zaune saman kujera dake kusa da ita,
Yusuf wanda ke kwance saman floor plat dashi daga shi sai yar tree quiter dake a jikin shi,
Gyaran murya yayi yana miko mata hannu alamar ta daga shi daga kwancen,
Dariya tadan kama mashi don sai a lokacin ta tuna da milk din da takawo mai,
Cup din milk din tadauko tanufo shi dashi inda yake kwance tana cewa tashi ga milk kada yai sanyi baja sha ba,
Idon shi a lumshe lokacin cikin kasala yadan kai zaune yajingina bayan shi ga kujera
Bayan ta mika mai yadan kurba kadan sai ya lumshe idon shi,
Azaton shi madaran ce sahihiyar ta sai da ya kurba yaji bambamci a cikin shi,
Sald milk ne a ka hada wanda ke bada kamshin flavor mai dadi,
Cikin lumshe ido Yusuf yace waya koya maki wanan hadin little Mum ?
Sunan da yakirata yasata dan shiga wani yana saboda ya sa tatuna da abubuwa da dama da suka wuce,
Mai makon tabashi ansa sai cewa tayi hmmm inji Assalam ko ?
Gyara dan zaman ta tayi sanan tace Uncle dama ko ina son in dan roki wata alfarma a gare ka,
Cikin mamaki ya dago kan shi ya kalle ta yace alfarman ke nan maryam,
Don Allah so nakeyi a bude min kitchen dina daban sai in barwa su ukeria wancan din surika abincin su suda sauran masu aiki ,
Sai tai shiru alamar tana jiran jin ansar shi a lokacin,
Shiru yayi yana kallon cup din milk din dake hannun shi kamar mai nazarin wani abu,
Sai dayadan kara kuba milk din sanan yace ko so kike akoresu don banyi zaton zaki iya kai warhaka dasu ba don nasan ki da kyamar mara sallah,
Kunya maganar tashi taba don dai yagano inda maganar ta tadosa amma sai tadake tace ,aaa bana son akore su,kawai dai yamanto bani aiki da kayan su,,,,,,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA
[5/5, 9:14 PM] ‪+234 703 055 6607‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
9⃣4⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI
Chapter 158 · 0% Book details