← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 171

Sashe 8

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zaune take gaban mirrow tana dressing kusan duk abinda mace zata bukata na fente fuskan zamani ta na dashi a gurin,
Dogon rigar atamfa ce ajiye saman gadon ta gefe hade da dan kwalin shi da gyalen shi,,,
A hankali tadauko rigar ta zura a jikin ta, ta gyara tsayuwar rigar cifcif a jikin ta ,
Ta mika hannu ta dauko dankwalin ta fara daurawa a kan ta,
Batafi minti shidda ba taga komai takara feshe jikinta da turare,har zuwa gyalenta,
Kinsan da gyale da hijab sun fi daukar kamshi a kayan mace,
Saboda hatsari mace ta dinga shafa turare a jikin ta yana kawo wa mata breast cancer so sai, wlh,,,,
Amma idan kin dan sa wa top din ki is ok ko ina ki kabi zaki na kamshi so sai, har na wani lokaci (pls be aware)
Wasu takalma ta jawo wanda sukayi matching colour da gyalen ta, da yan kunen ta ,,,,
Tsaye take gaban mirrow tana kare wa kanta kallo,
A, lokacin wayar ta yai kara cikin sauri ta dauko murmushi tayi don ta san ta bata lokaci,
Haba Aisha kin san fa cewa ance ba makara don Allah kada kisa a rufe get ba mu shiga ba,
Daidai lokacin ta rufe kofar dakin ta, don gudun kada yan kan,nen ta su shiga mata cikin dakin suyi mata barna,
A kofan gidan nasu ta iske Amina kawar ta cikin motar saurayin ta suna jiran ta,
Baka jin komai a motar sai sautin kida dake tashi kamar kune mutum zai fashe,
Duk inda suka bi dule a waige su don jin,karar kidan motar da ya hayhake ko ina,
Tunda ta shiga motar gaisuwa kawai ya hadasu da saurayin Amina
Ba su tsaya ba sai wani mating wuri da aka killance a rubuta da manyar haruffa, kamar haka,
SAFARA MOTEL,,,,,,
Sai wasu yan kananin gloves da ke haska wanan rubutun yana bada launi kalakala,
Duk saurin da sukeyi sun makara don sun samu an rufe get, ko,,,
Komawa Aisha tayi baya tadan jin gina bayan ta da mota, da sukazo da ita,
Tunda har an rufe get yanzu dole sai ta samu partner da zasu shi ga,
Sauriyi Amina ne keta faman zirga zirga bidan wanda yadace ya hada Aisha Sanda da shi,
Sanin halinta na zama first class ya sa bai yi gigin hada ta da kowa ba,
Wata mota ce ta dan no inda suke tsaye tunda ganisa kaji engine din motar kasan yar lafiya ce,
Rangerover sport, ce ta dan no tun daga nesa aka kashe mai ido da hasken motar,
Duk da bai san kowaye ba aciki yasan wanda yasan shine,
Don haka yai tsaye guri guda har na cikin motar ya fito
KB ne yafara fitowa ta gefen mai zaman, banza,sai kuma Jibrin wanda ya balle, marifin motar baya ,ya fito,
Tunda ga nesa ya gane su KB don haka yasan cewa,
Yanzu za ai solving din problem din su, ma,ana Aisha ta samu irin da zai hada su,
Joseph ne yafito karshe sanye yake da dinkin shadda mai ruwan makuba ,
Sai sarkar gold da zoben gold din guda biyu a hannun shi,
A hankali yake takowa har zuwa in,da su KB suke tsaye da Lawal abokin su,
Hannu sukayi da lawal din inda ba bata lokaci lawal ke fada ma su bukatar shi,
Ya na mai nuna Aisha inda take tsaye, cikin second duk suga wai amma banda Joseph, wanda kamar ma bai gane may ake nufi ba,
Inda lawal yaci gaba da fadin sun bar pass din su, a gida ne gurin sauri,
KB ne ya waiga inda Joseph ke tsaye yana kallon ya ce,
Man wanan taimakon ka ne, pls
Cikin nuna rashin ganewa yake kara tambayar su, komai zai mata nan dai KB yakara mai bayani,
Kafadar shi dan daga alamar ba damuwa ai,
Shigowan su a cikin dakin taron ya haskaka so sai don mai MC yai announcement din shigowar su kamar yadda idan wasu sun shigo ake cewa ga yan kungiyar kaza nan sun iso,
Kallo ya koma gare sai kuma dan kus kus yatashi a gurin kamar yadda aka saba, inda anga kirstan na shiga cikin musullumai adinga a queuzing din su ta hanyar da bai dace ba,
Wanda yin haka najawo ma su sanyin gwiwa, so sai,
Mafi yawan mutane sai mamakin Aisha sanda sukeyi a cikin su ke don sanin cewa sunan ta na cikin fitattun yamatan da ke tashe agari,
Kuma gashi kayan ta sundanyi shigen kala da na jikin Joseph din wanda shi bai ko dago da hakan ba,
Zaman su bada wani dadewa aka fara program din bukin,
Ana aka fara gudanar da abubuwan da aka tsara a gurin,
Zaune Joseph yake yadan tokare habar shi da hannayen shi dukka biyu,
Yana kallon yadda ake guda nar da bukin abokin su, wanda yai aure,,,
Wani can wanda Joseph din bai sani ba yazo ya ja KB da hira har suka bar kujerar,
Jibrin dake gefe a zaune wayar shi taikara bayajin may ake cewa don haka ya tashi yadan koma can ta waje kadan ko zai ji kiran,,,
Yanzu,daga Aisha sai Joseph ke zaune, a inda aka tanadar masu, suke zaune,
Daga inda KB yake suna magana ya jiyo muryan MC na cewa ana bukata Joseph da Aisha su fito su taya ango farin ciki,
Saida KB ya dafe kai don yasan cewa da wuya Joseph din ya fito tunda baida masaniyar hakan,,
MC nata nata abinda akace text kb yayo mai cewa yafirmta dashi da yari yar nan suyi rawa,
Kamar kada ya tashi sai yatuna cewa bazai kyautawa angon ba inda har bai fita ba don haka ya fara mikewa batare da ya kalleta ba yace mata sai ki tashi mu fita ko,
Ba wani rawa sukayi ba sosai amma anji dadin fitar nasu don Joseph ya nuna kulawar shi ga ango,,
Wasu yan mata dake ge fe zaune suna kallon yadda ake ta
Su ka fara yan suraitai kamar haka,
Au dama wanan ba musullumi bane ke inji wa ya fada maki,
Dayar tace bakiji lokacin da ake cewa ana son Yusuf Joseph yafito tare da,Aisha sanda
Sai gudan tace kai amma anyi harasa wallahi guy kamar wanan kuma bai sallah,
Dayar tace gaskiya ni saima kawai naji haushin shi ya kamani wallahi, ita kuma Aisha don kwadai sai wani shige mai take ta yi,
Wace ita ce cikon ta hudun masu hiran da tun da suka fara zance bata ce kala ba,
Tace kai ku dai na daukar wa kan ku wahala ma,
Iyaka,ku da shi kuyi mashi fatan alherin shiga cikin islama indan har yana da rabon shiryuwa, Allah yasa yagane gaskiya yadawo hanya,
Sai ta farkon tai caraf ta ce a haka ?
Wanan ai yai nisa baya jin kira, in bashi ba ai tun yana yaro da ya musulunta, ko,,,,,
Ita dai wace bata maganar sai cewa ta yi ai abin daga Allah ne kawai, in Allah ya nufe shi da shiryuwa saiko ya shiru, yadawo hanya,
Haka dai kusan ko wani kujera suke ta zancen su kamar yadda gurin buki ya tana da
Kai kana kallon wani wani yana kallon ka,
Ganin cewa dare ya fara yasa Joseph yai su KB magana akan cewa su zo su tafi don shi baya yin dare sosai a waje,
Don duk haka tarbiyar yaran IBO suke duk ganin kada su basu yarda,su kai karfe takwas na dare waje,
Wana na daga cikin irin tarbiyar da suke wa yaran su,
Idan kuma sana,a ce bakin karfe shidda andawo gida ke nan daga gurin sana,a,
Saidai kuma tun karfe bakwai na safe anbar gida ke nan zuwa gurin bidar kude, (Allah ya kyauta)
Wanan haduwar da Joseph yayi da Aisha itace silar haduwar su,
Don tun a gurin da ta ce ya ara mata waya takira kawar ta don su wuce tasamu nobar shi,,,
Da zai tafi ma lake mai tayi akan ya bata lift zuwa gida saboda dare yayi a cewar ta,
Anan yabar su KB daga shi sai Aish sanda suka kamo hanyar zuwa gida,
Da kwatance tai ta yi mai har suka iso gidan su, Aisha din,
Koda ya Parker motar shi bai ce mata komai ba sai jiran yakeyi tafi ta yasamu ya wuce
Ita ta tsaya wani yanga kamar wace bata da lakka ajikin ta
A hankali ta dan waiga inda yake tana cewa nagode fa,sai wani lokaci ke nan kuma ,
Kai ya kada mata yana mai cewa No ba matsala ai ,,
Tana fita yafigi motar shi da karfi yabar uguwar zuwa, gidan su,,,,,,,,
Chapter 8 · 0% Book details