← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 171

Sashe 10

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Maryam tana tsaye a gaban mirrow tana gyaran hijab din dake a wuyan ta,
Issalam tazo ta bayan ta ta rugumay ta ,
Issalam kada fa ki sa in fadi kasa wqnan rikon da kikai min,,,
Yar wasan kokuwa suka fara yi da Issalam din kama ba zasu makaranta ba,
Anty Dije ce ta leko dakin jin su shiru da tayi dakin,
Cikin mamaki anty Dije tace, amma dai, maryam anyi uwar banza
Yanzu ku shirya ku wuce shine zaki buge da wasan kokuwa da Issalam,
Maryam na dariya daidai lokacin da Issalam ta kara kai mata damka ta na ko karin wai sai ta kayar da maryam a kasa,
Daidai tana fadawa kan katifa, tace ma yar nata ai yanzu zamu wuce insha Allah,,
Anty Dije na tsuki ta sake labulen dakin tace ai ku ,za,a daka a makarantan,
Har ta kai kofa ta tuna Assalam baya dakin kira ta kwada mai,
Daga bayi ya karba mata mama gani nan ina wanka,
Cikin mamaki jin cewa yana cikin bayi har yanzu yasa anty mamaki
Hanyar bayin ta nufa don ganin may yake yi a ciki har yanzu,
Sabulu yasa a fuskan shi dumu dumu, bai ko san shigowar uwar tashi ba ciki,
Sai lokacin da yaji hannun ta a jikin shi ta danko shi,
Wani irin ra,zananen ihu, yasa wa uwar don yana ganin kamar zata buge shi, yasa yaron yaka ihu,
Daga, maryam har Issalam duk bayin inda yake kwala ihun suka nufa,
Wanka su ka samu Anty Dije tana mashi yana ta kokarin kubcewa,
Bayan sun shirya ne suka wuce islamiya saboda sun makara, yau
Allah ya taimake su ba su sami malam babba yadan fita don haka badu sha duka ba,,,

Isowar su Joseph da KB a majalissar su ya yasa gurin yadan kaure da hayaniya cikin dan lokaci kadan,,
Bayan dan gaishe gaishen da ya biyo bayan ne suka samu guri suka zauna
Fira akeyi amma shi Joseph uffan bai ce masu ba sai dai idan anyi abin dariya shima yadara,
Ana cikin hirane daidai lokacin da yan makarantan Isalamiya suka fara tasowa, a lokacin wayar shi tai kara alamar kira yashigo mai,
Aisha ce ya gani baro baro a jikin screen din wayar tashi,
Dan tashi yayi nisa kadan daga ind suke zaune, don ya karba wayan nata,,
Tambayar shi take yi yana ina ne ?
Don tana son ganin shi ne, kafin yabata ansa sai ji yayi an rike shi ta bayan shi,
Da alama kuma dan karamin yaro ne don daidai iya gwiwar shi yaron ya tsaya,
Kafin ya juya lokacin da yaji haka yake cewa Aisha yana zuwa pls,
Waigowa yayi a hankali yana kokarin ganin kowaye yaron,
Wani dan farin yaro yagani ya rike shi tsab yaron na cewa,
Abokina kullun sai na diba ko zan gan ka idan zamu tafi islamiya amma bana ganin ka,
Idan kuma na tsaya sai little, mum ta dinga zagina,
Rage tsawo Joseph din yayi don dai bai fahinci ko may yaron ke tawa bayani ba,
Maryam, dake tsaye gefe iyakar kuluwa ta kai har tafi nan,
Don ji takeyi yau idan ta fara dukan Assalam bazata daina ba tunda har yasa ta tsayawa daidai gurin yan sa idon mutanen nan,
Hannun Assalam Joseph yakama ya hade guri guda yana mai fuskantar yaron,
Kafin yai magana sai muryan maryam suka ji tana cewa Assalam bazaka zo mutafi, ba ko,
So kake dare yai muna a hanya kafin mu isa gida ko,
Nunata da hannu Assalam yayi yana mai cewa dakace kada in basu sweet dina sai da little mum ta ba Issalam tasha,
Joseph dai har yanzu bai fahinci yaron ba don ya manta cewa sun taba haduwa da yaron ,,,
Yace wa Issalam bari ,zan saya ma wani mai yawa amma kaba kowa yasha kada kayi rowa kaji,,
Jibrin dake kallon draman su tun dazu yadan taso daga inda yake saman wani benci yana cewa cikin turancin
Ai yaron da ka taba dauka ne da ya fadi a gurin nan da zasu tafi,makaranta,
Saida yadan yi tuna ne sannan yace ok ok na tuna a haba dai my friend kaine haka kazama big guy,,
Yakara jawo yaron zuwa cikin jikin shi ya rungumay yadan dago kai yana kallon jibrin,,
Yace wanan yaron baya mantuwa pa kadiba bafa yau ba wanan event din ya faru wai ama ace bai manta ba,
Maryam kuka kawai ya rake tayi a lokacin saboda sukuwar da yayi da Assalam,
Cikin zafin nama ta isa inda suke tana kokarin finciko Assalam, din,
Kai Joseph yadaga yana kallonta yana cewa haba barshi mana pls,
Wanan yaro ne fa shi ai baisan komai ba, yana fadin abinda ke a mind din shine fa kawai,
Batare da ta saurari may yake cewa ba tace kazo muje gida kaji wallahi yau sai na ma mugun bugu Assalam,
Jibrin da baiyi magana ba tun dazon ne yake cewa kutafi zan kawo shi gida,
Cikin mamaki ta dago kai tana kallon mai magana don ita a iya sanin ta bata taba ganin jibrin a gidan nasu ba,
Yagane kallon da take mai don haka yace mata ke wanan yaron fa nima yaro na ne kin ji,
Kafin mamakinta ya kai karshe
Taji yana cewa ke ba kaunar matan Isiya Custom bane,
Kai kawai tadan gyada mai alamar eh ita ce, din
Yace to kutafi kawai zan kawo shi,
Still wani irin mugun kallon see u tai ma jibrin din alokacin,
Yace ke nifa yaron gwago laure ne don haka ki wuce kawai,
Jin an ambaci gwago laure yasa maryam fara kama hanya rai bace hannunta rike da Issalam tana ja kiiiiiiii,
Anty tana kokari kauda abincin dare daga dan matsakacin kitchen din ta taga shigowar marya da Issalam a hasale,
Babu Assalam a tare da su hankalinta na kofar hanyar shigow taga shigowar Assalam din,
Kafin yatambaya maryam tace wallahi Anty gaskiya ba zan kara fita da Assalam ba tunda a gaskiya duk zamu wuce sai yabani kunya a hanya harda zuwa rokon fa naji yanayi,
Ido waje Anty Dije tace roko fa maryam ina yake in ci abu kazan shi,,,
Maryam tana kokarin shiga daki tabar Anty Dije a tsaye tsakar gida daidai lokacin da tace ya na can mana,
Idon dayafi na dazun fitowa waje tace can ina Maryam,?
Tare da wa yanda yake rokon ta fada kai tsaye kawai, tashige abinta,
Wuf Anty Dije ta bita ciki daidai lokacin da Maryam ta kwabe, hijabinta daga kan ta tace mata tare fa dadan gidan gwago laure suke,
Wani cikin su? Kenan inji Anty Dije
Uhumm nima ban san sunar shi ba inji Maryan,
Hijabin da Maryan ta kwabe Ànty Dije ta jawo tana kokarin sawa,
Daidai lokacin da sukaji ana sallama alamar shigowa cikin gidan
Karar takalman Assalam ne ya sanar da su cewa tare da mai sallamar yake tafe,
Assalam agaba da gudun shi cikin walwala da zumudin ya bude ledar dakw hannun shi
Anty Dije tai saurin kai mai duka a hannu ya wurgat da ledar ya, koma baya da sauri ya fara kuka,
Jibrin ne yace ma Anty Dije haba dai madam ya zaki buge shi tunda har kin gan mu a tare,
Cikin yar dariyar da batakai cikiba take cewa jibrin wallahi jibrin yaron ga baida dabiar kwarai,
Rokon ku fa yayi,
Nan da nan jibrin yakai kallon shi ga kofar daki inda Maryam take tsaye tun shigowar su,,
Hmm kawai yace yana kojarin komawa ya kamo hannun Assalam din
Bai roke mu ba yadai fada muna cewa wanan time din da aka saya mai sweet saida akaba kaunar shi,
Duk da joe yace kada yaba kowa,
Daga Anty Dije har Maryam duk sai jikin su yai sanyi,
Nan dai jibrin yaba Anty Dije labarin yadda akayi tun ranan farkon haduwar su da Joseph din
Joseph da ke waje tsaye yaga Assalam ya firo yana kuka riko mai hannu yayi yana kokarin lalashin shi,
Daidai lokacin Anty Dije da jibrin suka fito daga cikin gida,
Tana daga ciki kadan suka gaisa da Joseph din tana mai yi mashi godiya,
Yace kai haba ai ba komai bane wanan yaro ne Assalam bai san komai ba,
Jin hausan shi da Anty Dije tayi yasa ta gane cewa ba bahaushe bane shi,
Saidai sam batakawo cewa shi Christian bane, shi,
Joseph yace wa Assalm yai shiru zai sayo mai game da mota wasan yara,,,
Hakan yasa shi komawa cikin gida da sauri don yafada wa little mum da Issalam cewa za,a saya mai mota,,,,,,,

ZEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
8⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Chapter 10 · 0% Book details