← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 171

Sashe 145

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan ya kashe mota yafito yana rike da yar jakar gift da ya sayowa, mahaifin nashi, a lokacin,
Tundaga kafan shi har kai kallo daya zakai mai kasan cewa Naira ta yi rana agurin,
Tafiyan shi cikin takon kasaita irin na gogaggun matasan yan Abuja ko lagos,
Dan sajen da ya bari wanda yai mai round a fuska yakara fitar mai da kyaun fuskan shi fili,
Duk yadda matasan da ke gidan nasu suna kula da aiyukan gida ,
Sunzo karban ledar dake hannun shi amma sam ya hana ya na mai daga masu hannu alamar subar shi kawai,,
A sama resting chair yasamu Dad din shi ya dan kishingida kamar mai tunane muryan Yusuf yaji daga sama don sam bai tsanmani zuwan shi ba yanzu,
Direct gurin shi ya nufa, nufa yadan rungumo Dad din zuwa jikin shi,
Cikin lumshe idanun shi yace ma dan nashi you are welcome my child,
Tare da dan bubuga mai bayan shi cikin nuna mai kulawan ganin shi,
Kujera dake facing din inda Dad din yake ya nufa nan ya zauna suna facing din juna yadan tura mai ledan gift din da yazo mai da su,
Babu wanda keda alaka da giya ko wani abin maye daga duk cikin kwalaben, drinks din na karin jini ne da gyaran jiki,
A hankali tsohon yadago kai ya kallo dan nashi daga inda yake ya ce,
Joseph da gaskiyane ka auri yarinyar hausawa, kokuwa kana shirin aura ne,
Ba wani tsoro ko fargaba Yusuf din yace, baba da ba hausa da yar IBO duk guda ce fata dai in samu wace hankalin mu yazo daya,
Hannu Mr Emanuel yadaga wa Yusuf din wanda ya fara yiwa mahaifin shi dogon sharfi,
Dan tsohon yace lalai Yusuf yanzu kan nagane cewa kafita cikin mu gaba daya,
Don har gudun auren yar kabila, ka kake yi, yan mata nawa aka kawo min cewa in aura maka amma nace a,a don ina da, ra,ayinka zabi mace da kan ka,
Shiru yayi saboda wani irin bakin ciki da ya taso mai har yaji cewa bazai iya ci gaba da zancen ba,
Shima Yusuf din baiji dadi ba sam irin yadda ya ga rayuwar mahaifin nashi ya baci,
Sun yi shiru nawa ni lokaci don haka Yusuf din ya mike saboda yana da bukatan zuwa gurin mahaifi Jibrin don karin bayani,
Acikin rashin sa,a Yusuf bai samu mahaifin jibrin din a gida ba don haka ya juya motar shi sai zuwa gidan Anty dije,
Yasan cewa yau zai sha fadan rashi kiran su da baiyi ba kwana biyu kuma layin da zasu iya samun shi duk a rufe suke,
Da sallaman shi ya shigo gidan wanda kamshin shi kawai ya isarwa mutun sakon cewa yana a gurin,
Waje suke a zaune saboda garin akwai hadari wanda ke yawo a sararin samaniya tun da rana
Yanzu kuma sai yadan ba garin zafi,zafi da dan lumshi,lumshi,
Masara ce gassasa a ga ban su suke ci yayin da anty take kokarin hada kaya a cikin kitchen, saboda ganin hadarin da tayi,
Ganin shi girshi da sukayi babu wani hanya da zai sa maryam din ta boye mai,
Kallo guda su kai wa juna daga ita har shi kowan su ya kauda kai ga dan uwa,
Kowa da abinda yake sakawa azuciyar shi don ganin dan uwa da sukayi,
Safiya ce da Anty ke mai sannu da zuwa a lokacin sai maryam wace ke ta baya kadan ta mai sannu da zuwan acikin wani irin murya mai karyarwa,
a,ciki, ciki,
May yasa may ta ta ramay haka ?
Amma kuma ga jikin ta yai wani fresh maryam din yaga duk ta canza a lokaci guda,
Ita kuma maryam Yusuf din ne taga yakoma mata wani iri tankar yaune ta fara ganin shi,
A galon su , suke zaune suna gaisawa da Anty Dije wace bata san ko may yasa ba yau kawai ta tsinci kan ta da jin kunyan kanin nata, haka kawai,
Ya dan dago kai yana mata dan murmushin nan tashi ta bajin ta,
Anty Dije wace ala dole take wanan zaman da Yusuf din
Cikin dan dukar da kai tace wa Yusuf din, cikin marai,rai ce war murya,
Yusuf kawai sai kaji yadda zance ya kasan ce daga karshe ko,
Baba ya ya yiwa kowa baza ta don ko ni ban san da zancen auren nan ba sai bayan anyi,
Kasan irin yadda maryam din tai ta fama da jin jiki,
Duk wanan bayanin bata lura da cewa kallon mamaki Yusuf din ke mata a lokacin.
Anty ban fahinci maganar ki ba inji Yusuf din yake tabayar anty dijen,
Anty ta kara cewa nasan saboda mugun ciwon kan nan da tayi ya firgita ta shi,
Irin yadda maryam ta firgice ai duk wanda ya gan ta sai ya ji tsoro a lokacin,
Maryam din tayi ciwo ne har haka anty ya tambaya a cikin kulawa,
Nan anty ta kwashe duk yadda abin ya kasan ce ta,bashi labari, har zuwa zancen daurin auren su,
Cikin tambayar da ta gigitashi yace Anty kina nufin cewa maryam a matsayin mata ta take yanzu nan,
Mamakin tambayar da Yusuf yai mata taji saboda tazaci cewa tun farko ya san da zancen,
Cikin mamaki Anty Dije tace kana nufin cewa, baka da labarin daurin Auren ku kaida maryam din,
Hasbunallahi wani,imal wake,el,,,
Sai kuma yai shiru inda yadaga kan shi ya na dan kallon saman silindin dakin bakin shi na motsi, kawai,
Da alamar addu,a ya keyi a lokacin, don haka ido Anty dije tabishi da shi,
Yakara dago kai tankar zaiyi magana amma kuma sai ya kasa,cewa komai yai shiru,
Muryan Anty Dije ne yadawo dashi ga tunanen da ya fara inda yaji tana cewa,
Gashi baba yai alkawarin cewa duk ranan da kazo a wanan ranan maryam zata tare a gidan ka,
Cikin rashin fahintar may hakan da anty dije tace yake nufi ,
Ganin bai fahince ta ba yasa ta cewa maryam din baba yace a yau zata shiga gidan ka,
Cikin sauri Yusuf ya tare ta da cewa haba haba anty,
Kada baba ya ce haka pls
Yabari har muyi styling pls, ?
Murmushi Anty dije tayi ta dan kalle shi tace baka da inda zaka satane Yusuf ,?
Anty amarya ai sai sabon gida ko kamai ma sabo ko
Cikin mamaki anty dije tace ma Yusuf din , kai a ina kake zama ?
Yace a wanan dan gidan nawa mana kinga ai ban yi shi as na mace ba ko ?
Hmmm inji Anty Dije saboda mamaki abinda Yusuf yace a kan gidan da yake a ciki,
Ganin tana mamakin yasa shi cewa a gaskiya ban dauka cewa auren mu da maryam zai zo da wuri ba haka don haka ne ma ban wani dade da sayen fili ba nasa ai mun irin plan din ginan da nake son inwa mata ta ta zauna a ciki,
Sai kuma ya wani irin nisawa bayan yakai karshen maganar ta shi,,,
Shiru sukayi gaba dayan su a lokaci guda,
Kowa da irin abinda yake tunane a cikin zuciyar shi,
Mikewa yayi saboda yatafi gurin mahaifin Jibrin din don yana son ganin shi sosai don jin karin bayani,
Duk da zuciyar shi har gagan jikin shi rawa sukeyi a lokacin saboda duk a rude yake,
Mamaki kawai yakeyi wai maryam ce yau a matsayin matar shi,
Jin abin yakeyi tankar a mafarki, ba wai a fili ba, sai da ya kai kofar fita yadan cewa Anty Dije saida safe don da wuya yadawo anjima
Murmushi tabi bayan shi da saboda ganin irin yadda ya rude a lokaci guda,
Abin mamaki yana fita waje a gurin da yabar su maryam din a zaune ba su gurin daga ita har safiya din,
Yaso kwarai ya kara ganin yarinyar saboda tausayin take bashi ,
Bai tsaya wani mamakin ina suke ba don yasan cewa saboda shi ne, suka boye,

Gidan mahaifin Jibrin din yakoma, inda yaci sa,a wanan karon dattijon yana gida,,
A cikin mutunci da nuna kulawa, dattijon yatari Yusuf din,
Kamar yadda yaran hausawa suke gaida na gaba dasu
Haka,Yusuf din ya durkusa har kasa ya gaida mahaifin jibrin din,
Bayan sun gaisa, ne a cikin walwala, Dattijon ya tambaye shi, gajiyan tafiya,?
Sai Yusuf din ke fadawa mahaifin na jibrin cewa yazo ai dazun bai samay shi a gida ba,
Dattijon ya ce Allah sarki ai nadan zagaya nan bayan layin mune gaida wani makwabcina da yadawo umura,
Yusuf yace shima yana da sha,awan bana ya tafi Umarh din nan insha Allah,
Haka akeso ai, inji dattijon ya ce wa Yusuf din,
Kullun ana son al,uman manzo S,A,W su bazama izuwa gurin ibada kasa mai tsarki,
Saboda kara samun ci gaban musulunci a cikin duniya,
Yakare da cewa Allah yasa, Musulunci ya rinjayi kafirci akoda yaushe,
Yusuf ya karba mai da fadin amin, Ya Allah,,,
Dan shirune ya biyo bayan hiran nasu a lokacin,

ZEEE MAKAWA YALWA
[5/3, 10:53 AM] ‪+234 706 262 3470‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
8⃣6⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,
YAURI

RAMADDAM KAREEM👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏
Chapter 145 · 0% Book details