← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 171

Sashe 106

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Zaune take saman kujera mai zaman mutun biyu,
Hannunta rike da waya tana cewa safiya tazo mata da, wani mango drink datake yawan son sha,
Safiyan na cewa ita bazata koma baya ba tunda ta wuto gurin ko,
Tsuki taja tana cewa macuyiya don kawai kimin keta kin san ban shan duk irin da kika,sayo zaki ce bazaki sayo min ba,
Muryan shi taji daidai saitin bayan ta yana cewa kedawa ke fada haka maryam ?
Da sauri ta juya bayanta cikin dan tsorata don sam batasan ya shigo gidan ba a lokacin,
Bayan ta ta juya sai ta gan shi tsaye cikin wasu kaya masu shigen na indiyan musulmai,
Maganar su Anty Dije ne yafado mata arai cikin dan kankanin lokaci
Sai cewa tayi cikin dan wani murya kamar mai shagwaba,
Wallahi yaya safiya ce muguwa Anty ta aiketa sayen drink shine nace mata, tasayo min irin wanda nake so
Amma wai sai ce min tayi wai ita ai ta riga tabar shagon sayarwa ko kuma bazata koma ba,
A hankalo ya isa gurin dayan kujerar dake facin din wanda take zaune akai,
Cikin mamakin yadda yau ta sake jiki tana mai magana cikin mutunci da nuna kulawa,
A dan matse fuska yace ina Assalam da Issi suzo mutafi in kai ku ku sayo,
Wani iri maryam taji a cikin ranta na yadda zasu fita a tare gudun kada wani ya gan su ya zaci wani abu,
Amma sai gargadin Anty Dije da Safiya ya fado mata a rai,
Murmushi tayi a fili tace uncle kada na wahal da kai da abarshi kawai zai fi,
Kallo mai kamar harara yai mata yace ku sa may ni a mota pls
Kanta kawai ta gyada alamar to,
English wear ke ta cikin jikin ta don haka sai ta dauko wani katon hijab din ta , ta feshe shi tsab da kamshi ta zumbuda saman kayan nata,
Da ita da yaran suka fita bayan ta shedawa anty inda zasu da uncle din,
A can dan nisa kadan da kofar gidan ya parker motar shi,
Wata bakar Jeep ce mai kama da wani siffan abin ruwa,
Da karasowan su ya bude motar ta yadda zasu shiga ciki dukkan su,
Assalam wanda yasaba idan zasu fita ya shige gaba tare da shi
Yanzun ma kokarin shiga gaban motar yaron kayi
Amma sai Yusuf din yake ce mai, ya koma baya tare da Issi su zauna yabarwa little Mum gaba,
Suna barin gurin anty dije wace ke tsaye bayan labule tana leken su tai wani yar ajiyar zuciya,
Kira,an shek Ahmad suleman kano ke tashi a cikjn motar a cikin surar Al,imran ,
Maryam din wace itama bin karatun takeyi a hankali,
Inda Yusuf din ke ta sharara gudu a saman titin,
Cikin yan mintina kadan sai gasu a bakin wani store wanda akai wa rubutu da manyan haruffa 212 plaza,
Shagon yakai shago a wurin girma don haka suna tsayawa a wanan store din,
Maryam ta daga kai tun shigowar su motar,ta kalle shi,
Yagane may take nufi don haka yadan juya inda su Assalam suke ya ce,
Mufita mu zagaya kowa ya dauki abinda yake so kunji,
Cikkn zumudi suka firfito zuwa cikkn shagon inda yake rike da hannayen yaran,
Itama maryam din dole tabi bayan su badon ranta yaso ba,
Sosai suke ta sayayyan su shi da yaran inda yake biye wa duk wani shirmay nasu yana taya su jidan kayan da suke so, agurin,
A, baya baya maryam ke bin su wace har zuwa yanzu ko tsinke bata dauka ba,
Ganim bata da niyar zuwa yin abinda ya kawo su yasa shi ce mata,
Kinfasa sayen drinks din ne ko ?
Kai ta gyada mai alamar ,a,a don haka atare gaba dayan su suka tafi gurin,fani abin shaye shaye da yan tonde, tonde,
Sai kuma ya wuce zuwa gurin su man gyaran gashi da kayan kamshi dana wanka,
Juyowa yayi inda take yace sun ishe, ki ko a kara wasu,
Da sauri maryam ta kada kai alamar sun isheta,
Gurin biyan kudaden kayan da suka lodo ya nufa inda yabiya su makudan kudi a ka kai masu har cikin motar su,
Wanan karon a hankali yake tafiya ba kamar lokacin da zasu zo ba,
Sai can daga bisani ya dan karkato kanshi inda take yace,
Maryam ina saurayin ki naga tun da nazo ban gan shi yazo ba,
Kamar maganar bai soke ta ba tace, kai yaya Yusuf, har da yar kaunar taka kakesawa ido,
Surukin kane fa , yaya yusuf takare zancen a cikin zolaya,
Tsaki ya ja yana mai yar hararan ta yace, Allah dai ya kiyaye ni surikina mai mutunci ne,
Duk da ansar ya bata mata rai amma sai ta cije tace mai cikin dan sasauta murya,
Kai ya Yusuf duk wanan biyayya da girmamawan da yake maka, zakace mai hakan ?
Tsuki yaja cikin dan sasauta murya, yace, to be Frank maryam wanan guy din wallahi bai dace dake ba sam,
Gaban tane ya fafi dammm saboda jin abin da yace,
Muryan yaran dake bayane suna kokarin bude wani kwalin biscuit sai fada ga kaure a tsakanin su,
Sosai yanzu ya lula a saman titin cikin yan mintina ya iso kofar gidan nasu
Tun daga nesa kafin su karasa kofan gidan maryam ta hango motar A,A a tsaye amma yana acikk zaune,
Gab da motar shi uncle ya tsaya da tashi motar a gefe guda,
Cikin kidimaywa da nuna tsoro maryam ta bakina rawa take cewa malam tun yaushe kazo, shine baka kirani ba,
Hararanta yayi cikin daure fuska yace daga motar wa kike maryam,
A lokacin Yusuf dake kokarin kwasan kayan da suka,sayo yana jin su,
Dukar da kan ta tayi kasa tai shiru, sai daya kara dan dago fuskan shi acikin bacin rai yace,
Maryam ban fa fahince ki ba tambayar ki nakeyi fa,
Cikin gagawa yake azaman bude kofar motar shi,
Ya nunata da yatsan shi yace kada ki raina min wayo ki mai da i ban san abinda nakeyi ba fa pls
Nan da nan idon shi ya canza yai wani jajajir tsatsan bacin rai duk ya baiyana a fuskan shi,
Sosai rayuwan ta yai mata daci akan irin yadda yake mata agaban mutane,
Idanu a runtse tana jin wani irin zafi da bacin rai tace,
Dakata malam kadaina fada min irin wanan kalaman,kamar wata yar cikin ka,,,
Cike da mamaki A,A ya ware ido yake kallon ta don ta bashi mamaki irin yadda tarufe ido tana bashi ansa,
Juyawa tayi kawai zuwa cikin gida batare da takara koda second a gurin ba,,,,,

SEENABU MAKAWA,,
H🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
6⃣5⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA

IYAKA, NA,ABBUDU WA,IYAKKA NAS,TA INN,,,

Har kulun addu,a na,gare ku da fatan alheri ga duk masoya novel din furen juji, Allah yasa a gama da duniya lafiya Allah,sa mu, dace da rahaman Ubangijin mu,,,,
👏👏👏👏👏👏👏👏

Shigowar Maryam ya yi dai dai da fitan Yusuf da ga cikin gidan,
Dan gefe ta samu ta dan bashi hanya, tankar baisan cewa da ita a gurin ba ya sa kai zuwa waje abinshi batare da ya ko kalle ta ba,
Duk da rayuwan Maryam bai mata dadi ba soboda irn yadda ya nuna mata,
A kofar, gida Yusuf ya hango motar Yusuf din yana kokarin barin unguwar,
Sau,guda yadan kalli gefen da ya hango motar A ,A din yai wani saurin kauda kan shi, batare tankar A,A yasan da shi a gurin,
Sai bayan yaga shigewar shi daga kwanar
Yai wani irin dogon tsuki kamar wanda ya ga wani abin ki, ko tsana,
Chapter 106 · 0% Book details