← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 171

Sashe 108

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai da maryam tai wani irin ajiyar zuciya mai nauyi sai ta ce Allah ya kyauta,
Duk gurin suka amsa da fadar Ameen Ameen, gaba daya a lokaci guda,
Daga haka maryam ta wuce zuwa gurin da suke aiki sai dai zuciyar ta cushe da bakin cikin halin da wanan matar take ciki,
Tun zuwa lokacin da takoma haka kawai sai ta tsinci kanta a cikin damuwa da maganar,
To sai dai kuma ta ina zata fara wa zance daga karshe ma zuciyar ta ya bata shawara akan
Ita wace,ce da may ma zata iya tallafa mata tai tsuki tana mai cewa ina ma a ce musulman mu masu zuciya ne kamar yan mabiya addinin Christian,
Da wanan tunanen suka risketa a zaune, duk sallama da maganar da Jibrin kewa maryam hankalin ta ya zurfafa a cikin tunanen wanan matar da taji labarin ta dazun,
Gaba dayan su mamaki yadda yar karamar yarinya take irin wanan zurfafan tunanen da kurciyar ta,
Jibrin ne yasa keys din motar shi kusan fuskan ta ya dan kada mata shi a fuska,
Firgigit tadawo a cikin hankalin ta yayin da ta sauke idon ta a kan su su uku,
Suna tsaye suna mata wani irin kallon mamaki cikin sauri ta dukar da kanta kasa tana mai gaishe su da shigowa a lokacin,
Kara tambayar ta Jibrin din yayi a cikin tsigar wasa,
Ko dai A, A din ta dan masuga take tunane ya kira mata shi,
Murmushi mai kama da harara tai mai tana cewa ai ba sai kakira min shi ba,
An fada ma, ni banda wayan kiran shi ne a guri na,
Ke dai gaskiya barin kira maki shi kawai,
Wani wawan tsuki Yusuf yaja daga bayan Jibrin din yace
Ke Maryam Anty tace zaki fitar muna da kulolin abinci ko ?
Sai a lokacin maryam ta farga da su a tsaye bayan jibrin
Yusuf din wanda tun fara wasan ba,an su yake faman dan,nan wayar shi, kawai,
Irin yadda yai magana ta mayar mai da ansa ita ma,
Ta mike suka shiga fito masu da yawan kololin abincin da a ka dafa masu don jama,an su,
Gaskiya duk sun yaba da irin kalar girkn da anty dije ta tayi ita da sisters din nata,
Maryam ce ta dangware wasu set din plates masu yawa a gaban kololin,
Yusuf wanda ke can daga bayan su don yaki karaso kusa yadaga wayan shi yana kira,
A daidai lokacin da wata daga cikin matan tazo tana mai wani kirari a cikin harshen yaren su,
Sai wata yar boyayyar murmushi yake yi a hankali tankar wanda bai son asan may take cewa,
Matar ta juya da harshe hausan wanda ke da,surkin yare aciki tana mai cewa wasu jibrin,
Wanan da kuna ganin shi a nan,
Shan gerin mu shune manya, manya sosai don de baba nashi bai jauna a gida bane
Da yan junan yazama serki a gerin na su ko,
Kudi masu yawa yafito dasu ya mika mata sai ga sauran matan dake saye da zanin su na IBO
Anyi fanti, fatin sama da kasa sai farar bluewers, da gwagwaro a kai,
Nan suka shiga raira mai wani waka acikin yaren su suna mai yi mai kirari,
Tsatsaye su maryam sukayi suna mai kallon su gwanin ban sha,a wa,
KB da Jibrin su ma suka basu kyautan kudi masu yawan gaske,
Safiya ce ta dan muntsili maryam din tana mai mata nuni da Yusuf din,
Wani irin wawan duka takai ma Safiya din wace ta kauce tana dariya keta,
Caraf sai a idon Yusuf wanda, idon shi yakai gare su tun fara wasan nasu,
Daure fuskan shi yayi yana mai masu wani kallon ku daina haka man,
Duk kan su, suka sun,kuyar da kan su a cikin lokaci guda,cikin jin kunya,
Still, uncle inji Safiya ka bari mu ji kirarin ka mana ko zamu iya muma muyi ma, irin shi,
Duk daure fuskan shi da yayi sai da maganar safiya ta sa shi yin yar murmushin,
Ya dan kada kai yace kai,safiya baki da dama fa,
Dariya ta saka mai tana mai jawo maryam, wai zasuyi wa Yusuf din kirari,
Kanta ta koma sadawa kasa saboda irin kallon da Yusuf ke mata,
Mayar da hankalin shi gurin da kololin abincin suke ya yi
Juyawa kawai maryam tayi zuwa dakin, abin ta batare da takara wani abin ba agurin,
Ko da ya juyo bai ganta a gurin ba ta wutsiyar idon shi, ya dan hango ta, zata shige daki,
Daga cikin daki taji dirin motocin su, sun kwashi kayan abincin zuwa gurin da za ai recipetion,
Wanka maryam tayi bayan shigan ta daki inda ta fito cikin wani Dakkaken dinkin shadda din da yusuf ai,kowa Sadiyar, ce daka karshe kuma yace abar ma,maryam din,,,
Sune Anty Dije ta bayar akai mata wanan dinkin mai wani hannu shara,shara,
Sai lece, da aka darza mai bayan anyi mai aikin wuta, da kuma stone a jikin shi,
Kayan light green, sunyi mugun karban jikin ta takai wani lokaci a gaban miro tana gyara jikin ta tsab,
Itama dai safiya irin shaddan ta sa sai dai gurin dinki ne kawai suka sha banban dana maryam,
Sun kai wani lokaci a cikin daki suna yar hiran su ,saidai muryan mutane da suke ji sama sama a,waje,
Da sauri ta mike zuwa waje don tunawa da tayi cewa Anty fa bata gida suna gurin gyarawa Naimat gidan da zasu zauna,
Zaune yake shi kadai a cikin falon su, ya dan zauna rigingine.
Ya dafe kai da hannu shi guda idon shi a rufe ya lumshe su,
Ganin da tai mai haka yasa ta kudirawa barci yake yi a hankan,
Juyawa tayi da niyar ta koma cikin daki inda suke ta zabga hiran su,
Maryam, yace cikin wata irin nishadaddiyar murya,
Cak ta tsaya don jin mai zaice, mata,
Still bai kalle ta ba hannun shi ya na dafe da kan shi,
Jikin ta taji yai sanyi don irin yadda yai mata,
Kan ka ke ciwo ne yaya ta samu kanta da tambayar shi,
Shiru nadan lokaci tukun kafin ya cire hannun shi yadan kalle ta da idon shi da su ka kada mai sukai jajir kamar yaci kuka,
A hankali ya ce mata may kika gani ne haka ?
Cikin dakewa tace idon ka sunyi ja da yawa uncle,
Kan sa ya girgiza mata, yace babu wani ciwon kai dake damu na maryam,
Illa magana da ke kokarin tarwatsa min zuciya ta,
Maryam bana son in na fadawa mutum gaskiya,yana dauka ta tankar banda daraja agurin mutum,
Baki ta dan murgada mai kadan tace nidai ya Yusuf na dai kusa aure in huta da duk wanan sa idon da kuke min,
Don dai ni banga abin da nake yi ba har kake cewa hakan,
Niyar barin gurin tayi tana kun,ku ni, tana cewa wallahi shi yasa bana son shigowar ku KG sam, saboda takura da sa ido,
Tajuya kawai abinta,
Saidai batai nisa ba ta jiyo muryan shi yana cewa,
To aiko nai maki murna da kika fada min cewa, kina son aure kwanan nan
Don haka zan je in samu baba da Anty in sheda masu, abinda ki ka ce,,
Da sauri ta juyo tana fuskan tar shi batare da wani jin dariri ba ko kunyan shi,
Sai dai, kuma wanan karon kamar bashi ke kwance da zu ba,
Yanzu a zaune ya kyam,kamar ba shi ba, ya na mata wani kallon cikin zaki gane kuren ki,
Ba kunya ta, kama yar hararan shi, tace, ban san may yasa kake yawan samin ido yanzu ba wallahi,
Kawai ta juya ta shige abin ta zuwa inda ta hango Naimat zaune tare da bakin ta,,,
Bayan ta yabi da kallo a daidai lokacin da kiran sadiyar shi ya shigo mai,
Tana mai sheda mai cewa ga ta a kofar gidan Ànty tazo mai buki,
Tashi yayi daga inda yake yadan leka inda yaga maryam tabi,
Tsaye take sina diban waya ita da Naimat da Safiya,
Ganin shi ya leko daga kofan falon yasa su mai da hankali gurin shi banda maryam wace kanta yake duke tana kallon waya,
Sunan ta yakira yace tafita waje ta shigo mai da baki pls,
Lokacin da ta fita, ta samu su Sadiya ne bakin da yake nufi tai bakin ciki sosai don ita tana ganin cewa yai mata rashin mutunci sosai,
Ita Sadiya din bata san kofar shiga gidan bane da zai tura ta taron su,
Kallo guda Sadiya tai wa Maryam sai taji wani irin tsanar yarinyar ya kara shiganta,
Ita dai sam bata ra,ayin wanan yarinyar a rayuwar ta bata san mo may ya sa ba,
Rai a dan bace maryam ta dan tare su inda tai masu iso zuwa cikin gidan,
A falo kamar yadda tabar shi su ka samay shi a zaune hankalin shi kwance,,,,

SEENABU ZEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
6⃣6⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,

IYAKA, NA,ABBUDU WA,IYAKKA, NAS,TA,INN,,,

Ina mai baku hakkurin rashin jina da bakuyi ba kwana biyu, da fatan zakuyi hakkuri dani dan Allah,
Chapter 108 · 0% Book details