← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 171

Sashe 146

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Yusuf yana mai sunkuyar da kan shi a kasa ,
Sai shi daddtijon ne yai gyaran murya inda ya soma magana kamar haka,
Yusuf, kasan cewa yanzu dai duk musulmi na kwarai yakan yadda da kaddara,
Walau, mai kyau ko akasin ta watau mara kyau ke nan abin nufi,
Yusuf din yace hakanane baba dattijon ya ansa da fadin da kyau dan Albarka,
Yaci gaba da cewa ta a bayan ka abubuwa da dama sun faru.
A nan ya zayyane masa yadda sukayi tun daga farko da mahaifin su maryam din har zuwa daurin aure,
Kaga kenan al,amarin ubangiji ba, ai,mai shishigi,
Shiru Yusuf din yayi a lokacin tankar bazai yi magana ba ,
Har dattijo ya zaci cewa ko bai yi naam da zancen auren bane, haka,
Sai kuma yaga cewa ai Yusuf din ya can,canci ai mai wanan irin sakkayan da mahaifin su maryam yai mai,
Don gaskiya Yusuf mutum mai taimako da kyautatawa na kasa da shi,
Gashi ya fitar da jama,a da dama daga cikin kangin talauci kai taimakon shima dai mara adadine,
Amma kuma sai gashi wai mutum butulu ana,son abin hannun shi amma baza a iya hada zuria, da shi ba kamar ba musulmi ba,
To amma kuma gashi wanan bawan Allah yanuna halarcin shi gare shi,
Ya nuwa duniya bai kwadayin abin shi sai dai fatan alheri,
Don ko sadaki shi da kanshi ne ya matsa mai akan abarshi a dubu hamsin ,
Don shi mahaifin yarinyar yanuna, wai dubu ashirin ne, za,a bayar da farko,
Muryan Yusuf din ce ta katse mai tunanen ida acikin murya irin ta mai zubbar da hawaye, yace wa dattijon,
Baba ban da abin da zan furta a gare bayan ince Allah ya sa agama da duniya lafiya,
A cikin sauri dattijon ya ansa da fadin amin amin ya na mai gyara zaman shi,
Sai kuma yadan yi shiru hannun shi yasa ga aljihun shi yana kirgo kudin daga ciki,
Yan dubu guda gudane sababbi fill da su ya aje a gaban baban nasu,
Yace baba ga kudin da kuka bayar na sadiki sai kuma kudin goro da sauran su,
Kai, kai, inji mahaifin Jibrin din ya ce wa Yusuf cikin dan ja da baya kusa da kudin da Yusuf din ya aje, kamar wani wanda yaga abin tsoro,
Haba Yusuf ashe baka dauke ni a matsayin mahaifi ba,
No, no ba haka na bane baba, don Allah kayi hakkuri ka fahince ni,
Haba Yusuf duk abinda zan iya yi,wa Jibrin zan iya maka shi aduniyan nan ,
Sanan malam Abdulsamad shine ya siyo su goro da alawa, wanda aka rabawa mutanen,
Da suka sheda daurin auren naka don dai alhamdullahi mutane da dama sun sheda wanan daurin auren na ku, so sai,,,
Shirun da wurin ya dauka gaba daya shi ya sanya mahaifin Jibrin gane cewa Yusuf kuka yake,
Haba Yusuf ka kara godewa Allah ka da ya kaddare ka da yin wanan auren, cikin mutunci da girmamawa,
Don duk yadda ake halarci mahaifin Yarinyar ya yi gaskiya, saboda duk yadda yadace na gwada inda na fahinci cewa tsakani da Allah ya baka yar shi ba don kwadayin duniya ba,
Yusuf yace wa mahaifin Jibrin din nasan da haka baba,
Don wa yan nan mutane suna daga cikin sahun farko na tallafawa shi ga na, addini nan,
Saboda sam basu kyamace ni ba a rayuwar su, a lokacin danake cikin batar kai, kamar yadda sauran mutane ke nuna min kyama a baya,,
Kiran sallah da ya karade gari alamar magriba ya yi a lokacin shi dan tsaida zancen nasu,
Don haka suka mike kusan lokaci guda don haramar dauro alwala,
Amma sai Yusuf din ya dakatar da dattijon da cewa dazun na tafi gidan ita yar yarin wace ke rikon ta,
Take sheda min cewa wai mahaifin nasu yace, duk ranan da nazo a ranan yariyar zata tare agida na,,
Kai mahaifin Jibrin din ya kada yana cewa hmm malam Abdul zai iya yin fiye da hakan ai,
Don shi mutum ne mai ra,ayin kan shi bai bin ra,ayi al,umma,
To kai yanzu ya kake so a yi ne ?
Kai yadan sosa alamar jin kunya, yace baba naso ne ai mata kamar yadda naga hausawa nawa yaran su a gurin aure don saboda hankalin yarinyar ya dan kwanta,
Indan mun fito daga massallaci zan je gurin shi insha Allah, za a san yadda za,a yi,
Chapter 146 · 0% Book details