Sashe 147
Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Anty Dije wace tun bayan tafiyan Yusuf din duk ta rude saboda sanin halin mahaifin su da tayi, cewa bai magana biyu a rayuwar shi,
Don haka ta dauki waya kamar yadda ya umurce ta, da tayi a duk ranan da Yusuf ya shigo gari,
Bayan sun gaisa ne anty ke sheda mai cewa Yusuf yana gari don har ma yazo gidan ta dazun nan,
Albarka yadinga sa mata don bin umurnin shi da tayi ta sanar dashi a lokaci kamar yadda ya umurce ta din,
Nan yace mata da zaran an fito daga massalaci zai zo gidan nasu amma kafin nan duk wani shiri da ya dace tai wa maryam din ta tabbatar da cewa tayi mata shi,
Tun bayan kashe wayan su da babane sai Anty Dije taji idon ta ya ciciko da hawaye tausayin kaunar ta ya kamata,
Gidan uwale ta shiga inda tai mata bayanin komai kamar yadda mahaifin nasu ya, umurce, ta da, tayi,,
Don haka a,tare da Uwale Anty tashigo gidan a lokacin maryam da Safiya suna tare suna dan hiran su,
Safiya ce ke kokarin jan maryam din da hira don ta kwantar mata da hankali kamar ba komai,
Ganin shigowar su yadan tayar wa maryam da hankali amma da yake ita uwale irin wayyayun matan nan sai cewa tayi ,
Haba maryam may ye haka mijin ki na agari amma zaki zauna a haka ba wani gyara jiki,
Ta juya gurin da Anty Dije take tana cewa haba Hadiza kina kallo ko wani gyara baki mata ba idan ya shigo ya samay ta a haka fa,
Maza tashi ki gyara jikin ki kafin ya dawo ya samayki ba wani gyara,
Maryam ta turo baki gaba saboda jin haushin maganar da Uwale tai mata na cewa wai mijin ta,
Sai taji duk ta wani tsani Yusuf din kwatakwata arayuwar ta,
Amma sai taji Anty na cewa tashi mana maryam ana magana da ke,
Ba bata lokaci maryam ta mike inda uwale taimata nuni da cewa su je makewayi,
Abubuwa na gyaran jiki ta umarci maryam din da tayi a bathroom din ,
Inda uwale ke ta wajen bayin tana umurtan maryam da cewa yi kaza sa kaza gyara kaza har ta kimtsa tafito,
Wasu kayan kamshi ne aka bata tashafa wa jikin ta, inda duk hawaye ya cikawa maryam din ido a lokacin,
Daga matse,matsin ta har zuwa cibiyanta sai da uwale tasa maryam din ta shafe shi da wani dan ruwan mai kamshi acikin wani dan kwalba,
Daga haka kuma Safiya ta gyara mata kanta wanda dama tunda rana tai mata kitso mai kyau kamar sun san da zuwan shi a ranan,
Ita kan ta maryam din tasan cewa jikinta yasamu canji sosai, a irin yadda take jin shi,
Duk yadda zan yi bayani haduwar ta a lokacin mutun ba zai fahinta ba sai dai inda kungane ta a fili,
Sallah Uwale tasa ta gabatar daga magrib har isha,i, ta umurce ta dayi,
Amma ita maryam din duk a lokacin ba ta fahinci komai ba don babu abin da ta kawo a ranta,
Abu guda ne ya tsaya mata arai shine jin haushin yadda suke ta wani rawan jikin shirya mata jiki kamar wata bakuwan Yusuf din,
Bayan yasan ko ya take da tayi ado da batayi ba duk yasa ni,
Amma wai yau shine don ance yazama mijin ta shine suke wa ni rawan jiki à kai,
Gurin da tai sallah take zaune Uwale takara umurtan ta da takara shafawa jikin ta har zuwa kasan ta
Wanan ruwan dan kwalban da ta bata, da farko mai sa ta jin kasala ajikin ta,
Bayan ta gama shafawa kamar yadda Uwale ta umurce, tamika mata kwalban,
Takoma bakin gado tazauna tare da sake wani irin ajiyan zuciya,
Daidai lokacin da Ànty ta tashigo dakin dauke da wani dakakken lace a hannun ta,
Mai ruwan sky clour da stones farare ajikin shi suna sa shi shining,
Ran ta bai so ba amma ba yadda ta iya dole ta karbi kayan ta sa kamar yadda aka umurce ta dayi, don gudun sabawa manyan ta,
Daga bakin kofan sukaji muryan mahaifin su wanda hakan ba karamin haifar masu da kaduwa yayi ba dukkan su,
Nan da nan jikin maryam yadauki rawa kamar wace ke jin sanyi,
Baba kecewa ina Dijen take ne wai ko ba ta gidan ne,
Anty Dije ta karba da cewa ganin baba ya ce to, to , ya kun gama shiri ko, ?
Jiki a sanyaye ta amsa mai da fadin eh baba,
Ido Maryam ta zaro waje don jin abinda mahaifin su ke cewa yar ta,
Fito min da ita kawai maryam ta iyaji a lokacin ,
Wanda hakan yai daidai da wani irin sakin kuka da tayi a lokaci guda,
Na shiga uku Anty inji maryam cikin wani irin murya mai ban tausayi, take fadar haka,
Uwale ne da Safiya wace itama dai kukan take sakewa alokacin don ganin irin halin da aminiyar ta yau ta tsinci kan ta,
Duk da dai tasan cewa aure bautan ubangiji ne amma sai take ganin mahaifin kawar nata bai mata daidai, ba gaskiya,
Anty Dije wace hawayen dake idon ta alokacin suka balle mata itama dai kukan tashiga yi,
Jin kukan mu wiwi da baba ya yi, ya sa shi kiran sunan Anty Dije a hassale,
Wata, ashar ya wulwulo ya durawa gaba dayan su a tsorace, ,
Cikin sauri maryam ta koma jikin bango da gado ta kankamay Safiya wace itama kukan takeyi, a lokacin,
Baba wanda idon shi suka yi jawur a lokacin sai huci yakeyi,
Yakara kiran Anty dije a ciki wani kakausar murya wanda yakara sasu firgita,
Wuf maryam din tayi ta cakumi yar nata ta yadda baza ta iya kufcewa ba a lokacin,
Shiko baba daga waje sai cewa yake yi yo naga kina son raina min hanakali fa,
Anty Dije tace cikin muryan kuka baba ga munan fitowa ai,
Kara kankamay Anty Dije maryam tayi tana wani irin kuka cikin sauti mai ruda wakwalwan mai sauraren ta,
Cikin kukan take cewa ban san may nayi wa baba yake min haka duk cikin diyan shi anty kodai laifin da mahaifiya ta taimai yake ramawa a kaina,
Bakin ta Anty Dije ta rufe da sauri tana cewa maryam kan daya kuwa dakike irin wanan kukan,
Safiya tare da Uwale da anty kowa ya hau bakin shi sai magana suke ba maryam din,
Kai ta girgiza tace may ye na bani hakuri bayan wanda ma ya kawo ni duniya yana bidan kai dani,
Wanan karon bakin nata Anty ta buga da karfi sai da uwale tace mata ta daina dukan ta tabar ta taji da abu guda,
Duk zafin rai ne yasa take wanan maganganu bawai cikin hankali takeyin su ba,
Mahaifin su wanda yake tsaye daga waje yana jin abin da sukeyi a cikin daki yai murmushi mai daci,
Uwale ce tazo gaba da maryam din ta kira sunan ta ahankali tana cewa ki yi hakkuri,
Allaj ya kaddarata naki auren zai zo din haka don Allaj kiyi hakkuri da hukuncin da mahaifin ku ya yanke a kan ki,
Wani abu ta shafa mata mai sanyi a hanni tace Allah yasa gidan zaman ki ne maryam, Allah yasawa auren ki Albarka yabaki zuri,a dayyaba,
Sauran dake dakin suka karba da fadin Ameen ya Allah,
Tabbas maryam tasan cewa babu mafita akanta yau tabar gidan yar uwar na ta ke nan,
Safiya ce tai saurin goge lalin da a,ka shafawa maryam din a hannun ta,
Hannun ta ta diba ashe lalle ne aka shafa mata, shike nan tafaru takare,
Wanan karon kukan zuci ne maryam din keyi don sani ba wani makawa a kan ta, sai gidan Yusuf,
Ba suyi aune ba saga Baba har cikin dakin nata yashigo ya rike hannun, maryam din wace ke kuka wi, wi,
Anty dije komawa tayi falo inda tasa kuka sosai tare da yaran ta ,
Don dai harga Allah ba haka taso auren yar uwan nata ya kasance ba,
A falo daidai inda anty take a saman kujera tana kuka maryam ta daga murya tana cewe,
Anty na ki yafe min duk laifin da nai maki don girman Allah,
Da wanan maganar tabar gidan yar uwan nata tana rike da hannun mahaifin nasu,
Gaba daya yau taji ba Yusuf ba duk wani namijin dake duniya ya fice mata a rai,
Suna fita kofan gida motar Ibrahim ce suka gani waje a parke,
Wanda dama yana jiran
fitowar su ne kawai don haka yana ganin su ya tada motar ,shi,
Suna shiga daga ita sai baba kawai don yace bai yarda da rakiyan ko wace mace ba,
Maryam wace tadan jin gina kan ta da glass din motar tana kuka cikin sauti mai tsuma zuciya,
Muryan babane ke mata nasiha akan zaman aure, da kuma rayuwar duniya har suka isa G,R,A din unguwar da Yusuf ke da gida a ciki,,,,