← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 171

Sashe 16

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Why why mutane suke da gulma haka, may ye aibun taimaka ma KB dayayi da har za,a fada ma Dad din shi,
Wai may yasa mutane basu kaunar suga cigaban yan uwan su ne musan man hausawa,
Don dai yasan cewa wanan maganar daga bakin hausa yafito zuwa kunen mahaifin shi,
Zubur ya mike tsaye daga inda yake daga shi sai dogon wando da singlet a jikin shi,
Gurin window dake facin din titin da ke unguwar su ya nufa,
Fitinlo ne karara suka haske ko ina sai kuma duhun dare da ya gauraye gari lif,
Ya kai wani dan lokaci a gurin tsaye yana kallon sararin samaniya kawai,
Daga karshe bayan yasamu mafita yai wani dan ajiyar zuviya mai nauyi,
Fridge ya bude alcoholic ke ciki kala kala duk sunyi rabar sanyi yadda yake so,
Hannu ya mika da niyar yadauko wani mai berry a ciki,
Caka hannu shi ya tsaya daidai wuyar kwalbar
Muryan Jibrin ne ke mai yawo a kwakwawa duk addinin mu bai yarda da shan giya ba,
Duk wanda ya ganka a lokacin kana cikin maye baya kara kallon ka da dara a idon shi,
Don duk sanda ya gan ka wanan yanayin mayen dayagan ka aciko zai fado mai zuciyar shi
Kaga kimar ka da mutuncin ka yazube a idon shi,
Idan kuma ka samu iyali za,a dinga goranta masu cewa uban su dan giya ne, ai,
Cikin sauri kamar wanda akai ma tsawa ya dauke hannun shi saman kwalban,
Marfin fridge din ya buga da karfi kamar zai balla ,shi,
Da karfi ya fada kan gadon ta baya yana mai rike goshin shi da hannayen ,,
A haka wani irin barci mai nauyi ya kwashe shi bai farka ba sai misalin karfe tara saura na safe ,
Dan hasken ranar da hudu ta cikin labulen window dakin ya haska mai idon shi,,,
Mika yayi ya gyara kwanciyar shi don ya cigaba da barci amma sai kuma ya kasa ci gaba da barcin,
Mikewa yayi yashiga bayi yai wanka bayan fitowan wanshi ya na daure da towel
Yazo bakin gado ya rusun na kan shi saman gado
Nan yafara jero addua, our father whose as at heaven ,
Hello be there name,,,,,,,,,,,,,
Bai tsaya ba saida yakai karshen addu,an shi kamar kullun yadda ya saba yi duk safe kafin yafita,
Saida ya kintsa tsab ya sauko inda yasamu break fast din shi an shirya mai komai tsab
Jin gidan shiru yasa shi daga murya yana kiran Uchee, da karfi,
Uchee da ke can yana gyara cikin gida yazo cikin ladabi,
Cikin muryan nan tashi mai nuna sanyin hali a koda yaushe yace ma Ucheen ya na duk bear dake cikin gidan shi a kwashe su a zubar da su,
Jin maganar Ucheen yayi kamar a mafarki cikin sauri yadago kanshi ya kai wa ogan kallo,
Joseph da kanshi ke duke yana dan kada ruwan zafin da ya zuba a cup,
Batare da ya daga kai ya kalli Uchee ba yace
Yes I Mean it,,,,
Uchee zuciyar shi fam da farin ciki yasamu gara basa, yau,
Duk yawan giyar gidan oga a ce wai ya kwashe ya zubar,
Ba bata lokaci ya kwaso su jiki na rawa yafita dasu gidan,,
Saidai a kasan zuciyan shi yana mamakin ko may yasa ogan nashi ya ce ya fita mai da su gaba daya,,

KB ne ya kira Joseph din wanda duk yinin yau bai fita ko ina ba yana zaune a cikin gidan shi da ke cikin birnin Lagos,,,
Cikin kasala yadauki wayar don bai son yin wani dogon motsi yau,
Hello, KB ya kake ne yau ya, Abuja,?
Yace a lokaci guda sai KB ya amsa mai da cewa lafiya kalau gashi ma zai tafi suleja dibo wasu motocin da suka samu matsala,
Kuma suna dauke da mai a cikin su,
Duk da Joseph din yai kokari wurin bashi amsa sama sama,
Hakan bai hana KB gane cewa Joseph din yana cikin wani irin yanayi yau din,
What's wrong with u, today,,,?
KB ke tambayar shi a karshen maganar su da Joseph din,
Nothing ma,,
Inji Joseph din yaba KB amsa a takaice, kawai, daga haka suka kashe wayan,
KB din ne yadan shiga tunane don saboda dan zaman da sukayi da Joseph yakai kowa na iya gane mood din wanin su,,,
Duk abinda KB keyi hankalin shi na gurin Joseph don shi a zaton shi ko baida lafiya ne
Don yasan cewa ciwon Joseph kamae fitina ce ga duk na kusa dashi,
Saboda irin mutanen da basa ciro ne da wuri ranan da duk zasuyi sai duk wanda ke tare da su hankalinshi ya tashi,
A hanyar shi ta komawa cikin garin Abuja yakara kiran wayar Joseph din saidai wanan karon muryan da dan sauki sosai a saman da zu,
Ejoma, yarinya ce matashiya yar kabilar IBO mazauna cikin garin kwantagora,
Tana zaune tare da yayanta da mijin yayanta wa yanda suka kawo ta garin kwantagora da zama,
Tun bayan gama karatun secondary din ta ta shaku da wani yaron hausawa,
Dan cikin gari shakuwar su ta samo asaline ta yawan zuwa sayen abu da Aminu Aliyu ke yawan zuwa yi a,shagon su Ejoma Ibire,
Har takai sun kulla, soyayya da Aminu din batare da kowa yasani ba,
Sai da abokan mijin yayan Ejoma suka gan su tare shine suka fada ma mijin yar nata,
Ranan tasha fada har d a duka agurin yayyen nata so sai hakan bai masu ba saida suka fada ma pastor don yai mata preach
Duk wanan abin bai raba Ejoma da Aminu ba illa ma kara shakuwar da sukayi so sai ,
Har ta kai Aminu yai mata alkawarin cewa zai aureta
Hakan yasa har ta yarda dashi har suka kai ga kara aikata masha,a a tsakanin su hakan yasa Ejoma ta fara bijirewa yayanta da mijin yar nata,
A karshe saiga ciki, shiko Aminu Aliyu yana jin ta ce ciki gare sai yace ai sam bashi yai mata ciki ba,
Duk yadda yayanta suka so a sulhuta maganar sam Aminu yaki yarda da zancen cewa ai cikin sane,
Hankali duk wani IBO dake zaune ya tashi da jin wanan labarin na zance Ejoma ,,
Ganin haka yasa mijin yarta ya koreta gidan nasu yace saidai ta koma can gurin Aminu,

Wayan shi yake kokarin ajewa bayan ya gama waya da wani Abokin shi da ke zaune a janhoriyar Benin republic,
Inda yake kwadaita mai yadda sana,ar motoci da shimkafar kasar wane ke da riba so sai a harkan,,,
Kiran Samuel ce ta hana shi aje wayan dai yai niya,
Inda Samuel ke sheda mai cewa mahaifin su yana fama da ciwon kafa sosai duk kwanakin nan,
Don har takai ko shago da gidan mai bai iya fita yanzun nan,
Hankalin Joseph din ya tashi sosai don yasan yadda yakanyi fama da ciwon kafar na shi
Sanadin ciwon kafar ya samo asaline tun wani hatsari da yasa mu a saman mashin,
Joseph yakira mahaifin nashi inda yake tambayar shi lafiyan jikin nashi
Amma sai Mr Ema din yace mai a meke ,you, no worry my child,
Na small problem ,
I go manager amm,,,
Yasan cewa zai shigo kaduna sati mai zuwa don akwai wani wanda yake son gani a kaduna din,
Hakan yasa bai cewa mahaifin komai, ba,
Chapter 16 · 0% Book details