← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 171

Sashe 144

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Maryam wace take zaune tai tagumi da hannun ta guda,
Kallon abinda uwale takawo mata acikin roba takeyi,
Gashi uwale tace sai ta shanye shi duk gaba daya, yau din nan,
Safiyace ta shigo dakin inda idon ta ya hango mata abin kamar yadda aka ba ta,
Isa tayi gurin inda ta jawo wani cup dake gefe, ta debo wanan gumbar ta sa aciki,
Bayan ta gama damawa ta dauko madaran peak milk gwagwani guda ta juye a ciki,
Cikin tamke fuska tamikawa maryam din wace ke zaune a gefe guda,
Maryam da bata da wani option sai na ta karba ahaka takarbi cup din a hannun safiya ta fara kurban a hankali tana dan runtse idon ta,
Wani ruwa maikama da ruwan lalai yana kamshin turare a cikin shi safiya takaiwa maryam din a bathroom,
A ranan kusan sau biyar maryam tai wanka da wanan ruwan hadin ga kuma yakin jiki da safiya din da Anty ke tsare ta sai tayi wa jikin ta,
Jikin ta a cikin kwana guda ya sauya kalla, duk da ta ramay amma sai jikin nata yai wani fresh,
Ruwan kanin fari watau, (glove) cike a wani roba mai marfi shi ma tadinga shan shi,
tare da yin tsarki da shi a wanan yinin,
Anty Dije da kanta sai da taga canji a gurin yar kaunar nata,
Takoma wata fresh sai sheki takeyi jikin ta ya sauya a lokaci guda,
Kwana biyu ga naman yan shilan tantabara da uwale ke daho mata daga gidan ta ace wai ita kadaice zata zauna ta cinye, kashi kawai zata bari,
Abubuwa kala,kala aka dinga yiwa maryam din wanda ya kawo mata sauyi, a jikin ta, ita kanta har muryan ta duk taji ya sauya mata ga wani irin kasala wanda ke sata, barci a kai,kai, ,,,,,

Shiri yayi so sai don yasan cewa wanan tafiyan ya na bukatan kudi,
Gashi kuma mai laifi a gurin jama,a da dama bai san yadda zai wanke kanshi ba musan ma yar uwar shi dayake ji da ita Anty dije
Wace rabon da suyi waya da ita tun yana garin kano har zuwa yau bai kara kiran ta ba,
Saboda aiyukan da suka sha mai kai gashi kuma wani sabon magana ya bullo wanda yasan cewa zancen yakai gare ta a yanzu,
Sai kuma mahaifin shi wanda har zancen takaishi ga kwantawa ciwo sai rokon Allah yakeyi, akan Allah yasa ya samu kan mahaifin nashi ,,
Gudu motocin keyi kamar yadda suka saba yi a daji amma shi yau bashi ke tuki ba yazo da mutanen shi don haka, suke jan mota,
Sai lokacin da motar ta doshi garin kamfanin bobi sanan maryam tafadowa Yusuf a rai,
Maryam ya furta a hankali tare da lumshe idon shi da su kayi ma jajir a lokacin saboda stress, da yai mai yawa,
Idon shi ya lumshe a lokacin tare da tunanen abinda ya yanke a tsakanin shi da maryamm din,
Sonny kawai yakai mai can a irin yadda yake jin maryam a rayuwar saboda Yarinya tayi mai a irin yadda yake son mace,,
Komawa yayi yabi lafiyan kujeran motan yana mai lunshe idon shi gami da shafo fuskan shi,
Ba,a dauki wani lokaci mai tsawo ba suka shiga garin kwantagora,
Direct gidan shi suka fara zuwa inda suka dan huta, tukun tare da kokarin neman abinda sukaci,,
Amma banda Yusuf wanda ke jin shi a koshe lokacin baya bukatan cin komai a rayuwar shi,
Driver shi guda wanda yasan gidan su Anty Dije ya umarta da yakai masu tsaraban su kamar yadda ya saba kai masu,
Shi kuma yadauki mota shi kadai yabar gidan ba tare da kowani execute ba,
Gidan mahaifin shi ya nufa kai tsaye ba tare da wani shakkan komai ba,,,,,

Zaune suke a falon su gaba dayan su maryam wace ke rike da wani fresh milk na shanu da uwale takawo mata shi wai ta shanye dukka,
Sallaman da sukaji ne na wani mutun inda, Assalam ya,sheka waje don ya,diba masu kowa ke sallama a lokacin,
Sai gashi da gudun shi yana cewa uncle din shi ya, uncle din shi yazo sai kuma sukaji karan ana,sauke kaya a tsakar gida,
Ba maryam ba har su Anty sai da ga ban su ya fadi , badon komai sai don tunawa,da alkawarin baba na,cewa,duk ranan da Yusuf ya,shigo gari a, ranan maryam zata tare a dakin ta,,
Cup din dake a hannun tane ya ke batun faduwa wanda,safiya tai saurin karban cup din,,
Mikewa,tayi zuwa,dakin su cikin tashin hankali don jikin ta har rawa yake yi, a lokacin,
Sadiya ce ta mara mata baya ganin irin yanayin da aminiyar nata take ciki,
Dafa, mata kafadar ta Safiya tayi tana mai kallon ta,
Maryam ta,dago kan ta a hankali tana kallon safiya din,
Idon ta na silalan hawaye kai safiya ta girgiza mata ta bude baki cikin kariyan murya ta ce,
Ka dakiyi haka pls ki zama mai dauri ga duk jarrabawan da kika gani ga rayuwan ki,
Cikin muryan kuka maryam tacewa safiya amma dai kin ji abinda baba yace ko, ?
Kan,ta ta girgiza cikin kuka tace, wa maryam din ai ba lalai bane maganar baba din yayi tasiri a yau din don shima ai yana da nashi uzurin ko,
Sai a lokacin hankali maryam ya dan kwanta a haka tadan kai kwance ta dunkule guri guda kamar wace ki jin sanyi,
Zuciyar ta fam da tunane da addu,a Allah yasa maganar safiya ya zamo gaskiya,
Chapter 144 · 0% Book details