← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 171

Sashe 127

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ZEE MAKAWA YELWA,,
[4/28, 5:35 PM] ‪+234 902 951 1701‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
7⃣5⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI

Barka da jumma,a yan uwa musulmai masoya novel din furen juji,
Allah ubangiji ya karawa Annabi Mohammad, S,A,W daraja,👏👏👏

Jin hannun shi cikin nata, ya runtse, cikin nashi abinda bai taba faruwa da ita ba, ke nan,
Aiko nan take jikin ta yafara rawa, don wani irin mugun tsoro ne ya shige ta alokacin,
Shiko Yusuf yana ganin haka ya fahinci halin da take ciki hakan ya sanya shi kara rike hannun nata sosai,
A hankali tadago idon ta da suka sauya zuwa na mai kuka, ta na mai wani irin kuka,
Shima kallon nata yakeyi cikin cikin wani irin yanayi,
Ido cikin ido kowa ke kallon dan uwa, wani irin kallo da kowa da abinda zuciyar shi ke fadi,
Kallonta yake yi ita ma dai kallin nashi take tin cikin tuhuma da kaguwa ya sake ta, ba tare da sun daina ba,
A hankali ya dago hannun zuwa bakin shi ya dan subban ta,
Cikin wani irin sauri maryam tai kokarin jaye hannnun nata da yasha riko,
Sai kallon kofa takeyi da alamar kada wani yazo ya riske su a hakan, ta ke wa gudu,
Safiya ce tai murya tankar mai waya tana cewa hello,
Ai ko nan take wani irin kunya ya lulube maryam irin kunyar da bata taba jin shi ba don gani take safiya ta ga halin da suke ciki,
Cikin sauri da wani karfi ta fisge hannun ta yi masa wani irin kallo na don may, tai wani kasa da kan ta alokaci guda
Ko shi Yusuf din sakin hannun ta yayi batare da bata lokaci ba don a zaton shi fitowa safiya zatayi a lokacin,
Ya koma a kujerar da ya taso da farko ya dan kai bayan shi a kai ya kwanta,
Ya na mai da numfashi da sauri da sauri kamar wanda yai wasan tsere,
Jikin shi yaji yai mai wani irin sanyi gaba daya, don irin yanayin da ya riski kan shi alokacin da ya rikewa maryam hannu,
A lokacin safiya ta kara so falon tawa maryam din wani irin kallo cikin wasa tace lalai ma maryam,
May uncle ke fada maki haka da har kika mantacewa ina cikin daki tun dazu,
Gashi har nagaji da jira ki na kai ga fitowa don ba gadin daki nazo maki ba,
Kallon Yusuf din tayi wanda idon shi suke a lumshe tankar ba shi ba ne wanda ya dagulawa kawar ta lissafi har take ba tun kuka,
Kallon shi tayi kamar ta yi mai magana sai kuma ta fasa kusa da maryam ta dan zauna,,
Don ta kawar da shirun da sukayi a falon kowa da abinda zuciyar shi ke sakawa,
Safiya, ce ke kokarin jan maryam da dan fira dan ta sake jiki,
Maryam ta kasa cewa safiya din uffan sai da kai kawai take iya ansa mata,
Ànty ce ta shigo dauke da wani ruba tab da wake mai ruwan milk a ciki,
Maryam wace sai yanzu tai magana tun bayan halin da ta shiga, don haka har sadiya tagaji da fira da ita,
Yusuf wanda ke zaune a gefe batare da yace wa kowan su komai ba ,
Sai tunanen zuci kawai yake yi, a cikin ranshi duk ya dabur ce,
Tsam yamike yana mai yiwa Anty sai anjima jiki ba kwari,
A lokacin da ya isa gidan shi zama yayi saman wani kujera, sai tunane kawai yake,
Zuciyar shi tace mai Addu,a ce kawai ta kamance ka salim,
Ka roki Allah shine kawai zai kawo ma ka mafita ,
Abinda zuciyar shi ta dinga raya mashi ke nan a lokacin,
A take kuma ya amince da hakan, don haka da sauri ya mike zuwa bathroom din shi inda ya dauro alwala,

Itako maryam bayan fitan shi suka hada ido da safiya sai kawai safiyan ta kwashe da dariya
Wani dan filon kushin dake a gefen maryam ta dauka ta jefawa safiya din inda ta cabe shi a hannun ta,
Tana ci gaba da yi,wa maryam, din dariya har da kyalkyatawa,
Anty dije tagane may suke nufi amma sai kawai tashare su tankar ba ta fahince su ba,
Don ta kauda zancen sai cewa tayi dan wake take son yi da wanan waken da aka bata gashi kuma milk colour ne zaifi kyau ga dahuwa,
Sai a lokacin safiya tadan rage sautin dariyar ta tace wa anty aiko zai yi kyau so sai da dan wake ,
Har zuwa yamma Safiya na gidan sai a lokacin Jibrin yazo ya dauke ta ya mai da ita gidan su,
A gogon dake false n gidan ya nuna goma saura na dare yanzu,
Hakan ya ba wa Anty dije tabbacin cewa Yusuf ba zai shigo cin abincin dare ba ke nan yau,
Don haka ta umurci maryam da cewa ta rufe masu gida don dare ya yi ko,
Wanka tayi ta shirya cikin kayan barcin ta wando da riga masu ruwan light green,
Ta daure kanta da ribon kamar kullun takawo gyale dan karami ta daure kan nata dashi,
Zaune take bakin gadon su tana adduan shiga barci kamar yadda ta saba,
Wayan tane yai kara a lokacin alamar kira ya shigo mata,
Ta dan jima tana kallon wayan tana tunanen may zaice mata kuma yanzu,
Har wayan na batun katsewa takai hannun ta tadauka tare da yin sallama cikin wata murya,
Muryan wace ta sa Yusuf, kara rikicewa da jinta har ya rasa irin ansar sallamar da zai mata,
Tunane ya farayi bayan ya karba wayan yana mai cewa,
Shin wai dama haka wanan yarinyar take tun farko ko dai yanzu ne ta koma haka,
Jin muryan ta tana gaishe shi yasa shi saurin tuna cewa a saman layi yake fa,
Ansa gaisuwar na ta ya yi cikin wani muryan da zaka zaci ba ta shi bace,
Shiru, ne yabiyo bayan gaisuwar amna sai Yusuf din yai kokarin kauda shirun nashi,
Maryam ina abinci na ya tambaye ta cikin wani murya tankar ba tashi bace,
Uncle abincin ka yana kitchen mana ko kazo ne mu bude gida,
Sai da yai murmushin jin yadda ta rude a lokaci guda,
Ya ce No na hutar da ke ni ina gidana ai, yau bana jin cin abinci sam,
Kawai sai maryam ta tsinci kanta da tambayar shi ko saboda may ?
Ya ce saboda ke maryam
Yau kin sani a cikin wani yanayi kin ruda min zuciya ta kwata, kwata bani da sukuni yau,
Maryam yadda tayi tankar Yusuf yana ganin ta a fili don nuna kan ta tayi tana tambayar ita,?
Sai da yadan lumshe ido shi tankar maryam tana ganin shi, a fili itama,
Yace Yes of course ke, maryam don kin sa duk na wani susuce akan ki,
Idon ta tadan runtse saboda bakon ya,na yin da take ji a yau,
Uncle din ya koma mata tankar wani bako wanda bata taba gani ba arayuwan ta,
Daga haka yaci gaba da dan mata kalamai masu dadi a hiran nasu,
Maryam wace sam ta kasa sakin jiki da shi sai ansawa da Eh
Ko Um,umm takeyi sune kawai ansar nata da take iya bayar ba,
Harzuwa dan wani lokaci sannan yai mata sallama,
Sannu sannu ya dinga dan jan ta da hira tana dan sake jik wani lokaci tana hira dashi sama sama a kunyace,
Wanan dan kwanakin da sukayi dan sabo maryam ta kara haddace ko waye Yusuf din,
Tsab ta karanta halayan shi saboda shi mutum ne wanda keda wata irin baudadiyar ra,ayi,
Idan har ba sanin halinshi kayi ba da wuya ka iya fahintar shi,
Gashi miskili irin na karshe din nan gashi da saurin fushi,
Abu dan kan kani zai bata mai rai amma kuma sai dai yana da saurin saukowa daga fushin
Ga yin alheri a gurin shi tankar zuban habo daga hanci,
Alherin shi irin ta bajintace, sai gurin da mabukaci na gaskiya yake yake yin ta,
Abubuwa da dama maryam ta fahinta daga gare shi alokaci guda,
Ko dan da farko bata damu da yanayin shi bane saboda kyamar da ta dora mai na gaira ba dalili,

Tafiyan shi yazo kusa don haka ji yake yi tankar kada ya koma a wanan lokacin,
Amma kuma yazama mashi dole yakoma din saboda harkokin shi da ke cen,
Dama abinda ya kara tsayar da shi akan binciken da yakeyi a shagon mahaifin shi ne,
Badon rai yaso ba yai sallama da su ya koma Abuja cikin jin wani iri,
Sai bayan tafiyan shi ne Sadiya tasamu labarin cewa ai ya koma,
Duk tasan cewa wanan zuwan da yayi kawai dai hakkuri tai ta yi don ba wani kulawa da ta samu daga gurin Yusuf din sosai,
Jin shi shiru da tayine ya sa tabugowa wa Jibrin tana tambayar shi ko Yusuf din yana garin KG har yanzu,
Amma sai kawai taji cewa wai ai Yusuf din ya koma, ko
Sadiya wace wayar ya kusa sullubewa daga hannun ta saboda kaduwa,
Hankalinta yai mumunar tashi ta kasa zaune ta kasa tsaye,
Jibrin takara kira tana tambar shi ko may ya fahinta akan ta gurin Yusuf
Bai boye mata komai ba ya fayyace mata a kan zancen,
Wani irin mumunar faduwan gaba taji bayan taji cewa wai yasamu wata
Sai yanzu tagane takuma fahici ko may yasa Yusuf duk zancen shi akan anty je ne,
Idan ita kuma anty dijen ashe makircin da take kullawa ke nan,
Don su mallakeshi su hada,shi da maryam din yarinya karama da ita,
Gumi taji yana fito mata don jin wani irin zafin dake fitowa daga cikin ta,
Ji takwyi tankar an watsa mata ruwane a lokacin
Dije kinyi kuskure a rayuwar ki in har kina tunanen zaki iya rabani da Yusuf a lokaci guda,
Dije sai na raba ku da yusuf sai na dasa tsana da gaba a tsakanin ku,
Takai,wa hannunta guda naushi tana cewa daga yau zan fara yaki da duk wani wanda keda hannu acikin wanan maganar,

ZEEE. MAKAWA YELWA
[4/28, 5:36 PM] ‪+234 902 951 1701‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
7⃣6⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,
YAURI

*_Masoyan Yusuf da Maryam ku kwantar da hankalinku kar hawan ruwanku yatashi, abunda nikeso ku gane shine sadiyafa real lover ce_*😜
Chapter 127 · 0% Book details