← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 171

Sashe 46

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Bakaramin mamaki Joseph yayi ba lokacin da Ibrahim yagabatar mai da sokon da Anty Dije ta aiko mai dasu,
Dambun nama ne cike a roban sai kuma kilishi mai yawa,
Daga kilishin har Danbun Joseph yarasa wani yafi dadi daga ciki,
Sai mamaki yakeyi yana kada kai cikin jin nauyi, kamar a gaban anty din yake,
Shi yana gani kamar ta ksshe kudin da yakai dubu dari akan wanan abin,
Bai daga daga gurin ba sai da ya kira ta acikin waya yana mata godiya daga karshe ma yarasa may zai ce mata,
Mamaki kwarai anty tayi don jin yadda yake zabga mata godiya akan dan abinda baikai yakawo ba,
Shida ta lodo mata tsaraba har saida ta ba makwabta da kuma gidajen su ita da mijin ta,
Amma,shi gashi ko dubu ashirin bata kashe mai ba yata zabga godiya,
Shin shi Joseph din nan wani irin zuciya gare shi ne wai gashi da bawai, yasan kaidar zumunci ba ne a ddini,
Amma yarike ta tam kamar wata yar uwar sa ta ji,
Ita dai fatan ta dai,akullun Allah ya kebo Joseph, yadawo cikin Islam's,
A hankali Joseph ya maida tsarabar anty wani abincin shi na daban koda yaushe yana amfani da abinshi kadan kadan,

Wani irin gurnani take yi wanda har a fili zaka iya jin yadda takeyi wanan karar,
Joseph dake shirin hawa sama yagama kallon national news, a TVC,
Da sauri yai hanyar dakin na maman choima wace ke faman wani irin Gumza takar ana shirin yankar ta,
Da karfi Joseph da Ejoma ke kokarim daga ta daga kwanciyar da tayi tana fidda wanan sautin,
Cikin wani irin kara tabude idon ta tana mai cewa Joseph's da karfi,
Firgigit take kallon su da sauri ta rugumo Joseph din daga jikin ta,,
Sai kuma ta fashe dawani irin kuka tana magana maiban tausayi, cikin kuka,
Tana mai cewa,Joseph they want to carry u away from us,woooo,
Joseph da ya rungumo tsohuwar zuwa cikin jikin shi, yace mata sowaye,
Cikin kuka tace bata san su ba amma tana yawan gani su,,a tare dashi acikin su,, koyaushe,
Sai yaune babban su ya ce har da ita zai wuce in,har tana rike shi,
Shine wanan gumzar da take tayi cikin barcin ta da ihun da take ta kwasa yanzu,
Joseph yadan tallabo kan kakar tashi, zuwa jikin shi yana mai lalashin ta
Tunda yaga cewa tadan kwantar da hankalinta yasamu ya sata kwantawa don ko zata samu barci,
Yamike zuwa dakin shi jiki a sanyaye, zuciyar fam da tunane kala kala,
Ashe haka wanan yar tsohuwar ke wahala idan tace mai tayi wanan mafarkin,,
Hankali shi yatashi matuka yana tunanen may ke shirin samun shine haka,
Washegari, tunda safe Joseph yabar gida zuwa gidan wani babban pastor da ke zaune a cikin Lagos,
Saidai bayan bayanin da Joseph yai mai sai ya umarci da azo mai da wnan tsohuwae wurin shi
Joseph yakoma yazo da maman choima acikin shirinta na irin manyan matan IBO,
Pasto ya riko hannun mama zuwa yan wasu lokota,
Can sai ya sake yadan daga kai yana mai kallon Joseph wanda ke zaune gefen su saman wata far kujera, yana mai rike habar shi da hannu guda yana dan shafa, gemun shi,
Idon da pastor yadan tsura mai baisa Joseph ya canza daga yadda yake zaune ba tun farko,
Pastor yadan kada kan shi yai yar gyarar murya wanda yasa duk suka kura mai ido,
Don jin irin bayanin da zai masu gamay da mafarkin da takeyi,
Mama inji pastor kada ki damu wanwn bawani abin damuwa bane danki zai zama wani abu ne nan gaba shiyasa kike ganin wan nan abin,
Amma,zai bata holy water wanda zata dinga wanke fuskan ta dashi har zuwa sati,
Idan ta kara wanan mafarki sai su dawo, duk kan su,
Sukai godiya Joseph ya kawo kudi yabawa pastor pastor yaka da kan shi alamar aa ba,zai karba ba,
Yace we are just send to help, the, neediest,
Yai masu addu,a a baki dayan su inda sukai sallama dashi zuwa gida,
Tun,daga wanan ranan maman choima ta fara amfani da ruwan holy water, kamar yadda pastor ya umurce ta tayi,

Shiri yakeyi sosai saboda tunda safe yake son takama hanya zuwa kano don dibo wasu kaya da wani tsoho yai mashi tallan kayan company,
Duk shirin da,Joseph keyi hankalin shi na gurin kakar shi wacce ta nuna batason zuwan shi garin kano sam,
Saida ya gama,shirin tsab ya sauko cikin shigar kananin kaya,
Kayan ya karbe shi sosai don ya fitar mai da surar shi tsab,
Karfafan namiji mai duk wani siffa mai nuna karfi daga jikin da namiji
Saidai Joseph ba mutum bane mai son magana don haka ko murmushi da wuya kaga yayi ta, kasafai,
Guda guda yake tako hannu shi guda na acikin ajihun wandon shi guda kuma yana dauke da yar briefcase din shi,
Direct saman kujerar da maman choima take zaune ya nufa inda shima yazauna gefen hannun kujerar,
Yadan langabo kanshi zuwa saman kan maman Choima din,
Mama ,I, gona miss u, wooo,
Kamar yadda yasaba fada mata duk lokacin da zaiyi tafiya mai yar nisa, dasu,
Cikin muryan da tanu cewa ta manyanta tafara magana,kamar haka,
My child , god dey with u,for D whole time , u go spend there,,,
Ejoma dake gefe ta amsa da fadin Ameen,,
Joseph yamike tsaye yana dan gyara, wandon shi, tare da yi masu sallama,
Motar da zaitafi da ita Ibrahim ke ta faman gogewa da kakabewa,
Nan sukayi sallama da ibrahim din yabashi dan kudin da zai yi amfani dasu kafin yadawo,
Adduan dayaron ke mai kullun tasashi jin dadin rayuwar shi aduk lokacin da uai mai ita,
Ahankali ya furtawa ibrahim din da Ameen, tnxs brother,
Yaja motar shi yai gaba yanama Ibrahim horn alamar bye,bye,
Chapter 46 · 0% Book details