← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 171

Sashe 130

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zaune yake saman lalausar kujera guda daga cikin wa yan da ke cikin falon,
Duk hankalin shi na ga Jibrin wanda ke bashi labarin irin yadda mutanen yankin kasar,, kwantagora ke da dawakai masu lafiya,
Da kuma irin yadda matasan yankin ke wasan polo din su a cikin al,adun su,
Da yadda,suke hawan Dabah a garin irin yadda matasa suke kara kawata abin gwanin ban sha,awa,
Sonny wanda sai yanzu yadan gyara zama don yai magana yace very interests,
How i wish to be there ,
Yusuf wanda tun fara hiran tsakanin Jibrin da Sonny bai ce kala ba,
Sai yanzu yadan gyara zaman shi ya daina rubutun da yake yi a cikin system din shi,
Yadago kai yace wa Sonny din ai sai ya gasu da, idon shi zaigane abin da shi Jibrin din ke nufin da kyau,
Sonny wanda da farko yaso yai magana akai amma kuma sai ya ga cewan hakan, shi ya fi don yagani da idon shi,,,
Sai dai kuma matsala guda ce a gurin shi ba komai ba,
Saboda jin da,yayi cewa da mota zasuyi wanan doguwan tafiyan,,
Shiko tafiya ko a cikin jirgi,ne bai son mai tsawo sosai, don baya son zama da yawa guri guda,
Ga shi kuma, yana jin dadin labarin da Jibrin ke mai na al,adun mutanen kasan Kwantagora,
Don haka yaji kawai zuciyar shi na bashi shawaran akan ya tafi yaganowa idon shi komai,
Sai muryan shi suka ji kawai yana cewa
When are we going there ?
Ba Yusuf ba har Jibrin wanda ba wai ya san Sonny din bane da farko
Sai da yai mamakin jin maganan da ya fito a bakin Sonny,
Yadan daga masu gira irin na gogagun yan duniya yace Yes of,course i want to be there,
Yusuf wanda ke sauraren su duk zancen da suke yi murmushi yayi kawai,

Tun safe take, expecting din wayan shi, amma sai taji shiru,
Tuna ne kiran shi takiyi amma kuma sai tana jin nauyin hakan
Amma kuma maganar da Safiya tai mata akan tayi kokarin cusha kan ta gare ko da bata ra,ayin yin hakan,
Don haka taji wani kwarin gwiwa yazo mata a lokaci guda, na takirashi, kawai,
Bata lokaci tadauko wayan ta dake saman gadon ta,
Dialing din nobar shi hannunta, yayi a lokaci guda taji kiran ya shiga,
Har zuwa lokacin da kiran ya katse batare da an,daga wayan ba,,
Tana kokarin aje wayan ne taji kira ya shigo a na ta wayan,
Sai da tai wani dan murmushi irin da ke makalewa a can karkashin zuciya ,
Receiving ta dan,na bayan dan jan ajin da tayi bata dauka ba,
Assalamu Alaikum ta fadi a cikin wani yanayin murya wanda zaka dauka yar larabawa ce ,
Sai da yadan rausaya kan shi daga gurin da yake kadan , sanan ya ansa mata, sallamar ta,
Idanu a a runste tana jin wani abu na fisganta a zuciyar ta wanda bazata iya fassarawa ba,
Muryan shi takara ji kamar mai mata rada a cikin kunen ta yana cewa,
Hajiya maryam barka da warhaka, ya kuke ya yau ya su anty da Family ta ?
Duk sai taji ta wani rude daga kawai jin muryan shi, da ta yi,
Ya fahinci hakan daga inda yake don haka cikin lumshe ido shi, sai ya kawar da zancen da cewa,,
Kin san kuwa cewa dama ke ce nake jira ki, kirani don in tabatar da zargin da nakeyi a kan ki,
Sai dai kashhii, gaskiya zatona ashr ba gaskiya bane a kan ki,
Muryan maryam cikin mamaki take tambayar shi ko wani zargine yake a kan ta, ?
Cikin kashe murya tankar maryqm din tana agaban shi yace
Ina Zargin Maryam, ce da rashin so na sai dai akan tursasawan mahaifin ta da yarta,
A take taji wani irin nauyi da kuma kunya sun lulube ta saboda abinda yace,
Zubewa tayi akan gadon ta sannan ta lumshe idon ta
Bugawar ta zuciyar tana yi don haka tadan sa hannu tadafe gurin a hankali,
Zuciyar nata kawai take iya sauraron bugawan nashi yadda yake karuwa
Tambayar kan ta tayi may zatace mai daidai da ansar da ya dace da maganar shi ?
Cikin wani irin murya taji bakin ta na ce mai amma ai ance zato zunubi ko ?
Cikin yar dariya irin ta kasai,ta Yusuf yace kenan zaton ki nakeyi da hakan ?
Yafada cikin wani irin murya kamar ba tashi ba saboda taushin ta,
A cikin dabara maryam kau da zance don bata san may zatace a irin yadda take ji, ajikin ta,
Ganin zata kawar da zancen yace a hankali cikin muryan nan nashi,
Baki bani amsata ba maryam zaki kawo wani maganar ta daban,
Murmushi tayi wanda har ya ji shi a cikin zuciyar shi,
Wanda har saida ya lumshe idon shi don jin dadin hiran da su ke yi,
Yace to shike nan tunda bazaki fada min ba amma fa ki sani dole sai kin ansa min tambaya na ,
Maryam wace ta sadad da kai kasa cikin jin kuyan tankar a fili suke hiran,
Tambayar ta yakara yi da cewa "Kin amince ?
Da cewa zaki bani ansar tambaya ta ko,
Kai maryam ta daga gami da cewa "eh, tankar yana ganin ta ,
A cikin wani muryan farin ciki taji yadaki wani abu a gurin dayake ,
Ya ce "Great, maryam ko a haka na gamsu da ansar da zaki bani nan gaba,
Nagode taji yace,
Ba za ki taba regrets a kaina ba insha Allah,
A zuciyar ta karba mai da cewa Ameen ya Allah, tana mai dan lumshe idanuwar ta,
Muryan shi taji kamar a mafarki yana cewa Ina son ki maryam,
Son da ban san lokacin da har haka ya shigeni ba a rayuwata,?
Murmushi maryam tayi cikin jin kunya take cewa ai shi so ba sai an san lokacin shigar shi ba,
Idanun shi yadan kara lumshewa yace Really ? Cikin alamar tambaya,
Tagyda kai ta ce kwarai kuwa,,
Cikin wani irin nishadi da jin dadi suka kasance tare a wayan har zuwa wani lokaci,
Ganin lokaci yaja basu sani ba yasa shi cewa maryam har naji bana son ki ajewa yau,
Dariya tayi mai sauti har saida yaji sh a ranshi yai mamaki kwarai yadda akayi yau tai hira dashi haka cikin sakin jiki
Yau zuciyar shi ya tabbatar mai da cewa ya samu karbuwa agurin maryam, fiye da tsan manin shi,,

Dan Allah kuyi managed da wanan nagaji sosai wallahi jiya nadawo daga gurin seminar,👏👏👏
[4/28, 5:38 PM] ‪+234 902 951 1701‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
7⃣8⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI

Zaune yake bayan sun gama waya hannun shi duk biyu a dukule saman habar shi,
Tunane yakeyi na yadda yau maryam har ta sake jiki dashi suka dan dauki lokaci suna online,
Gaskiya har zuwa yanzu zuciyar shi na bashi cewa akwai dai,
Can kuma sai wata zuciya take tambayan shi a kan may zai damu da ko ma may ye, ma dai oho,,
Don haka kawai sai ya ja wani dogon ajiyar zuciya ya furzar da iska daga bakin shi,,,
Duk wanan abinda yake yi Sonny wanda yazo da niyar ti mai magana ya na tsaye daga kofan office din yana kallon shi,
Karasowa yayi inda Yusuf din yake zaune yadan zagayo ta bayan shi,
Sai da yadan dafa shi sanan yake cewa, Yusuf din,
Ina mamaki irin yadda wanan Baby din ta samu sa,an ka haka,
Idon shi yadan lumshe yai, rau da idanun shi cikin rausayawa,
Ya ce, I really love the girl,
Inji Yusuf yafada cikin lumshe idon shi,
Sai kuma yai wani firgigit ya,dago kai yakali Sonny, ya ce,
But she she is a small girl not More than 20 years now,
What inji Sonny cikin wani irin mamaki ya tambayi Yusuf,
Yusuf yadan gyda mai kai alamar abinda yaji ya fadi gaskiya,
What a surprise, ?
A small girl like dis charming your heart ?
Sonny ya tambaya a cikin mamaki yace, kuma tasan yadda zatai handling din ka,
Dariya kawai Yusuf yai mai ya mike tsaye daga inda yake
Sai da yakai wurin window dake manne da office din yadan tsaya yana kallon motocin da ke sintiri a saman titin dake layin,
Cikin wani irin murya mai amon wani sauti na fahinta yace,
That is good characters in my religion, sai kuma ya juyo gurin da, Sonny yake tsaye yana kallon shi cikin mamaki,
Har gaban shi ya karaso gab da shi har suna iya jin numfashin junar su, kamar zasu yi fada,
Yace she is gift for me from Allah,,,,
Chapter 130 · 0% Book details