← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 171

Sashe 34

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau kam churchi ya yayi mugun cika makil da mabiya wanan akidar ta Catholics,
Bukine sosai babu kama hannun yaro anan aka shirya wani kungiya, wanda zasu dinga bi kauyuka suna jan ra,ayin mutane da abubuwan duniya,
Joseph na daya daga cikin wa yanda suka bada gudun mawar su don asai kayayyaki, da za,a rabawa kauyawa, dakuma masu bukata daga cikin su,,,
Wani irin ihu church din yadauka bayan jin abinda sukatara har yafi abinda suke tsanmani samu da farki yawa,
Wani dan gajeren mutum ne tsaye da lassifika yana cewa
"PRESS THE LORD;
Sai sauran su karba mai cikin murnan jin dadi suce "HALELOYA'
Nan take masu kida sauka hau kada ganga duk kowa ya mike akafara wankan JESUS DEY HEAR, HE, DEY,,,,,
Duk wurin yarude da wani irin ihu sai tafi kake ji, da rawa maza da mata,yara da manya,,,,,,
A hankali yazamay jikin shi daga cikin su yana dan tabe kamae may zuwa yin wani abu,
Sai alokacin ya zaro wayar shi daga cikkn aljihun shi yana ta kokarin bidan nobar waya,
Bai tsaya ko ina ba sai gidan, su Ànty Dije, ta kofar gidan gidan ya tsaya yace ace yana wa Assalam sallama,
Anty Dije bata gida maryam cs da yara kawai a gida suna kallo a falon gidan,
Shigowar yaron da aika aiko kiran Assalam ne yadan sa su daga labuken falo,
Maryam na zaune da waya a hannunta tun kusan minti ashirin suke waya da A,A, din ta,
Sam bataji yaron ba har fitan Assalam din sai dai ganin shigowar Joseph da assalam tagani ya na rike gam da hannun shi,
Muryarsa mai,taushi yai sallama da ita tankar musullumi,
Tuni zuciyar maryam ta tsinke, don ta rasa da wani kallama zata ansa mai sallamar tashi,
Mikewa tayi zaune daga kishingiden da take saman kujera,
Ganin da yayi tadan dadirce yasa shi samun daya daga cikin kujerun falon yazauna
Yana mai jawo Assalam zuwa jikin shi cikin nuna kulawa da kuma yar fara,a man,ne a fuskan shi,,,,
Sannu da zuwa ta iya furtawa a lokacin
A dakile ya amsa mata da yaiwa, saboda sanin halin miskilanci irin nata,
Issalam dake zaune tun shigowar shi ta tashi cikin murna ta nufi gurin shi tana cewa Uncle sannu da zuwa, kamar yadda uwar su tace su dinga ce mai,
Wani irin laulausar murmushi yasake mai yar sauti yajawo ta zuwa kusa dashi yana fadin,
Wai, wai, wai Issin mama may aka baki haka kikai girman nan,
Sai a lokacin Maryam tadan kalle shi a karo na farko tun shigowar shi falon,
Cikin sauri takauda kai a zuciyar ta tana fadin Wa,subbahanallahill, Azeem,
Saboda yada taga Joseph yakoma lokaci guda ,
Yazama wani irin, handsome guy, ,sai ka rantse kace ba,a kasar nan yake ba,
Sanye yake da dinkin shadda sai shining shaddan keyi sky colour,
Ga wani sarka da zakai ma kallo guda kagane cewa ta gold ce,
Akawo ma ruwa tasamu bakin ta da iya furtawa a lokacin,
Harara ya dan sakar mata ta gefen ido yace No ki barshi kawai,
Sai yaci gaba da hiran da yakeyi da yaran suna ta kwasan dariya, don jin dadin kasancewa dashi,
Wayan ta ta dauko taima antyn ta text cewa ga wanan kafirin mai zuwa yazo,
Saiga Anty ta kira layin maryam din tana tambayar ta Joseph take nufin yazo ?
Maryam tace eh shine,
Mikewa Maryam tayi tana mai hada kayan wayoyin ta da kuma wani takarda da take dibawa,
Ba,a dauki wani lokaci ba Anty Dije tadawo daga unguwar in da ta tafi karban, bashin ta,
Da murna Anty Dije ta tari Joseph suna ta kwasan dariya ,
Maryam dake daki duk sai taji haushin Anty Dije don may zata dinga washe baki da kafiri,
Sosai yake dan ba,Anty labarin irin abubuwan da suka dan faru dashi bayan wucewar shi,
Maryam mamaki irin shakuwar su tankar yan uwa takeyi,,
Don dai ko yan uwan su da suke mahaifi guda basu shaku da Anty kamar haka ba,
Wanan dibgegen motar da ya aje a kofan gidan su Anty Dije yasa mutanen gari sanin cewa yashigo gari,.
Kafin wani dan lokaci mutane sun farga da zuwan shi,
Abokin Damo, Tsari, sai ga KB da jibrin su ma sun shigo garin,
Abinda maryam bata so shi yadawo don kagin wani lokaci gidan su fam da yan zuwa maula,
Don sun figane masu samay shi a gidan anty Dije bisaga gidan mahaifin shi,
Dayake gab ake da afara azumin watan Ramadan,
Kowa kagani kokarin wanan shirin yakeyi, sam shi da ba musullumi ba bai san cewa wanan lokacin ya gabato ba,
Sai da wani dan uwan Jibrin yazo gurin Jibrin din neman taimakon abin da zai dan sai abinci,,,
Dubu biyar Jibrin yaba mutumin yana mai cewa kayi hakuri akwai mutane da yawa,
Mutumin ya juya yana zabga godiya,saboda dama duk tunane ya ishe shi, ta inda zai dan samu abin da zai fara sayen abinci kafin ai masu albashi,,,,
Haba dai man wanan mutumin fa kamar cewa yayi yanason abinda zai sayi abinci azumi ko,?
Joseph ne ke tambayar Jibrin din,
Jibrin yace haka yace, sai Joseph yadan kada kan shi alamar takaici,
Yo aiko sukarin azumi bazai sai masu ba, haba, haba man,,,
Kiramin shi pls,
Dubu hamsi yabawa mutumin nan ya rasa irin godiyar da zai ma Joseph don murna,
Yau shigan safe yai ma gidan nasu Anty, Dije saboda yana son shan kunun gargajiya da kosai,
Yana Sanye da farar T,shirt anrubuta agaban rigar, snow, da wani jan kala,
Sai dogon wando mai kyau ruwan baki,wani farin agogo ya makala a hannun shi na D&G,
Sai kafan shi dake saye da wani farin takalma rufafu masu kyau gani,
Maryam ce Anty tasa ta gabatar mai da kunu wanda yasha kayan yaji sai kamshi ke tashi,
Da kosai wanda shima yaji hadin kayan markade, da aka soya su tare,
Aikin kullun yake yi waya, don ko zama yayi kafin ya tashi sai yayi waya da kusan mutum ba iyaka,
Yana daga cikkn abinda yakesa shi zama a gidan anty in yana gari don yakan samu time din yin waya,
Tunda tadoso wurin fuskan shi na kallon gefe bayan shi ne,
Tana isowa yajuyo fuska a daure, tamau, yace dan Allah kawo min ruwa mai sanyi pls,
Mikewa tayi bayan ta aje dan tire din da tadauko kayan karin a ciki,
Wani harara ta,dan na masa, alamar kama raina ni,ke nan,
I don't have your time don ni ba yar aikin ka bace,
Azuci take tunanen ta fada ashe, har afili, ana jinta,,,,,
Cikin rashin damuwa yace mata sorry pls just bear with me for sometimes,
Da sauri maryam tabar falon cikin jin nauyi da kunya don sam batai tunanen maganar zai fito fili har yaji ba,
Tun shigewar ta bata kara fitowa waje ba saboda nauyin da taji,
Saidai tana jiwo hiran shi da Anty yana tambayar ta a gamay da azumi, Ramadan dake tafe,
Cikin hikima yakewa Anty Dije tamabayoyi tana bashi ansa yadda yakamata,
Maryam dake waje tana tunanen cewa anty zata sako mai zance addini aciki sai taji shiru,,
Ba wani tambaya ne yakewa Anty Dije ba, illa abinda mai azumi ke bukata, yasamu idan yai azumi,
Saboda azumin mu da nasu ba iri daya bane, don su daga sha biyun dare zuwa sha biyun rana suke azumin su,,,
Bayan wanan maganar tasu da kamar kwana biyu,
Basai ga kaya niki niki wata mota Peugeot mai budaden baya ta,o dasu ,
Sukace Anty Dije akace sukawo wa inji Joseph yace zai bugowa ya suyi magana shi yatafi, Abuja,
A cikin wayane yake mata bayanin cewa ta rabawa mabukata da sukafi bukatar taimako, wa yan nan ka ,,,
Sai kuma ga su gero da sauran kayan hatsi ankara kawowa,
Nan akaita bawa mutane sadaka saboda ba wanda yasan ko daga ina ne kayan suka fito,
Sai daga baya mutane suka fara ganewa cewa Joseph ne ya base taimakon,
Har gida wani mutum yazo yasamu Anty Dije da masifa cewa don may zata yaudare shi ta bashi abin kafiri yai azumi dashi,
Inda yake shiga banan yake shiga ba taso yatara mata mutane,
Kafin ma yabar gurin saibmutane gungu,gungu sunzo abasu sadaka idan akwai (Dan Adam,)
Unguwa unguwa yasa adinga dama kunu da sugar ana bawa almajirai sadaka,
Allahu akbar nan zancen ya tadu a gari cewa ai ya musuluntane kawai a boye,
Saiga shi magana har wurin mutanen su ya kai bayan sun bukaci yazo,
Nan yabugo masu waya cikin bacin rai yana sheda masu cewa ba ruwan su da shi balle su sa mai ido a harkokin shi
Shi yana yi ne "for god sake,,
Don haka bawai su za su nuna mai ga wanda ya kamata ya ba, ba,
Basu gane mai ba ganin cewa yawuce sanin su ko don haka dole suka sa mai ido da halin shi,,,,
Irin abin da yakawo ma gidan su Anty Dije ya ce ta rabawa yan uwan tav abin ba,a cewa komai,
Bakomai yasa yai haka ba don kawai yadda yaga ta kamanta mai gaskiya ga abubuwan kamar yadda yasa ayi,mai,,,
Malam A,A ma ya yowa Maryam kayan shan,ruwa nagani na fada,
Kamar su kayan tea manya gwagwani, millo, sugar eggs, butter, cooker oath, cornflakes, dasauran su kamar yadda akeyi wa mace wace zaka aura wanan sayayyan a kasar kwantagora,
Maryam taji dadin wanan kayan da malam,A,A yakawo mata badon komai ba saidon dama tana kyamar na gurin Joseph,
Duk da tasan cewa dole wata rana tayi amfani da dayadaga cikin abin da yakawo a gidan,,,

Ansa lokacin bukin KB sallah da sati guda don haka abubuwa suka dan cabe w anty saboda tana cikin masu gudanar da tsarin bukin
Duk da gidan amarya sun nuna cewa basu so asa masu Anty Dije acikin har kan su,
Don a cewar su, suma za,su iya gudanar da komi da kan su,
Don gani sukeyi cewa maganar Anty yan matasan ke kokarin bi,,,,
Sun manta cewa mutunci na iya sa komai don dai ita sanadin dantane duk yajawo mata wanan badakalar,,,,

ZEEE MAKAWA
[2/20, 10:31 PM] ‪+234 806 595 8685‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2⃣2⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
Chapter 34 · 0% Book details