← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 171

Sashe 19

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da hannu guda yake tukin motar hannu shi guda yana yi yana shafan fuskan shi a hankali,
Wata bangararen zuciyar shi kuma maganar Aminu ce ke mai yawo a kai,,,
Tsawon lokaci suka dauka yana tafiya a hankali da motar,
Ba, wanda yai ma wani magana tunda suka fara tafiya,daga shi har Jibrin din,,,
Gidan Anty Dije kawai zuciyar shi taraya mai yatafi alokacin,,
Kofar gidan Anty Dije yai parking jibrin baiyi mamakin hakan ba don yasan cewa yakanzo gidan,
Sai a lokacin ya dan kalli jibrin din yace mai, ina son in,gaida sune,,,,
Bayan shigar su cikin gidan sun samu Anty da yara a falo suna karatun hadda,
Nan suka zauna suna kallon yadda anty ke wa yaran karatu cikin fasaha,,,,,
Joseph yana zaune gefe duk sai yaji yaran sun kara birge shi,,,
Saida suka gama ne Anty Dije ta waigo inda suke suka fara gaisawa,
Nan sukan dan fara hiran karatun yarw sai kuma na yanayi dake zuwa,,,,,, saidai hiran duk akan zafin da aka fara ne a lokacin,
Maryam maryam Anty Dije ce ke kwalawa maryam kira a wanan lokacin
Maryam wace ke daki tana gyarawa ta ansa daga can,,,,,,
Daidai kuma lokacin da wayar da ke a cikin aljihun rigarJoseph tai kara,
Aisha ya kike, ?maryam wace ke shigowa don amsa kiran Anty Dije
Idon shi, a lumshe yake magana yadafe goshin shi,
Batare da ta kalle su ba tace Anty gani
Baki gaida mutane ne maryam , ?
Wai may yasa baki iya gaida mutane, maryam, sai a lokacin ya bude idon shi da suke a lumshe,
Ya sauke su ga wace ta shigo falon
Cikin kwantar da murya kamar ta shagwaba, ta dan rusun na tace ina wunin ku, a kunya ce,
Jibrin ne ya amsa mata da lafiya lau,
Jin gudan bai amsa mata ba yasa tadan saci kallon shi inda yake zaune,
Dammmm gaban ta yafadi don gani wanan dan Christian din da tagani kuma gashi da shiga kamar ta yan musulumai,
Shiko ido yazuba mata kamar itace yake kallo, hakan yasa ta wani daure fuskanta ta ma,u,,
Don ita dai gaskiya bata ga abinda zaisa su anty su kama hurda dashi ba,
Sai muryan Anty Dije ya bugi kunnenta tacewa maryam dauko ma su abin sha dan Allah,
In har ba kunnenta ke mata karaba da,zata shigo kamar Aisha taji yace,
Amma kuma sai gashi taji yana kamar magana da maishi ta tsigar soyayya,
Tir tayi da Allah waddai da irin halin wasu diyan musullumai masu kokarin watsar da daranjan su da kima, soboda kwadai, suna, hurda da diyan kafirai,
Ruwa da goran kunun aya, tadauko hade da cups sai dai har yanzu wayar yake yi,
Ji tayi yana cewa ina gidan Anty yanzu haka,
Cikin wani irin mamaki ta kalli inda yake zaune, yadan kwanta Abayan makarin kujerar,
A cikin zuciyan ta tace ji wai Anty Allah ya tsari anty da zama antyn ka,
Kwantacen gidan tajiyana ma wace suke wayar tare,
Gaskia bazata iya zuba ma kafiri ruwa ba,don haka ta dan gware ruwan da cups din tafito,
Amma tana mamaki jin cewa, wai gidan Antyn shi, sai kace wani dan uwar mu, can Allah dai ya raba mu,
Tana tafiya ita kadai har tana tuntube,tana guna,guni, a fili ,,,,,
Ba,afi yan mintina ba sukaji sallama Aisha, tana sanye da wasu materials dinkin redemaid, tasa yellow,
Da wasu takalma masu tsini a kasan su, rataye da wani handbag na company Gucci,,,,
Joseph dake zaune yai mamaki kwarai da ganin Aisha har gidan Anty, don bai taba tsan manin cewa zata biyo shi nan ba,
Cikin girmamawa ta gaisa da Anty Dije duk da bawai sanin ta Anty Dije tayi ba ,sun gaisa a mutnce da ita
Sai ta juya inda su jibrin suke zaune tana mai kallon su, yar karamar harara ta sakar mai,,
Tace ance mun an gan ku,a tudun wada, lokacin Anty Dije ta mike don ta basu guri,
Joseph da sai a lokacin ya iya magana tun shigowar Aisha yace, Anty
Ina son zamu, wuce ,don ina son zanga Dad dina kafin gobe,
Ku bari mana kudanci a binci dan Allah saboda ku na kara yawan shi,
Da wata kasalaliyar murya ya ansa a hankali da kinbari wallahi mun gode,
Jibrin ne yace kai Man ka tsaya kawai kaci abinci don ko mun tafi ba abincin, zakaci ba acan,
Juyawa jibrin yayi yanamai kallon inda Anty Dije take tsaye kusa da kofa ya fara bata, labarin abinda yafaru da Ejoma yarinyar da yanzu haka tana gurin baban Joseph da zama,,,,,,,
Dawowa tayi inda ta tashi tana maimata Innalillahi ,cikin tashin hankali, da nuna damuwa,
Kai kawai take iya girgiza a lokacin saboda tana mamaki, yadda za,ace diyan muna musullumai suna bibiyar diyan arna suna lalata dasu,
Cikin sauri ta kalli inda Aisha take zaune sai wani irin salo takeyi a gaban Joseph,
Nan ta kara yin tir da irin masi rayuwa irin na Aisha saboda kwadan duniya ka wulakanta kanka,
Don dai shi wanda takeyi kashi baima san cewa tanayi ba don ko kallo ta baiyi ba tunda tashigo,
Wanda ma nunawa yayi da bai ji dadin shigowar nataba
Ita dai Anty Dije fatan ta koyau she Allah yasa Joseph ya gane hanyar gaskiya,
Sai a lokacin maryam tashigo falin cikin shirinta na isalamya,
Kallo daya ta watsa masu inda suke gabadayan su,
Wata uwar tsana da takaicin ganin su ya rufto cikin zuciyar ta
Annurin fusakarta duk yagushe, ta bata rai, tana mai murtuke fuskan ta,tankar taga wani mugun abu,
Duk wanda ke falin yaga irin mugun kallon da maryam ke watsa masu a lokacin,
Amma sai suka dauka kila halinta ne hakana kawai,,,,,,,

Barci yake yi amma kuma yana mafalkin garin da yafi kauna lokacin da yake yaro,
Watau garin mahaifiyar shi da yafi kowa kaunar ace za,a tafi wanan garin,
Kusan wata biyu kenan ko yaushe yana cikin ganin wanan nahiyar a mafarkin shi ko kuma tunane,
Don haka yanasa wa ranshi son zuwa ya dibo yar tsohuwa mai munhinmanci tilo guda data rage masu,
Watau mahaifiyar maman su wacr tun suna yara aka hana su zuwa gurin ta cewa wai ita witch ce
Inji dangin uban su, haka yasa busu saba da ita ba sam,,,
Yadda yaso shine sai yaga yadda zancen Ejoma ya kai karshe sannan zai koma Lagos, gurin sanar shi,
Amma sai elders sukace sai nan da karshen wata zasu kara zaunawa,
Don haka yabata gudu taboye yadda zata iya taimakawa rayuwar da abin bukata,,,,,,

Gari ya nuna alamar hadari kamar ,ruwan sama, zai iya fadowa kowani lokaci,
Zaune take da dauri zani a gaba duk da tana da riga a jikinta amma daurin gaba tayi,,,
Wake take tsinta a wani tire maidan fadi, sai wakan su na yan church take rewa cikin wata murya maiban tausayi,
Cikin sauri take aikin duk da ta tsufa,
saboda yanayi, da garin ke ciki don ruwa na iya zubowa ako wani lokaci
Wani kare ne kwance gefen benci da take zaune, daganin shi zaka ce ko shi kadai ake kiwo a gidan saboda koshi,
Jin karan motar da karen yayi yana nufo gidan su shi yasa shi mikewa tsaye yana haushi cikin karfi,kamar zai tashi sama,
Horn din mota ce duk ya ruda gidan yar tsohowar dake zaune a lokacin tana kokarin mikewa don jin yadda karen ta ke ta haushi alokacin, guda.
Jin horn din mota ya tabbatar mata da cewa a,kofan gidan ta ake horn, din
Sam bata kawo cewa bakon ta bane don rabon da ta, ga wani yazo gurin ta har ta manta, lokaci,
Don tun lokacin da diyar take zuwa da mijinta dayaran su idan sun zo daga Arewa,
Bayan fitinar da akayi ita da dangin mijin yarta yasa duk suka dauke kafar su da ita,
Duk da tasan cewa ita ba muguwa bace sheri ne kawi irin tasu,
A hankali ta dan fito daga can ta bayan gidanta inda take girki don taga ko waye a vidan ta,
Duk da girman da yayi da kuma nuna cewa yana cikin daula,
Hakan bai hanata gane jikan nata ba,, a lokacin don rabonta dashi yanzu kusan shekara ashirin ke nan,,,,

ZEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
1⃣3⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

Daga karshe hukuncin da aka yankewa Ejoma baima Joseph dadi ba,
Don Samuel ne yakira shi ta waya kamar yadda yabar mai maganar cewa ya kirashi ya sanar dashi duk yadda akayi,
Don haka yai kokarin samun nobar ta yace ta shigo motan da zai kawo ta Lagos,,,,
Wanan shine silar zaman Ejoma a Lagos cikin karkashin kulawan Joseph,,
Chapter 19 · 0% Book details