← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 171

Sashe 129

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallahn Shafa,i da wutir ta gabatar daga inda ta idar da sallah ta ke zaune tana gyara jikin ta a hankali, tai shirin kwanciya barci,
Ta mike a hankali zuwa gurin shimfidar yaran yayan nata ta gyara masu,kwanciyar su inda tabisu daya bayan daya kamar kullun ta tofa masu addu,oin shiga barci,
AC dakin nasu tadan kunna masu don dakin yadan dauki sanyi kafin barci ya kwashe ta,
Da Bissimillah ta hau gadon ta kwanta a hankali,
Wani irin ajiyan zuciya tasaukar saboda sanyin da taji yana,shiga jikin ta, ga kuma wankan da tayi ta dinga jin tankar ancire mata wani nauyi ne ajikin ta,
Idanun ta ta lumshe gami da jawo bargon ta har zuwa wuyan ta,
Ga mamakin ta karar wayan ta ya shiga yi a cikin wanan daren,
Da sauri ta mika hannun ta tadauko wayan da ke aje a side drower din gadon ta,
Yusuf ne don haka tai mamaki jin kiranshi a cikin wanan dare don bai faye kiranta ba bayan goma na dare,
Da wata karamar murya yakira sunan ta, amma sai tai shiru tankar bata a online din,
Yasan cewa tana jin shi ansawa ne kawai aiki a gare ta,
Wanda hakan na daya daga cikin abin dake kara burge Yusuf din akan maryam watau jan aji,
Din haka yaci gaba da tambayar ta cikin muryan shi maikama da an tilasta mai yin magana,
Kusan hiran hakkuri ya bata najin shi datayi shiru kwana biyu,
Wanda aiki sukeyi sosai shi da Sonny dake kara mai fasaha akan harkokin business din shi,
Cike da farin ciki maryam ke sauraren shi a lokacin amma bazata iya baiyana mai hakan ba a fili,
A karshe yake sheda mata cewa Sonny zai shigo kwantagora saboda ya gan ta,
Sai a lokacin Maryam tai magana cikin yar siririyar muryan ta tace ni ?
Ni ?
Da murya kamar wace zatai kuka a lokacin,, dama yasan haka zai faru don sanin halin ta da yayi,
Jin shirun da yai yawa yasa shi cewa Maryam din dare yayi ta kwanta ta huta dama don yaji muryan ta da lafiyan ta yasa yakira ta
Maryam wace taji dafin abin da yace tadan ji kunya ya dan lulubeta tankar ya gurin haka yasa ta kashe wayan cikin sauri ta koma saman filo ta kwanta rigingine tana tunane,,
Shiko Yusuf din yamai da kanshi saman kujera yana mai lunshe idon shi cikin jin wani irin farin ciki, a rayuwan,
A duk lokacin da yake waya da Maryam shikadai yasan irin yanauin da yakan shiga,
Ya kasa fahintar ko may ye dalilin hakan kasancewa ai ba ita kadai bace mace ta farko da yake waya da ita,
Amma sam bai jin wanan yanayi gurin sauran matan da yake waya da su,

Maryam wace tun suna waya da Yusuf take jin alamar call na shigowa wayan ta,
Amma ba dama ta diba don suna saman network ita da Yusuf, a lokacin badu jin ashhh,,
Jin sako ya shigo yasa ta saurin daukar wayan da ta aje abayan filon ta,
Azaton ta mutumin natane ya yo mata text din Nice, dream,
Ga abinda tagani a rubuce kamar haka,

Maryam kin bani mamaki sosai kuma na yardda cewa kudi suna iya canza mutum ko shi waye,
Amma ki sani kinyi babban kuskure a rayuwan ki na zaban da IBO a matsayin gwanin ki,
Duk da nasan badon Allah kike son shi ba saboda dukiyan shi kawai yarki makwadaciya ta saki son shi,
Idon ta rintse don jin irin yadda ya aibanta mata yar uwa,
Zaman ki ustaziya kamila ashe duk na iya baki ne baikai ciki ba,
Idan har da gaske ke ustaziya ce ai abinda ki ka tsayar hujja akaina ba zai zama hujja ba,
Sai dai ki min uzuri da nasiha akai har in daina dama ba sona kikeyi ba kindai yi amfani dani kin cin ma manufar ki kawai na haskaki gari an sanki,
Idon ta takara rintsewa saboda jin wani irin abuda ya tokare mata zuciya,
Bari kiji maryam da ace wanine zaki aura ba furen kan juji ba,
Wanda daga karshe zaki fada cikin dangin arna ki haifa ma arna jikoki,
Innallillahi wa,in na alaihim rajiun
Abinda kawai Maryam take iya nanatawa ke nan don bazata iya karasa karantawa ba,,

ZEEE MAKAWA YELWA

Anty na Anty Nafisa harzami da maman Farida, Mariya SB Hafsat Yusuf, da duk wani masoyi na ina muna fatan alherin a rayuwan mu,
Duk wanda ban ambaci sunan ta ba ina mai bata hakkuri dan Allah ,,,
Nagode👏👏👏👏👏
[4/28, 5:37 PM] ‪+234 902 951 1701‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
7⃣7⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI

Barcin da gajinyan da take ji a lokaci guda tane mesu tarasa saboda wanin irin bacin rai da ya rufe mata zuciya,
Shi A, A baiji kunyan fadar haka ba akan yar uwan ta,
Sau nawa yana lalashin ta akan taimai hanya gurin Yusuf ko ta fada wa antyn ta akan a taimake shi
Ya samu aiki a Abuja don yabar wanan lecturing din amma ita maryam din ke nuna mai cewa hakan ba daidai bane zubar da mutnci shine,
Amma wai shine yau har zai kira ta da cewa makwadaita,
Ita wani kwadai tayi da har za, ai mata wanan lakanin,
Abinda take gudu ke nan tun farko,daya daga cikin abin da yasa, taki amincewa da zancen Yusuf din ke nan,
Gashi tun duniya basu ji ba an fara mata gori akai wanda ita sam ba laifin ta bane,
Hawaye ne masu dumi suka silalo mata daga cikin idon ta zuwa kumatun ta,
Zaune take a bakin gado kafanta,zube a kasan gado
Idon ta na kallon, kasan dakin kamar wace ke neman wani a bu a kasan gurin,
Mikewa ta karayi tsaye zubur kamar wace aka tsikara,
Hannunta takaiwa nashi da suke a dun kule guri guda,
Ko mawa tayi guri da tashi tafada, da karfi saman gadon tana mai rintse idon ta,
A hankali ta kai kwance daga gurin da take ta zaune idon ta a rufe
Sai kuma hawaye suka fara malalowa daga idon nata,
Daga har dare ya raba a hankali barci ya sace ta batare da ta sani ba,

Anty dije ce ba taga maryam ba,a waje yau don haka ta leka, dakin nasu,
A zaune ta hango ta ta kure guri guda, saman sallayan ta ,
Idon ta da taci kuka a cikin dare yayi sulu, sulu don kukan da taci da dare,
"Maryam a cikin wani irin muryan, wanda ke nuna damuwa,
Anty Dije ta kira sunan maryam din dashi,
Inda tace haba maryam wai ke yaushe zaki fitar da damuwar zancen nan a zuciyar, ki ?
Cikin idon da suka rine mata saboda wahalan da suka sha ga kuka ga rashin samun issashen barci,
Tace Anty ni ban fa sa wani zancen damuwa a raina ba,
Kawai dai fa irin zargin da mutane ke muna na akan wanan zancen,
Murmushi Anty Dije tayi da taji abinda kaunar nata tafada
Takai zaune bakin gadon su maryam din ta dan dago kai tanawa,maryam din kallo,
Tace ni wallahi maryam duk abin da za,a ce bai dameni ba sam,
Don Allah yasan zuciya cewa bana kwadan dukiyan Yusuf,
Don ban taba rokon shi komai ba koda kuwa akan yadda zai tallafawa addinin shi ne,
Maryam wace ke takure gefe guda ta sauke wani nau,yayan ajiyan zuciya a lokaci guda,
Sai a lokacin maryam tai magana tace to amma ai mutane basu gani su,
Don kinga kowa zargin ki yakeyi akai cewa kin sa dukiyan Yusuf a gaba kuma
Badon Allah kike tare dashi ba,saboda abin hannun shine kawai,
Murmushi mai daci Anty maryam tayi a lokacin saboda jin abin da yar uwar ta ce,
Sai dai acikkin zuciyan ta, ta dauka cewa wani sabon fitina yar uwan nata ke son jawo kawai,
Hannu maryam ta mika ta dauko wayan ta dake gefen ta,
Dai, dai gurin text din da A,A ya turo mata cikin dare ta nunawa Anty Dijen
Sai,da tagama karantawa tas sai tai wani dariya mai kama da yake,
Tace to shine may maryam, har kike wahal da kan ki akai, ?
Ai har fiye da,wanan sai ki ji a gurin mutane, balle shi A, A dake ganin cewa saboda dukiyan Yusuf ne kika ki shi,
Maryam ta dago kai cikin kumburarun idanun ta tana kallon Anty dije da mamaki,
Tace to anty shi,,,,,,
Sai Anty Dije ta dakatar da ita daga abinda zata fadi ,, ta alamar daga mata hannun,
Ganun haka yasa maryam yin shiru cikin ladabi tana mai dukar da kan ta kasa,
Cikin murya mai kama da fada ko lalashi Anty ke magana,
Ki kwantar da hankali ki duk abinda wani zai ce ki share mai shi hassada,ne kawai irin na dan Adam ,
In ba,shi ba da iyamuri musulmi da bayerabe da bature ke har balarabe idan ka aura sai anyi zuden ka,
Saboda haka daga yau duk irin abinda wani zai fada ki dake ki shanye kiwa mahaifin ki biyayya kawai,
Kai,kawai maryam ta gyada mata alamar ta gamsu da bayanin ta,
Anty dije wace ke daga zaune tamike tsaye tana cewa maryam din ki tashi ki kama harkan gaban ki,
Ki raba kan ki da tunane haka kada ki sawa kan, ki damuwar da har hawan jini zai kamaki a banza,
Daga haka tabar dakin inda maryam tabi bayan ta da kallo harzuwa lokacin da ta fice, daga dakin,,,
Chapter 129 · 0% Book details