← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 171

Sashe 71

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Kowa agidan sai murnan kudin da ya raba musu su keyi dubu guda guda kamar a mafarki,
Wasu daga cikin sun ne ke cewa maryam gaskiya kin yi dace,
Da mamaki maryam ke tambayar zuciyar ta kamar ya ta dace,
Caraf ta ce masu nifa ba komai a tsakanin mu dashi gaskiya,
Sam basu yarda ba sai zolayar ta sukeyi, suna mata ba,a
Maganganu barkatai suka dinga yi akai kowa na fadar albakar bakin shi,
Sosai lafiya yasamu ga mama wace yanzu take iya yiwa kanta wasu abubuwa,
Mama da maryam ce acikin dakin suna yar hira ta sakanin uwa da , "yar ta,
Yar baba may ke a tsakanin ki da wanan bawan Allah ne wai,?
Cikin wani irin kallon mamaki maryam ke kallon mahaifiyar ta,
Mama tace duk da naga alamar ba wai kina son shi ba ne
Ki daure ki kalli kyawawan dabi,un shi kiyi nazari akai,
Maryam takai wani,,, lokaci tana jimamayn zancen mama azuciyar ta,

Washegari sai gasu shida KB da Jibrin da Assalam
Sai kayan fruit niki,nike da sukazo dashi daga can kwantagora,,
Ranan Dan wake su maryam sukayi da mai da yaji, sai kunun gumba yaji kayan yaji yana ta kamshi,y
Sosai sukaci wananyaci jiyw, danwaken gaba dayan su har shi Assalam din nan yusuf ke masu hiran irin abincin da ya ci jiya da yazo,

ZEEE MAKAWA
[3/12, 10:47 PM] ‪+234 813 139 5577‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
4⃣6⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,

Yan uwa har wayau ina mai kara maku tuni akan barnan da wasun mu ke kokarin yadawa acikin al,uma,
Baidace abin da ke boye mu fito fili kara muna yada shi ba fa,
Musa jin tsoron ubangijin mu da mairubutawa da mai karantawa,
Allah yasa mu gane gaskiya,👏👏👏

Zaune yake a office din shi dake a cikin Abuja, inda yanzu yafi bada karfin zaman shi,
Gaban shi tarin takardune yake dubuwa sai gefe guda inda system din shi yake a bude dagani aiki yake acikin sa,
Baka jin komai sai karan na,urorin sanyin da ke office din suna ta aikin su,
Sosai hankalin shi ke ga wasu takardu da yake diba inda yake nazarin su,
Kokari yakeyi ya kara haffako da arzikin masana,artar shi da Sonny yabar mai shikadai yanzu,
Duk da Sonny din ba,wai yabar masa abanza bane, don abi biyu zuwa uku yabar mashi,
Na farko dai, yasan cewa sun samu riba sosai da gurin cikin dan kankanin lokaci,
Sai kuma kokarin da yakeyi na yabar duk wata harkan business din shi a Nigeria, kwatakwata, saboda rayuwan shi a yanzu a can take don iyayyen shi sun mutu,
Nabiyu kuma yanzu Yusuf ya zama musulmi irin wanda ba guda ba jada baya, hurda dashi zai mashi wuya don yana gudun yazo ya jefashi a cikin kamar yadda shi ya shiga,
Na uku yana tausayin abokin shi Joseph acewan shi don yadda yaga yan church suna ta faman bugo mashi waya akan ya cire shi a harkan shi,
Wanan abin yasa yaga cewa Yusuf ya cancanci yabar mai wanan gurin amatsayin tukwicin zaman da sukayi suna business a tare da dadewa,

A hankali ya dan juya da kujerar da yake zaune yana mai nazarin, takardan da ke hannun shi,
A hankali ya cire glass din dake idon shi ya kara kurawa takardun ido, har zuwa dan wani lokaci,
Bakomai bane sai takardan wani business din motoci ne da suka sawa hannu da dadewa kuma gashi har lokacin business din ya yi,
Sai,dai matsala guda gashi basu tare da Sonny yanzu don haka bai san ya abin zaici gaba ba,
Don dai harkan ba karamin alheri zata jawo masu samu so,sai ,
Bai bata lokaci ba gurin kiran Sonny don ya tunar dashi akan zancen business din da zuwa yanzu komai ya kammala ko,
Kira guda ga nabiyu Sonny din yadaga wayar yana mai cewa A,loo,
Nan dai suka gaisai da junar su suna mai, ya kwana biyu ya aiyuka,
A tsanake Yusuf yai,wa Sonny bayanin komai kamar yadda da farko suka tsara,
Kafin Yusuf yacigaba da bayani Sonny ya katse shi yana mai ce mai, to ai yanzu wanan business din yadawo nashi shi kadai
Cikin mamaki Yusuf ke sauraren bayanin Sonny din don hali irin nashi sai antona
Abinda shi Yusuf bai sani ba shi ne, yanzu Sonny yafi karfin wanan karamin business din,
Don ya na harka da masu hada kwaoyoyi mahaukatar kudi nazo mashi ta ko ina har bai san ya zai yi da su ba
Allah ne yafitar da Yusuf daga ciin wanan har kan kafin abin yai kauri,
Har sunan shi ya shiga cikin bata gari ,
A je wayar yayi cike da mamakin halarcin da Sonny yai mai a rauyawa,
Hannu yadaga sama yai,wa Allah godiyar irin wanan baiwa da yai mai a,cikin lokaci guda,
Ga baiwar samun haske na shiga cikin addinin musulunci dayayi,
Ga kuma ta samun cigabar arziki da yayi acikkn lokaci guda ta yadda bai taba zaton arzikin shi zai kai haka ba,
Wanan samun cigaban yasa Yusuf daukar ma,akata da dama daga kasan kwantagora, saboda cigaban su,
Har mai Sudan saida yasa akakira mashi Yusuf yakara yi mai godiyar irin taimakon da bawa kasan shi tare da taimakawa matasa,,,
Maman Choima yanzu sun dawo abuja tare da Ejoma wace idan baka sani ba zakace blood sister din Yusuf ne ita,
Saboda yadda take taimaka ka mai tsakani da Allah ga al,amarorin shi,
Ejoma ta dade a cikin zuciyar ta tana son ta zama musulma kamar yadda tun tana yarinya take da ra,ayin haka,
Saidai batai dace da musulumin kwarai wanda zai tsaya akanta yaga cewa ta musulunta,
Sai ma baya da yajuya mata don kada ya sha wahala, akanta,
Chapter 71 · 0% Book details