← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 171

Sashe 154

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kwanan su biyu da zuwa Abuja inda maryam a hankali take kara tantace sauki hali irin na Yusuf, wanda sam bai dauki duniya da zafi ba shi,
Balaifi a gurin yan aikin gidan ma suna mutun ta ta kamar yadda ogan su ya umurce su da yi,
Pipkin dai ne har yanzu bai yarda da ita ba don ko da yazo gurin uncle din shi bai kula ta,
Yau ya kasance Monday don haka Yusuf da wuri yabar gidan zuwa office,
Don tun da sukazo ba wqni abinda ya shiga tsakanin su saidai yana kula duk wani moved na ta a gidan,
Sai da tai barcin ta tagaji ta tashi tadan yi wanka,
Atamfane ajikin ta dinkin buje da riga masu ruwan, dark blue da yan adon farare kadan,
A yadda taga table din alama ya nuna cewa ba wanda yaci abinci a gurin,
Pipkin ne ya fado mata arai tunda taji uncle din shi nacewa ba school suna hutune,
To ya akayi har zuwa wanan lokacin bai ci komai ba,
Tsab maryam ta mike daga inda take zaune ta nufi dakin yaron duk da dai bata taba shiga ba,
A hankali ta tura kofan dakin a yadda taga dakin ba laifi komai neat amma kuna dakin yana bukatan kara tsaba ta shi, ga idon ta,
Har zata juya don a ganin ta bakowa adakin sai taga kamar ana motsi a cikin blanket din da ke saman gadon,
A hankali ta isa har gurin muryan yaron taji yana cewa iam testing,
Subbahanallahi marya tace da sauri ta yane bargon inda taga yaro kwance ya dunkule guri guda yana rawan dari,
Hannun ta takai ga goshin shi taji wani irin zafi jikin shi radau,
Rudewa tayi da farko amma daga baya sai ta tuna cewa su Assalam idan suna ciwo kusan itace mai dawainiya da su,
Bathroom tafada na taga dan towel din yaron shi tadauka ta jika da ruwa ta matse shi sama sama,
A hankali ta cire mai rigan jikin shi tafara dan goge mai jikin a hankali tanayi tana taba temperature din shi,
Wani irin ajiyan zuciya taji yayi sai a lokacin ta tuna cewa bai ci komai ba
Sauka ta yi inda ta koma falo ta hado mai ruwan tea mai kauri, bada bread ba,
Daga kwance tawanke mai bakin shi tada shi zaune a hankali,
Mika mai cup, din tayi inda tace mai ya bude bakinshi,
Yaron ya ce, ba zai sha ba cikin kada kai, a hankali maryam ke lalashin shi har yadan sha rabin tea din,
Maryam ta dauko wani riga ta samai sai a lokacin take tunanen ko ina nani din shi ta tafi har tabar shi cikin wanan halin haka,
A hankali ta sauko zuwa, kasa hanyar da take tunanen shine kitchen,
Can tagan su zaune wasu na aiki wasu na gulma, duk da tasan cewa gulman akanta ne,
Suna ganin ta duk sai suka dan rude kowa da irin gaisuwan da yake mata,
Cikin turanci take tambayar da tun yaushe ne Pipkin baida lafiya,
Cikin faduwan gaba yar matashiyar ta dafa gaban ta tace Pipkin o, woo my goodness
Maryam takara jefo mata tambaya ina maganin shi suke,
Maimakon taba da ansa sai kuma ta kwasa tai sama da sauri,
Itama maryam din bin bayan nani din tayi zuwa sama din,
Ganin yadda maryam tai mai har gyara yaron yasa ta cewa cikin rudewa, iam sorry ma,
Maganin maryam takarba da kan ta tabashi cikin hikima da basira har yaron yasha,

Can ko a kitchen bayan fitar maryam din sauran yan aikin biyu dama su mata ukune ke aiki a gidan.
Da ita nani da mai goge da gyaran gida sai wace ki girki,
Bayan sun bita da kallo suka hada ido small girl, sukace a lokaci guda,
Gudan cikin wani ya tsune fuska take magana ,
I wander how Oga managed marry dis girl, na Small girl woo,
How she go do with oga ?
Sai suka sa dariya, dayan tace
Na because of her beauty woo,
Beauty for where dis girl ?
A,a na jealous you dey do
D, girl look fine, woo
She is moderate,
Sai wace ke maganar banzan mai gyaran gida ta wani irin tabe bakin ta wai ita takaici
Sosai ranan maryam ta kula da Pipkin wanda daga kwance yake kallon yadda ta kara gyara mai daki,
Yarone karami amma sai ji kawai matar ta kwanta mai a rai,

YUSUF yana zaune a office din shi maryam ce ta fado mai a rai saida ya wani lumshe idon shi tukun sanan ya furza iska daga bakin shi,
Dagowa yayi daga kan computer din da yake aiki,,
Kan shi ya mayan saman kujera yana dan juyawa a hankali,
Irin surar halittan maryam din ne ke masa gizo a idon shi,
Komai nata kamar ita taiwa kanta, anmata shi wadatace,
Ga ta yar black beauty, da ita ga suma har baya ga dukiyan jiki ta ko ina Allah ya,wadatar da ita shi,
Wayan shi yajawo saboda yana da bukatan jin muryan ta aima yayi kokari don rabon shi da ita tun a Kwantagora,
Saboda yana tausayin kada ya wahal da ita don bata saba ba sai a hankali don ya kula da cewa indan ya kasance da ita, tana wahala da rana,
Wayan maryam din na ringing amma bata daga ba ,
Lokacin tana bathroom din Pipkin tana mai gyara,
Fitowan ta cikine daidai lokacin da kiran ya katse da sauri ta isa gurin amma kiran ya koma miss call
Ganin nomban wanda yakiratane yasa ta maida kiran shi da sauri,
Yadauka tare da ajiyan zuciya yace Maryam kina ina haka har hankalina ya tashi,
Sai da tai murmushi sanan tace ban komai ina gurin Pipkin ne yau baida lafiya.
Dam gaban shi ya fadi don bai son abinda ya taba yaron sam,
Sai yaji muryan maryam na cewa amma yaji sauki har yayi barci ai,
Ina ita nani take da zata bari kina wahala, bana son ki na wahala, da kanki,
Ki kwanta ki huta komai ayi maki bana son ki dinga komai maryam,
Iyakarki ki kwanta ki huta ki kunna A C ,
Maryam wace ta ke sauraren shi tun fara maganar shi,
Sai yanzu ta katse shi cikin murmushi, da cewa uncle nifa mace ce dole dole inyi hidimar gida,.
Ya no, no, maryam hidimata, na kawai zakiyi doni ne kawai dolen ki a yanzu,
Amma ai hidimar Pipkin kamar naka ne ko ? ta tambaya cikin son jin ansa,
Ya girgiza kanshi kamar tana ganin shi yace mata, No" may ye amfanin Nani din shi,
Maryam ni banda ra,ayin matana tai aiki alhalin Allah ya hore min abinda zan biya don ki huta kamar yadda Allah yace,
Kawai aiki gudane daga hidima na sai ta daukan ciki idan Allah ya kawo,
Wani irin kunyane ya kama maryam din don dole badon taso ba takatse layin kiran,
Murmushi yayi don yasan kunyar maganar taji,
Don haka yasan maganin ta zai yi kokari yacire wanan kunyan gaba daya very soon,

Ta gama shirinta tsab jira kawai takeyi gari ya waye basai ta fadawa jikan nata cewa tana hanya ba,
Duk wasu yan tsaraba da ya kamata ta,saye ta saye a lokacin,
Zaune take asaman wani benci dake a gidan ta,
Tunanen mafarkin da tayi da jikan nata takeyi wanda takasa gane ko may hakan ke nufi
Saidai mafarkin yana nuna mata cewa wani abin alheri ne zai samu Joseph din,
Nan ta fara rero adduoi a cikin harshen yaren IBO tana mai yi wa Yusuf din addua,
Rashin shirin shi da mahaifinshi yana damun yar tsohuwar sosai don tasan irin weakedness din Mr Ema din,
Yan kabilan su ko acikin IBO riko gare su kamar bafillacen mutum,
Chapter 154 · 0% Book details