← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 171

Sashe 138

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gajiye yake taka matakal ginan ya na saye da rigar shadda mai ruwan makuba
Dinki rigar iya cinyar shi kawai da yar gutunwar hannu daidai gwiwar hannu,
Saboda zaman da yasha gurin meeting din starching rigan yadan takure , takure,
Kan shi babu hula sai sheki da yakeyi yaji oil ga kamshi,
Hannun shi guda yana a cikin aljihun shi da sauri sauri yanzu yake tafiya don ya isa gurin motar shi,
Tundaga nesa ya bude motar yana isowa yashiga,
Fuskan shi ya shafo da hannushi yakara mayar wa har zuwa wuyar shi wani iska yafurza tare da fadin Ya Allah,
Yana daukar waya kiran anty dije yana shigowa mashi,
Sai a lokacin ya dan yi ajiyar zuciya a irin yadda yake ji, a zuciyar shi,
Sallamu Alaikum Anty Sorry zan kira ki dan anjima kadan pls, ina saman hanya ne,
Bata aje wayan sai fada data haushi dashi cewa zai kashe waya haka har kwana biyu,
Murmush mai sauti ne yadan sake saboda yasan cewa shi mai laifi ne sosai,
Don haka yace gwiwa na a kasa Anty aimin afuwan pls,
Kwanar asibitin da yanufa don diba tsoho ya karya batare da wani dogon tafiya ba ya isa asibitin,
Tsohon yana kwance saida hannun shi guda yana daure da ruwa ana mai kari,
Dan tsohon najin muryan Yusuf ya yunkura da niyar tashi,
Gaba daya har Yusuf din suna hada baki gurin cewa ,a, a, a baba ka kwanta da ruwa a hannun ka,
Tsohon yakoma ya kwanta yana cewa to, to, yana mai gyara kwanciyar shi,
Yusuf ya matso gab da tson inda suka sa mai kujera ya zauna suna fuskantar juna da tsohon,
Alokacin Yusuf yaji a zuciyar shi dama ace wanan tsohon shine mahaifin shi
Dayafi kowa morewa, mahaifi a rayuwa da ba zai iya gusawa nan da can ba a wanan halin da zai tsaya ya kula da,duk wani motsi na shi,
Yana zaunawa wanan tsohon yafara zuka mai albarka ya na mai fatan gamawa da duniya lafiya,
Wani abu ne yazo mai a makoshin shi ya tokare mai yakama jin wani irin tukuki a zuciyar shi,
Da kyat ya samu,ya hade wasu miyau masu daci, da yauki
Sai yar dariyar yake yake yi a fuskan shi tankar ya kai mai ciki,
Kai mutumin wani gari ne ?
Tambayar da tsohon yajefo shi da ita ke nan a lokacin da yake cikin tunanen shi,
Forgigit ya tuna cewa ko shi waye,
Inda har za,a tambaye shi ba zai gushe da fada masu gaskiyan ba kamar yadda ya saba fada cewa Asalin shi FUREN KAN JUJI NE,
Dayan yaron tsohon ne ke cewa ana tambayar ka ko kai mutumin wani gari ne wai,?
Kwantagora ya ba da, ansa, a ta kaice ,,,,
Wai, wai, akwai nisa gaskiya a cikin wani jaha garin yake dayan mutumin ke tambaya,,
A can cikin jahar Niger garin yake, yankin yamma,
Allahu akbar inji tsohon ya fadi lokacin da yake dan gyara kwanciyar shi,
Saida muma zamane yakai mu can asali mu yan jahar,Benue ne,
Gaba dayan su suka juyo da kallon su inda yake cikin mamaki,
Yace musulunta nayi bada dadewan nan ba saboda fahintar musulunci itace hanyar gaskiya,,
Gaba dayan su a lokaci guda sukace Allahu Akbar,
Kan shi ya sunkuya kasa don abinda yake ji, a jikin shi tun jiya,
Babu abin dake a zuciyar shi duk yinin yau kamar yadda zai furta hukunci da ya yanke a kan su,
Dan tsohon nan na kwace cikin cijewa irin ta mai jin jiki,
Tsohon yai ta bashi labarin ko shi waye da kuma yadda ciwon ya samay shi ,
Nan ne Yusuf gane cewa dan tsohon irin malaman nan na zaure ne masu tara almajirai da yawa agidan su,

Zaune take cikin wani yellow material dinkin buje da riga masu kyau,
Dan kwanlishi ba daurawa tayi ba just ta aza shi saman kan tane,
Wayan ta yana a hannun ta tana dan yin game da shi,,
Kirane ya shigo mata sai dai bata gane ko waye mai nombar ba,
Da sallama ta dauki wayan muryan mace ce ke magana a layin,
Maryam taji an anbaci sunan ta, batare da ta ansa ba taci gaba da sauraren mai maganan,
Sai kuma mai maganar bata kara cewa komai ba dan shiru ne ya biyo baya,
Tace baki sanni ba amma dai da zaki gan ni zaki sanni,
Kiran da nai maki shine akan nasaban ki da Yusuf watau Joseph dan gidan Ema mai manja,
Gaban maryam ne a lokacin yabada wani dam haka kawai batare da tasan ko may ye za,a fada mata, ba a lokacin,
Wani,tsoro ne ya lullube ta da sauri tadan kama waigawa ko zataga Anty ta da ido, a kitchen ta hango ta, tana kada miya,
Karo na biyu mai maganar ta kara ambatar sunan maryam din wanan katon kamar mai rada tai maganan
Daidai lokacin da maryam din ta iso gurin da yar na ta take ,
Kada kiji tsoro maryam ki saurare ni da kyau kiji may zance maki, da kyau,
Gaskiya ni bazan iya cutar da mutum dan uwana ba shi yasa naga ya dace in fito fili in fada maki abin da ke gudana akan ki,
Wayan suka zuba wa ido daga ita har yar ta suna sauraron mai magana,
A kofar shiga gidan ku an rufe wani abu wanda daga ke har Yusuf din indan kun taka kun rabu kenan har abada,
Sannan kuma ba zai kara kula koda Anty kiba bale wani naki,
Ke kuma ance a sakar maki ciwo mai kama da ta hauka ko batar hankali,
Don kowa yazaci baki da lafiya ne shi yasa zai guje ki,
Tagumi sukayi suna sauraro sai innalillahi suke ambatawa kawai,
Inda taci gaba da masu kwatancen gurin da aka binzine masu abubuwa akofar gida,
Anty ce ta tambaya cikin saurin jin datayi kamar mai shi tana kokarin rufe wayan ta, da cewa,
A sake cikin sauti mai karfi tace yanzu may abin yi yar uwa,
Mai maganar tace don girman Allah ku rufamin asiri kada ku bari agane cewa nice na fada maki wanan zancen,
Tambayar ta Anty Dije takara yi akan cewa may ye mafitan zancen,
Sai cewa tayi aje daidai gurin da aka bizzine abin a tone tun gudan su bai bi gurin ba,
Don tun daren kwana hudu daya wuce, aka rufe abin agurin,
Kuma wanda akaba kudi don yadiba koda maryam din tabi gurin yace har yau baiga fitan ta daga gidan ba,
Kinga ke nan abin bai fara aiki ba ke nan ko tace cikin nuna kulawa,
A sanyaye Anty Dije takewa mai wayan godiya sosai inda take cewa ai babu komai don duk ciwon musulumi na musulmi ne,
Inda tace insha Allah idan taji wani abu zata kira su ta sheda masu da wuri, wuri,, don su dauki mataki,
Maryam wace tun fara zancen idonta yaciciko da kwalla,
Take,hawaye yafara mata sintiri a idanun ta take dan she,shekan kuka,,
Anty don Allah ku taimaka ku jaye zancen nan tun ba,a halakani ba,
Zan hakkura da Yusuf din don dama nasan cewa ba sa,an yina bane
Kawai dai biyayyane nayi har na takai na fara jin shi a jikina,
A haka ta dinga share hawaye da bayan hannun ta,
Fuska a daure don jin abinda maryam din tace Anty Dije take kallon ta, tace wa yar uwan nata,
Yanzu maryam ina imanin ki da tauhidin ki ya shiga da har zakiyi believed da wanan maganan,
Kiyi imani da cewa duk abinda ya samay ki daga Allah ne maryam ,
Tunda har Allah yasa munji abinda ake yi akan ku kin ga sai kawai mu roki Allah ya kare muna ke,
Da sauri maryam tadan kalli yar,uwar nata tana kada mata kai tace, cikin muryan kuka,
Anty kawai dai a fasa wanan abin ni bazan iya ba gaskiya tun yanzu ace har an fara yiwayiwa mutun irin wanan sherin,,
Tana kokarin share hawayen ta, sheshekan kukanta na tashi cikin tashin hankali,
Murmushi Anty Dije ta yi ta girgiza kai, kaiyya maryam ai idan kince haka sun samu galaba akanki ke nan,
A sanyaye maryam tace cikin muryan kuka, Anty to ya za,ayi,
Anty Dije tace barin kira baba in sheda mashi abinda ke faruwa kafin abu yai nisa,
Daga haka suka bar wajen cikin tashin hankali saboda duk sun shiga rudani,

Yusuf ya kasa wuce saida aka sallami wanan tsoho ya dauke su zuwa, gida,
Badon komai ba sai don ya fidda kan shi a zargin da suka yi mai tun farkon dauko su zuwa asibitin,
Sosai mutanen kauyen sukayi mamakin ganin su tare da mutumin da sukayi zargin cewa dan yankan kaine da farko,
Saboda mugun haduwan da sukaga yayi gashi matashi ga kyau ga kudi kuma,
Nan malam yaroki Yusuf akan don Allah idan an kwana biyu yadawo garin yana da bukatan ganawa da,shi,
Amma kafin ya wuce yasa yaron shi karami yai mai a wani rubutu a ruwa yace yasha,
Yusuf wanda bai, so hakan ba azuciyar shi amma sai ya daure ya sha saboda biyayya kawai,
Da zai tafi yakawo alheri masu yawa yai ma malam da jama,an shi sukayi sallama dashi cikin dadin rai,
Sunkarbi nomban shi don su kirashi a cewar shi idan ya isa,
A hanya ne ya ke tunanen kitan Anty Dije wace yaiwa alkawarin kira tun daren jiya,
Ya so ne da kawai idan ya koma sai ya samu lokaci ya je kwantagora ya fadawa Anty irin shawaran da ya yanke a kan maganar shi da maryam acikin ruwan sanyi,
Duk da yasan cewa akwai rikici a gurin baba don dawuya yadauki yar shi haka kawai yabawa wanda bai san asalin shi ba,
Amma dai shi da kan shi zai fadakar dasu don su fahinta akan Sonny din,
Duk da yasan cewa ko shi don sun san asalin shi dakuma irin cin fuskan da akai mai akan neman mace,
In badon haka ba yasan cewa baza,a bashi ita ba sam saboda su talkawane da suka san mutuncin kan, su,
Chapter 138 · 0% Book details