Sashe 6
Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Tun shigowar su gida, yafara kiran mummy zo kiga kayan da aka sayo min ance inci ni kadai bada kowa ba,
Maryam da ta shigo rike da hannun Issalam ta wani zunburo baki gaba tana cewa wallahi anty in har Assalam na muna haka ni bazan kara zuwa dashi makaranta ba,
Dariya maganar maryam yaba a yayan nata, tace idan baki je dashi ba, ai sai ya zauna dama kece mai daurewa karya ai,
Nan Maryam taba yar ta labarin abin da Assalam yai masu hannu takuma mika mata ledar kayan kwalamar da aka sai mai,
Uwar ta karbe ledan tana cewa aiko bazai sha ko kwara guda daga ciki ba, tunda abin da yayi ke nan,
Anty Dije takarbe ledan ta shiga dashi dakin ta,
Wani sabon kuka yasa yana kokarin turje turje a kasa,
Maryam ce tabi bayan anty da sauri tana fadin dan Allah kiyi hakkuri yaya,
Abashi gobe ba zai kara ba, ai,
Da mamaki anty dije ke kallon Maryam ce ta langabe kai kamar zatai kuka don ankarbe ma Assalam kayan shi,
Sai kace ba ita bace ta kawo karan shi yanzu har tana ikirarin bazata kara fita dashi ba,
Murmushi tayi tana cewa kai Maryam abarki kawai daidai lokacin da maryam din ta karbi ledan a hannu anty,
Ido anty Dije ta bita dashi tana murmushi acikin zuciyar ta tana yaba irin son da yar kaunar nata takeyi wa yaranta,,,,,,,,,,
Afuwan ba yawa pls,,,,,,,
ZEEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
5⃣
BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA
🐎HUGUMA GROUP🐎
Maryam Abdullahi bobi, diyace ga malam Abdullahi bobi,
Asalin , Mahaifin su daga wani kauyen kwantagora suke wanda ake cewa kamfanin bobi,
Su malam Abdullahi yan asalin can ne saida zama yakawo kakanin su a cikin garin kwantagora da a cikin jahar Niger State of Nigeria,
Sana,ar maihafin su shi ne saida kayan masarufi a cikin kasuwa,
Yana da mata biyu inna hussai da maman, tunga,
Saidai da dadewa can ya, auri wata yar uwar shi daga bobi, saidai gaskiya babu so a tsakanin su ,
Don tana da wanda take so a can bobi, don haka ta tada hankalinta bata zauna,, auren bai dauki wani lokaci ba ya mutu,
Ashe akwai rabo a tsakani don haka aka samu cikin maryam,
Bayan haihuwar maryam ne tai wani aure anan cikin kauyen Kampanin Bobi,
Tunda aka haifi maryam sau guda aka taba zuwa da ita gidan mahaifinta,
Duk yarinyar na ran malam Abdullahi amma yasan cewa kawo ta cikin iyalin shi wani sabon fitina ne,
Saboda sun riga sun tsani uwar Maryam har abin ya shafi yarinyar don zuwan da akayi da ita ko kallonta ba wanda yayi,
Sai Dije ce kawai taita nan, nan da maryam din tana nuna kulawar ta akai,
Amma a lokacin Dije tana secondary bata kare karatu ba balle tayi aure,
Bayan kare karatun tane ta hadu da wani dan makwabcin su Iliyasu ma,aikacin aikin custom ne,
Sukayi aure tun lokacin da dije ta tsaida miji tasha alwashin cewa za ta dauko maryam su tafi tare,
Amma sai uwar ta Inna, hussai tace mata sam bata yarda diyar ta ta dauko mata, wata wahala ba can daga kauye,,
Don haka Dije tabar wanan zance kamar ta fita batun sai bayan auren su da ILiyasu ne
Baba yaje dakan shi bobi ya dauko maryam da yan kayan ta yazo ya danka wa Dije ita amana,
Tun wanan lokacin Anty Dije ke kula da yar kaunar ta , ta cikin amana,
Har zuwa lokacin da Allah yabata nata haihuwa,
Assalam.shine nafarko sai Issalam, wace yanzu daga gareta ba,a kara samun wani ba, tukun har yanzu,
Mijin Anty yana zaune a can jibiya ne bakin border don da lagos yake har ya taba zuwa da su sai da anty ta kusa haihuwan Assalam suka dawo,
Inda mahaifiyar shi tace bata yarda ya koma da ita ba , don in yatafi da iyalinshi wai yana dadewa baizo gida ko kuma aike,
Tun wanan lokacin anty ta zauna kwantagora bata kara bin mijin ta abisa umurnin uwar mijin ta,
Saidai har yanzu abin bai canza ba don gwamma da da yanzu don yanzu baifi ya zo sau uku ba a cikin shekara,
Saidai yakan aiko masu da sako akai akai,
Maryan yanzu tana karatu ne a Girls day secondary school kwantagora,
Tana Ss² yanzu su kuma yaran antyn ta sun fara nursery a wani preravent school,,
Maryam ita ba fara bace kuma ba baka ba yar doguwa da ita bata da jiki tana da hanci madaidaici da ido masu dan girma,,,,,
Yau kusan satin shi biyar da barin gari yana can suna ta harkan man fetur,,
Saidai a kai akai suna yawan waya da abokan shi,
Musan man KB da jibrin wanda dama sun fi shakuwa da su tun suna yara,
Don duk irin wulakancin da ake mai lokacin suna yara na kasan cewar shi dan kirstan acikin su
KB da jibri a gaskiya ba suyi mai sukan ja shi zuwa gidan su ,
Idan kuma mahaifin shi yasani a lokacin yai mai dan karen duka,
Har akwai wani lokaci da ana bukin babban sallah yabar gidan su tun da safe zuwa gidan su KB , da kayan shi dunkule a leda a cewar shi zai bi su gurin yawon sallah ne,
A gidan su anyi bidan shi har angaji kasan cewa idan musulimi suna irin wanan buki su kiristan sukan killance diyan su a gida basu bari su fita ko ina,
Hakan yasa shi yin asubancin barin gida zuwa gidan su KB din,
Dashi akayi ai,kin komai na naman inda aka diban mashi zuwa gida dabara yayi da zai tafi yaba KB saura yace ya boye mai
Baban su KB shi yaraka shi da yaga yana labe ,labe
Suna zuwa tun daga nesa uban shi yafara yi mai sababi saida mahaifin KB ya bashi hakkuri,
Wucewan mahaifin su KB kadan akasamay shi akai ta bugu kusan duk wanda ya girmay shi a gidan ranan sai da ya doke shi,
Yana kallo naman da yaje kwadai yai wahalar aiki aka zuba a cikin ruwan kwata aka murje,
Duk da haka washe gari saida ya koma, wurin KB da zai tafi kasuwa yadan dade gidan sanan ya wuce, kasuwa,,
Iya gaskiya shi Joseph yana jin dadin zaman da su keyi da su KB da sauran friends,
Idan yana cikin su ana hira yakan ji kamar an yaye mai wani nauyi duk da ba magana yake yawan yi ba acikin su,
Yadda suke hira ana challenges din juna ko kuma kuma yayi ta kallon yadda mutane ke ta faman zirga zirga,
Abin yana burge shi so sai don idan a cikin yan uwan shi IBO yake sam babu wanan irin dabi,ar sai dai kawai kulun a na gurin bidan kudi,,,,
Shidai dabiar hausawa tana mai a rayuwan shi don in ba haka ba da irin dukan da yasha yana da ya daina kula su,,,,