← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 171

Sashe 153

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan shi maryam tabi da kallo bayan gitan shi daga kitchen din,
Tana mai ajiyar zuciya a filli,
Wanan ne karo na farko tun bayan daura auren su da taji wani abu gamay da Yusuf din,
Zaman kwana biyun da sukayi a gida guda yasa har ta dan fahinci kowaye Yusuf din,
Shi mutum ne mai saukin kai ga kokarin ba natare da shi hakkin shi,
Duk da dai sabon aure sukayi amma tadan fahinci yan abubuwa adangance da shi din,
Itama gudun kada ta makara ta mike ta fada daki ,
Har ta idar da sallah ta zauna tana lazimi a gurin tare da yin tasbihi,
Batabar gurin ba har Yusuf din yashigo yana dauke da basket din abinci da aka kawo daga gidan anty dije,
Maryam din ce tamike tare da bin shawaran safiyan ta,
Saman dining taka kulolin inda tai mai bissimillah cikin jin kunya da nauyi,
Bawani abinci suka ci ba,sosai sun dai dan taba kadan,
Wayan shi tai kara inda ta fahinci cewa da ma,aikatar su ne yaje waya,
Mikewa maryam din tayi tsam tafara kwashe kayan da sukaci abincin zuwa kitchen,
wanka ta fa da Inda tadan bata lokaci gurin gyaran jikin ta cikin bathroom din,
Tana,zaune tana shafa mai da turare, dan gyara jikin irin ta mata taji motsin, shigowan Yusuf din,
Bai wani bata lokaci ba,shima wankan ya shiga don kamar har yafi maryam din tsabta, ma,
Daure yake da bathrobe a jikin shi yana kokarin goge ruwan jikin shi da dan karamin towel,,
Yar jakar kayan da yazo da ita garin ya bude inda ya fito da kayan kamshin shi yakara gyara jikin shi tsab,
Ta mirrow suka hada ido dashi ya wani dan kashe mata ido guda,
Hakan yasa tai saurin dukar da fuskan ta a kasa
Murmushi yayi kawai yaci gaba da,yin abinda yake yi,
Batai aune ba taji muryan shi gab da ita yana cewa yau ina,son in cire wanan mugun kunyar da ake min wayo da,shi,
Murmushi maryam tayi kasa,kasa saboda maganar da ya yi yana kallon yadda take wani takuran kan ta guri guda,
Hannun ta ya kamo yana dan wasa da su can kuma ya dan tsaya yana kallon su kamar mai kallon wani abu a hannun,
Daga haka ya fara canza sallon wasan nashi zuwa wani nau,in,
Sosai ya canza mata sallon don wata irin mahaukaciyar soyayya ya ke nuna mata,
Wanda bata taba sanin anayi wa mace ita ba, duk yadda maryam din yau taso ta kwaci kanta gare shi abin ya faskara so sai,
Yakai wani lokaci manne da ita kafin ya sarara mata,
Don haka yau ma a makare suka tashi don har an kusa tada sallah,
Dasafe suna shirin komawa barci sai ga kira dole tafiya ya kana,su na komawa Abuja,
Sai a,wanan lokacin hankalin maryam din ya tashi saboda bazata yarda da zancen bin shi ba,
Abin da take sakawa azuciyar ta ke nan don haka ita ko a jikin ta shi kawai ke ta,shirin shi abinshi,
Barci ya dan fara kwasan ta ke nan taji sallaman Safiyan ta,
Dole ta bude idon ta da mamaki take kallon safiya din,
Kafin ta kai ga tambayar ta sai ga Ànty Dije tare da yaran ta,
Safiyace ke cewa maryam din wace zatai sammakon tafiya ce kwance abin ta,
Cikin mamaki maryam ke kallon Anty ta tace aiba da ita za ai tafiyan ba, so may zai sa ta tashi yin shiri,
Sai a lokacin Dije ta sa masu baki da cewa kamar ya badake za ai tafiyan ba,
Zaman may zaki zauna nan din yi bayan mijin ki yana can shi,
Ki tashi ku shirya ga safiya nan ,zata taya ki don shi tazo,
Idon maryam ne ya kawo hawaye, a,lokacin amma sai ta daure bata bari ta zubo su ba,
Badon ranta yaso ba tashi ta fara shirin Yusuf yacewa anty ba sai ta tafi da kaya ba don zasu saye a can idan sun tafi,
Yan abubuwan sirin ta dawasu daga cikin kayan tada take so ta dauka,
Maryam na gani tabar yan uwan ta da mahaifan ta da Anty ta da yaran ta,
Aminiyar ta Safiya tana daga mata hannu duk kan su idon su ya kawo hawaye don rabuwa,
Haka ma suka wuce garin mahaifiyar ta tana kallo babu daman shiga,
Aure ke nan ta nisa a hankali don shi yakai can,
Yusuf din ke jan motar da suke ciki da kan shi inda ya ke tuka su a hankali,
Basu yi wani nisaba sosai barci ya dauki maryam din,
Yadda yaga tadan kwantada kanta saman glass din motar sai ta bashi tausayi,
Don yasan cewa tana tare da gajiya don ba karamin wahala yabata ba, a daren jiya, din,
Yadan lumshe idon shi saboda abinda ya tuna a zuciyar shi,
Sun isa gidan shi na Abuja lafiya inda ya yan aikin gidan suke ta faman yi mai sannu da zuwa,
Babban falon gidan ne suka sauka inda sukaya da zango,
Maryam wace sai kallon wanan gidan may kyauwo take yi a sace,
Irin yadda masu aikin suka tare ta yasa maryam din jin dadi,
Wani yaro ne ya sheko da gudu daga cikin gidan ya saye da,wata yar farar riga ga karamin wandon short niker, ajikin shi
Yana cewa you are welcome my uncle,
Daga shi sama Yusuf din yayi yana cewa miss u, my Pipkin,
Maimata sunan maryam tayi tace a cikin zuciyar ta Pipkin,
Da sauri ta daga kai ta kalli yaron inda ta ke mai kallon kurullla, ita ma,din,
Yusuf wanda a yanzu ya rage dan tsawon shi daidai tsayin Pipkin din,
Ya nuna ma Pipkin din maryam wace ke zaune a lokacin,
Murmushi tasakar wa yaron da sauri, yaron yadan boye bayan Yusuf din,
Ciin kunen Yusuf din yake magana a hankali yana cewa,
Uncle who is she,?
Yusuf yakara nuna maryam din yace she is your new Mumm,
Go and greet her,
A hankali yaron ya fara tafiya zuwa inda maryam din take,
Kamar ba zai yi magana ba yace a hankali you are welcome mum,
Jawo hannun yaron maryam tayi zuwa jikin tana cewa how are you Pipkin?
Yana tafiya yake bata ansa da cewa iam fine,
Murmushi maryam ta bi bayan yaron dashi don ganin cewa wai wanan yaron dan Naimat ne,
Abin sha aka kawo mata tare da dan abin tabawa,
Abinda hankalin maryam yafara kaiwa gare shi da farko shine ganin masu dan buje dake kai da kawowa agidan,
Kalman nan da A,A yace ma don zata auri FUREN KAN, JUJI,
Shi ya fado mata arai tana mamaki ya akayi duk irin son addini na Yusuf zai zauna da irin wa yan nan a gidan shi,?
Wace yakira da,sunan NANI RUTH itace yace takira mai wayan nan masu aikin gaba dayan su,
A gaban shi suka tsaya acikin natsuwa inda ya gabatar da Maryam gare yace masu matar shi ce,
Daga yanzu itace matar gidan don haka duk wani tsari yanzu ,daga gareta zai fito,
Suka ansa da fadar yes sir tare da kai kallon su caaa ga maryam din wace ke zaune cikin kamala da mutunci,
Duk da karamace amma sai ta cika masu ido, Yusuf ya umurci Nani Ruth da takai mata kayan ta dakin dake facing din nashi na Pipkin,
Da saurin ta ta wuce dauke da dan trolley din da yan kayan maryam ke ciki,
Wanka tayi daga can ta dauro alwala tare dashirin gabatar da sallah don azahar har la,asar duk ya wuce su,
Bayan ta idar ne tadan tashi takara bin dakin da kallon dakin acan acan, dashi yai mata kyau sosai, sai dai tana ganin yai mata girma ita kadai,
Kofan dakin aka turo Yusuf ne wanan karon shima yai wanka ya sauya kayan shi zuwa wasu fararen simply material na maza,
Inda take ya karaso fuskan shi dauke da murmushi ,
Matse ta yayi ajikin shi har sai da yaji ta sauke numfashi ajiyan zuciya sanan ya,sake ta,
Bakin gado yaja hannunta suka zauna, yadan daga kai ya kalli dakin yace maryam wanan shine dakin ki da fatan zakiyi manage dashi kafin in samu time ai maki gyaran yadda ya kamata,
Kallon shi tayi har yau acikin jin nauyi tace babu wani gyara da za ai yi anan is ok hakan ma, ai,
Hannu ya daga mata yace Nop is my responsibility in gyara maki komai kamar yadda nai alkawari,
Don haka maryam din bata kara cewa komaiba sai cewa da tayi, nagode a hankali,,,,,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA,,,,,,
[5/4, 7:10 AM] ‪+234 703 055 6607‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
9⃣1⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,
YAURI

RAMADAN MUBARAK MASOYANA ALLAH YA SADA MU ALHERIN DA KE CIKIN WANNAN WATAN MAI ALBARKA
ALLAHUMA AMEEN 👏👏👏👏👏👏👏👏
Chapter 153 · 0% Book details