← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 171

Sashe 139

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Zaune take a gurin da tagama sallah isha,i amma tunane duk ya addabe ta azuciyan ta,
Ba komai take tunane ba illa ta yadda za,a bullowa wanan bakon al,amari da yazo mata,
Don dai ita a iya sanin ta batada abokin fada ko kuma hamayya, ako ina,
Amma wai sai gashi kwatsan an wayi gari ana son a cutawa rayuwan ta,
Wayan hannun tane ta daga don ta diba time, tagani, saboda tasan cewa da zaran angama sallah isha,i baba zaizo,
Takwas da rabi taga don haka tamike tafara dan tattara kayan da tai sallah don kada baba yashigo bata a falin su,,

Falon yai shiru, baka jin komai sai muryan Anty Dije kawai da ke koro wa baba da bayani tiryan tiryan,
Kamar babu kowa a falon bayan ita, kowa da irin nazarin da yakeyi, daga baba har aminin nashi da sukazo tare,
Maryam ce a gefe guda tsugune sai hawayen da take zubarwa akai akai,
Baba kan lumshe idon shi yayi saboda mamakin yan Adam daya kama shi,
Yasan cewa Allah ne ya kare mashi yar nashi saboda addu,oin da yake yawaita yi musu, akai akai,
Yarinyar tana bashi tausayi saboda yasan cewa akan shi ce tai biyayya
Wani irin mugun tausayi tabashi da yadan kalle ta da,wutsiyan ido yaga irin yadda take share hawayen dake sintiri a idon ta,
Abokin baba ko ince aminin shi kuma makwabcin su, yai murmushi cikin gyada kai bayan ya gama jin bayanin da Anty tai masu kaf,
Yadan kalli inda baba yake yace, ina kon kwanto, amma ai babu komai idan har sun san wata aibasu san wata ba,
Don kaga Allah ne ya tona masu asiri don ya wargaza masu plan din su,
Amma zasu sha mamaki don ta Allah batasu ba sherin su zai koma masu,
Sallama sukayi wa su maryam din suka tafi tare da kwantar masu da hankali na cewa babu abinda zai faru da yardan Allah,
Hakan yasa hankalin maryam ya da yar uwanta ya dan kwanta amma ba wai gaba daya ba,
Koshi saboda sanin da sukayi wa shi malam na ngaski din ne cewa bakanwar lasa bane shima,,,,,,

Masallacin Jumma,an ya cika saboda anan sarki ke sallah da sauran dattijan gari,
Mahaifin jibrin da yawa daga cikin makwabtan su suna acikin sahun da suke kusan gaba, gaba,
Bayan an idar da sallah jama,a suna kokarin wuce wane sukaji wani bawan Allah mai zakin harshe yana cewa don Allah a,dakata ,
Akwai daurin aure ga wanda Allah yaba ikon tsayawa,
Hakan yasa jama,a da dama suka dan dakata don su sheda wanan daurin auren, da akai shela,
Mahaifin Jibrin tare da, malam Abdulsamad suka matso kusa da liman nan shima Mahaifin su maryam tare da sauran yan uwan shi har su, mijin mahaifiyar ta da ya aikawa yana son yazo ciin gari a yau,
Yakuma zo din duk suna gurin su malam A, A da su KB wanda shima yazo garin saboda matar shi da take dauke da tsohon cikki,
Anan ka gudanar da shardan aure kamar yadda aka sharida wa musulumi, ci, da sha da sutura,,
Sanarwa kawai sukaji mai fada na fadin cewa an daura auren Yusuf da maryam akan sadaki naira dubu hamsi, kacal,
Inda mahaifin Jibrin din ya gabatar da kudin a hannun waliyin auren maryam din watau mijin mahaifiyar ta da malam aminin shi,
Ba,a dauki wani lokaci ba wasu mutane suka gane ko auren wa akadaura a lokacin,
Ciki har da A,A dasu KB da sauran abokan hurdan Yusuf din,
Ba,karamin mamaki mutanen da suka halarci daurin auren sukayi ba don basu da wani masaniya akan zancen auren, shi,,,,,,

ZEEE MAKAWA YALWA,
[4/28, 5:40 PM] ‪+234 902 951 1701‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
8⃣3⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,
YAURI

YA,Allah, Ya Rahaman Ya Rahimee, Ya Maliki, Ya Salam, Ya Fattahu, Ya Haiyyu, Ya Kaiyyumu, Ya Malikil, Mulku,Zullani Wal,ikiram,
Allah kasa mudace ya,Allah kasa mugama da duniyan mu lafiya, Allah ka rahama muna,👏👏👏👏👏

Kiran layin wayan shi yake yi a gagauce tun bayan minti goma sha da suka wuce,
Amma layin baya shiga sam switch, off suke cewa tun dazu,
Ba halin shi bane hakan sam rufe waya don haka yake mamakin abinda ke faruwa,
Layin Jibrin ne yakira don ya ji ko Yusuf din lagiya yake ya kashe duk layin wayan shi,
Kira guda layin Jibrin din yashiga sallama tare da yar raha kamar yadda,suka,saba,
Amma wqnan karon Jibrin din kawai keyi shi KB yaki mayar, mai da martani kamar yadda,suka saba,
Sosai abin yabashi mamaki don ba irin haka suka,saba yi a tsakanin su ba,
Kai ina mutumin yashigane wai duk wayoyin shi a kashe tun dazu,?
Au Yusuf kakw magana gaskiya ban da masaniya don dai jiya yana hanyar shi ta,dawowa kano mukayi magana, dashi,
Amma yanzun nake son daga nan mosque in wuce gidan shi in mai sannu da zuwa,
Ke nan kana da labarin auren shi kai ko ?
Ban fahince ka ba in Jibrin wanda tambayar ta KB tazo mai wani iri,
Aure ?
Wayai aure kake nufi wai ?
Ansa yabashi dace wa wai kaima kana nufin kace min baka da labari,
Bayan mahaifinka ne yai waliyin auren da aka daura mai a massalacin jumma,a dazun nan,
Mamaki kwarai Jibrin din yayi sai kuma ya kama tambaban ko da wace ce aka daura auren,

Zaune yake a gidan inuwan wani ice dake cikin gidan man nashi can gefe guda , yana kallon duk wani mai shige da fice a haraban gidan man,
Mutun biyune saman wata tsohuwan mashin suzuki blue,
Tunda Mr Emanuel ya hango su ya daure fuskan shi,
Saboda suna daga cikin masu zuwa gurin shi yawon maula,
Hakan yasa yana hangosu ya daure fuskan shi saboda yana bakin cikin irin wanan halaiyan na irin mutanen nan masu yawon maula,
Gaisuwa,sukafara dashi tare da tambayar lafiyan jikin sh,
Daya daga cikin mutanen ne kecewa Mr Emanuel din wanda ya,daure fuskan shi tamau, don kada su ji dadin rokin shi,
Mutumin yace ashe yaro ya yi aure shine muka ce bari muzo muyi ma murna,
Mr Ema yace cikin kada kan shi wa ?
Ummmmm, Ummm ba yalo namu bane,
Shiru mutanen sukayi sai zuwa can gudan yace yaron kane mana wanda ya musulunta kwanakin baya,
A,a yana kada kai alaman bashi bane, cikin daurewa fuska,
Mutumin ya dage da cewa shine fa wanda akecewa Yusuf Joseph,
Gaban tsohon ne yaba ba da damm, saboda bai taba zaton haka daga dan nashi ba,
Indan ko har hakane plan din su akan Yusuf din ya rushe ke nan,
Don tun da har yaji cewa anyi aure tsakanin shi da diyan musulmai, yasan cewa mawuyacin abu ne, kuma ya dawo cikin su ,
Don haka bai tsaya sauraren wani abinda zasu ce ba yadogara sandar shi ya mike tsaye,
Fuuuu yabar gurin batare da ya tsaya takan mutanen ba,
Inda haushi yakama su don su azaton su zasu samu kyauta a gurin shi,
Chapter 139 · 0% Book details