← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 171

Sashe 45

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali maryam ta ajiye, plate din da ta debo abinci, agaban Anty nata,
Wacce ke kwance saman dogon kujerar da ke cikin falon nasu,
Anty Dije tadan dago kai kadan ta kalli maryam wace ke kokarin juyawa don komawa dauko ma yar nata ruwan sha,,,
Cikin murya ta wanda je jin jiki Anty tace wa maryam ,
Maryam ba,zan iya cin wanan abincin ba don sam bakina bai min dadi wallahi,
Cikin dan marairaice murya Maryam tace anty dan Allah ko kadan ne kidaure ki danci, zaifi rashin cin da bakya, son yi,
Da taimakon maryam Anty Dije tadanci abincin kusan spoon, hudu, gana biyar ta mayar tana mai cewa ta koshi,
Bazata iya karawa ba haka don ji take tankar zata amaye dan wanda taci,
Gudun kada tai amai Maryam ta kyale yar nata tana mai tatara plate din zuwa kitchen,
Ido Anty tabi maryam dashi tana mai jin dadin irin kaunar da yar uwar nata ke yawan nuna mata ita da yaran ta,
Ringing Tone din wayar Anty Dije ne ya karade gidan nasu a lokacin,
Da sauri maryam ta isa inda,wayan take tana ruri, don ganin mai kiran yar uwar nata,
Yusuf Joseph tagani baro,baro a screen din wayar,
Kurawa wayar ido tayi har saida ya katse don kan shi,
A hankali Anty tadan dago kai daga inda take, kwance tana son tasan kowaye ke kiranta ya katse,
Don tana,son kaunar nata ta fada mata kowaye a layin,ke,kiranta,
Tana kokarin aje wayar ne wani kiran nashi yakara shigowa again
Dole ta nufi inda Anty take kwance, da hannu take mata tambayar waye akan layin,
Joseph tace tana kokarin kara mata wayan a kunen ta,
Da hannu taimata alamar, ta dauka kawai sai ta maida kanta saman hannun kujer a hankali,
Cikin muryan mai,kama da ta maijin kasala take magana,
Hello, ina wuni ?
Mai wayar batada lafiya ,
Juses crisis,
Dif maryam tayi tana mai cewa wa,iyazu,billlah,
Jitayi tankar ta aje wayan do haushi,
Sai jin shi tayi yana cewa may yasa may ta haka,
Zazzabine ke damun ta yau kwana biyu ke nan,
Jin wa,iyazu,billah da tafada dazu yadan sosai mai rai don yasan kalmace ta nuna wani tsari ga tsanar, abu,
Don haka yanzu sai yadan gyara harshen shi da cewa ayya sorry fa ina gaisheta pls anjima zan bugo mata,
Kagin ma ya kashe har maryam ta kashe wayar bin wayar yayi da kallo,
Sai mamaki kuma yake a ran shi cewa may yasa musulmai ba su iya boye felling din su in suka ji an ance Juses,a gaban su,
Maryam ko a hankali ta juyo gurin Anty tana fada mata abinda yace mata,
Yinin ranan duk a kwance anty ta ti shi saboda yanayin jikin ta duk ba dadi,
Ganin tana wahala da yawa yasa maryam bugawa yaya illiya waya tana sheda mai abinda ke faruwa xa yar uwar nata,
Wace duk kwanakin nan akwance take bata jin dadin jikin ta,
Ga wani amai dake zo mata yanzu duk abinda taci sai ta fitar dashi koda ruwa ne,
Hakalin Maryam ya tashi sosai cikin dare da Joseph yabugo muryan ta kamar na mai kuka take mai magana,
Tana sheda mai yadda ciwon ke matsawa yar uwan ta yanzu sosai,
Shiru yadan yi nawani lokaci har maryam din na,,zaton ko cewa ya kashe wayan ne,
Tace cikin siririyar murya, hello,,
Yace ina jinki kunje asibiti, ta girgiza kanta alokacin kamar yana ganin ta tace a,a
Saidai zuwa gobe insha Allah zamu tafi yaya yau ya bugo waya yake cewa mutafi goben,
Ok to barin yi magana da shi Illiya din tukun 'I will call you back,,,
Ok tau nagode tace tana mai kokarin aje wayar a lokacin shikuma yana mai ce mata ina Assalam yana lafiya ko?
Cikin kosawa da yin wayar tace mai yana lafiya sai anjima,
Itace kuma still dai ta,katse wayar kamar yadda ta yi dazu
Yai shiru yana dan mamakin irin halin Maryam na rashi son mutane
Yasaki ajiyar zuciya yana mai kara nazarin ta,
Tuna wa yayi da zancen kiran illiya don haka nobar shi ce ya kira,,
Bayan sun gaisane yai mai jajen ciwon matar shi sai, ya,kecewa
Dama ya bugo waya ne don ya tambaye shi ko yana iya tura mai doctor lawal yadiba matarshi
Don yadda akace mai tana jin jikin har ta kasa daukar waya daya kirata,
Ya, illiya yai murna kwarai da wanan taimakon da Joseph yai mai na turawa har gida a diba mai matar shi,
Saida Doctor Lawal ya iso gidan sanan Joseph yakira yake sheda masu cewa gashi nan shigowa,
Mamaki ne yakama maryam sosai don ganin cewa yasan yadda shari,ar musulunci yace ayi,
Am.a kuma da,tai tunane saitaga babu mamaki don yana tare da su jibrin yau da gobe dole yasan komai,
An mata allurai dakuma yan magunguna, sai fitsarin ta da akace akai gobe,
Bayan fitar doctor dakamar yan min tina sai,gashi ya kara kira yana tambayar ta
Ta girgiza kai tace ban san may doctor yace ba yadai mata allura,
Nan yai mata sada safe yana mai jaddada mata cewa ta tabbatar da cewa Anty tana shan maganin ta,
Joseph yaso ya shivo saidai yana tsoron irin masifar da tsohon shi ya za,zaga mai,
Inda ya bashi umurni da cewa indan har bashi yace yana son yazo ba kada ya fara yashigo garin kwantagora,
Tunda badon su ya haife shi ba da zai dinga kashe masu kudin shi abanza hakana,
Fada sosai yaiwa Dan nashi lokacin bukin KB da sukayi inda labarin komi yazo kunen Mr Ema din a lokacin ne yai kamar zai daki Joseph din don haushi,
Jikin Joseph a sanyaye don badamar zuwa yadiba halin da Anty nashi ke ciki, don gudun masifar mahaifin shi wanda sam bai son hurdan shi da yaran varin da yake amfana dasu,
Hannu yasa yadan shafo sanjen fuskan shi da ya kwanta mai lub a fuskan,
Ya furzar da yar iska mai dan dumi daga bakin shi,
Ibrahim ne yafado mai arai don haka yatadashi inda yai mai shatar mota zuwa kwantagora da kayan dubiya irin ta marasa lafiya,
Anty Dije tayi mamaki kwarai da irin kayan da Joseph ya bayar ,akawo mata tundaga Lagos har KG,
Lemo, Abarba, Ayyaba, Apple, kwakwa, carrot, water millow, pears, da,sauran su bar manja da garin can saida ya siya mata,
Waya anty tasa aka bugawa Joseph tana son tsi mai godiya na taimakon da yai mata, ga likita ga kayan marmari, da yayo mata,

Likita ya tabbatar da cewa Anty Dije tana dauke da shigar ciki na wata biyu da da kwanaki,
Maryam tafi kowa murna da wanan labarin cikin, wanda har uwar mijin ta tafara zance wai ya karo mata tunda anty tabar haihuwa,
Da sun dan samu matsala dasu yanzu zasu fara mata gorin taki haihuwa kuma ta hana auri wata,,,,

ZEEE MAKAWA
[2/21, 9:16 AM] ‪+234 806 595 8685‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2⃣9⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,

Yan uwa musulumai ina mika gaisuwa gare ku ,akan wa yan nan yaran makaranta yan garin misau da ke cikin jahar Bauchi da suka samu harin mota ta hanyar su zuwa kano ziyarar Arewa 24,wanan satin da yagabata suka mutu su ashirin ta re da malaman su,,
Masoya TAKARI novel da FUREN JUJI ina fatan za muyi masu adduan fatan samun Rahamar ubangiji, tare da mika ta,aziyar mu ga yan,uwa, da, iyayyen wa,yan nan yara, Allah ubangiji kasa Aljannan Fiddausi tazama makomar su,👏👏👏👏

Mahaifin , Ibrahim Abdulsamad, yaji dadin yada yaga dan shi ya koma cikin dan kankanin lokaci,
Bakamar yadda suke zube a cikin gari ba da babu mataimaki,
Babu wanda ma yasan cewa suna cikin wani halin bukata na rashin yan uwa da galihu,
Yana ji yana gani matar shi ta gudu mai da yan shi mata, zuwa kasan su,
Wanda bakomai yasa shi kyaleta dasu ba sai tsabar yawan talauci dake cin shi,
Ki abinda zasu ci tunda yai gobara shagunar shi suka kone kurmus,
Amma sai yara,daya daga cikin musulmai wanda zai taimaka mai da wani abin,
Gashi har zuwa yanzu yan uwan shi na da suna kawo mai tayi akan ya koma akidar shi tafarko,
Babu komai acikin wanan sabuwar akudar da yadauko, illa wahala,
Dariya kawai yakan masu yabasu amsar cewa shi yabar su ke nan har abada
Bazai kara dawowa cikin banyar bata ba saidai ya mutu a hakan,
Girman da yaran shi suka farayi ne yadan rage mai wahalar don suna zuwa yin dako a bakin kasuwa sukawo dan abin da suka samu ayini asarrafa,
Ko shi Ibrahim saida bukin KB da akayi ne yasan cewa suna da alaka da Joseph,,
Lokacin da yaga irin yadda Joseph ke yi agurin yazo yana fadawa mahaifinshi cewa baisan cewa IBO bane saida yaji yana yare acikin waya,
Abdulsamad yai dariya inda yakewa diyan shi bayanin ko ya suke da Joseph,
Nan ne ibrahim yace zai je gurin shi ya ziyar ce shi yagani ko za,a samu wani cigaba anan,
Maihaifin na Ibrahim baiki ba don yasan kowaye Joseph zai iya taimama wa ibrahim din,
Sai ko gsshi cikin ikon Allah ibrahim din yazo cikin kamata alheri don bai taba zaton cewa yaron zai can za cikin dan lokaci guda haka ba,
Ga sakon kudi har dubu hamsin anbashi yakawo wa mahaifin shi tare da tsaraba,
Kwanan shi biyu da zuwa inda yakoma shedawa Anty Dije zai koma,
Sako tabayar akai ma Joseph din wani robber da akai sild din shi
Sai kuma kilishi cikin envelop, mai yawa cikin wani babban leda tace Ibrahim yakai wa Joseph,
Chapter 45 · 0% Book details