← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 171

Sashe 137

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kwance take saman gadon ta tana barci amma sai juye juye takiyi daga kwancen, da take din,
Gudu take tayi a,wani bakin daji mai duhu da kuma, sarkekiya,
Rigar barcin dake saye a jikinta shine saye gareta a cikin mafarki,
Gudu kawai takeyi sai wasu halittan da bata taba ganin irin su ba ke bin ta a guje,
Hakin da takeyi agudun shine ya baiyyana afili tana ta juye juye,
Tana gudun tana cire wanan yagwagen dake sarke mata hanya da jikin ta,
Bakin wani rami suka kawo ta inda taja ta tsaya guri guda,
Gani cewa wa, yanan halittun sunyo kanta gadan gadan yasa maryam din kara hannayen ta biyu ta rufe jikin ta zuwa fuskan ta,
Tare da furta Innalillahi cikin wani irin murya mai karfi,
Wanda har mueyan yakai dakin da Anty dije take tare da dan ta Abubakar da maigidan ta, da yazo kwana biyu da suka shige,
Wanan sautin da Anty Dije da maigidan tasuka ji na maryam shi yasa su taso cikin sauri zuwa dakin da maryam din take kwance,
Jikin ta ya jike kamar wace akaiwa yayafin ruwa akai,
Jin karan bude kofan su anty yai daidai da saukowan ta saman gado da karfi ,
Inda tayo kan Anty nata cikin kaduwa tana kokarin shigewa jikin ta a tsorace,
Hakalin Anty Dije ya tashi matuka saboda irin halin da, ta ga kaunar nata a ciki,
Don haka sai ta rugumay maryam din a jikin ta inda take ta maida numfashi guda guda a tsorace,
Dakin suka fito da ita zuwa falo inda sukabar mijin na Anty yana yan dube dube a dakin kamar wanda ke bidan wani abu, a dakin,
Kusan a nan suka karasa kwana falon inda har da yaran suka kwaso zuwa falon,
Dakyat suka ga safiya da maryam din saboda irin halin firgicin da ta shiga ciki a lokacin,
Tun a massalaci gurin sallah Asubah mijin Anty ya shedawa baba abinda yafaru da maryam din a daren jiya,
Gida baba ya koma ya gyara shiryawa ta re da zuwa gurin, wani aminin shi malami ne,
Malam na, Ngaski, inda yai yan abubuwan su na malamai,
Daga karshe ya danyi rubutu yasa a cikin wani leda yace abata tasha zata samu barci,
Hakan akayi kuwa don dai maryam din ta samu barci sosai har da kuma zafin da jikin ta yayi duk ya rage,
Sai zuwa kusan la,asar tasamu tadan mike, ruwa ta watso a jikin don takara jin karfin jikin ta,
Bayan ta dawo tasamu anty ta hada mata abincin ta ,
Saida tai sallah sanan ta samu guri ta zauna tafara dan tsankwaran abincin a hankali,
Mafarkin da tayi ne yafado mata a rai irin yadda tai ta gudu acikin wanan bakin daji,
Siffofin wa yan nan miyagun namun dajin da tagani su yo kanta yasa ta saurin zabura da karfi tankar a lokacin ne abin ke faruwa,
Anty ce cikin fadar Wa,iyazu Billah, maryam ki dinga karanto addu,a a bakin ki pls,
Hakan yai daidai da shigowan baba gidan wanda yake dauke da wani bakin leda a hannun shi,
Anan ne yadan murmusa yace Allahu Akbar watau duniya abin tsoro ne Dije,
May Maryam ta tarewa mutun da har zai sata gaba haka yarinyar da naga bama fita takeyi ba,
Karbi wanan maza bata tashanye kuli guda gaba daya yanzu ta, shafa sauran ajikin ta,
Dayan kuma da dare idan zaku kwanta sai ki bata Allah ya kyauta,
Duk sukace amin alokaci guda tare da karban kullin suna budewa
Mahaifin nasu ya dan kalli yar tashi wace take hankali a tashe duk ta wani ramaywa a lokaci guda,
Yadan gyada kan shi alamar takai ci acikin zuviyar shi fam,
Addu,oin tsari ne ya kara nanata mata idan zata kwanta tare da cewa insha Allah zata daina ganin abinda take gani, kuma Allah zai kare ta daga duk wani maisheri,
Daga haka ya mike zuwa yai madu sai da safe,

Yusuf wanda yake masaukin shi zaune ga abincin da aka kawo mai ya sa agaban shi amma yakasa cin komai,
Tunane duk ya addabi zuciyar shi kamar yai ihu ko zai samu relief a lokacin,
Sakon da Sonny ya kara turo maine akan zancen yana son musulunta am.a sai idan Yusuf zai bar mai maryam a matsayin gift din shi na shiga musulunci,
Wani irin nisawa yayi tare da runtse idon shi da suka kada mai sukayi jajir alokacin,
Kara bude su yayi inda ya kurawa labulen dakin ido kamar mai son gano wani abu a cikin dakin,
A gaskiya yana son musuluntar Sonny do min wani babban jahadi ne a gare shi,
To kuma ya zaiyi da dakon son maryam da yakeji tun tana yar ficiciyar ta,,
Wanda sai a yanzu ne ya gane cewa So ne yake mata shi yasa yake kin duk wani al,amari na,ta a wancan lokacin,,
Idon shi yadago ya bude inda yaci gaba da nazarin shi akan abinda ke damun shi,
Ya san halin Sonny sosai yana daga cikkin ire iren mutane yan son rayuwa wa yanda sam sukan manta da akwai mutuwa,
Gashi kuma matashi ajin farko masu fada aji a kowani, kasa,
Duk inda suka kyalla ido suka ga mace har sukaji suna son ta tofa sai sun lasa suke iya kyale ta,
Wani irin kishi ne mai karfi ya tukako zuciyar Yusuf saboda tuna kowa ye Sonny din da yayi,
Maryam din ce ta bashi tausayi a yadda yake ganin cewa duk laifin shine da ya kawo shi inda take,
Inda zuciyae shi tai dan sayi shine tunawa da yayi da kowace ce maryam din,
Shi kadai ya murmusa don sanin kowace maryam din dayayi da sanin halaiyanta,
Maryam yarinya ce da tasan ciwon kanta, wace abin duniya bai taba tsone mata ido,
Ga tada kau da kai ga abin mutum don shi duk iya sanin da yai mata bata taba cewa tana son wani abu agurin shi ba,
Ire iren wanan tunanen yai tayi kala kala inda daga karshe ya yanke shawaran, abinda ya dace yayi akai,
Jiki ba kwari haka ya mike daga gurin da yake zaune saboda shawaran da ya ke ganin itace kawai mashi mafita,
Ya hana shi sukuni a zuciyar shi don haka wanka ya fada ko da zai ji sanyi a zuciyar shi,
Ga abinci a gaban shi amma sam yakasa koda spoon guda, ne saboda irin yadda yake ji, a zuciyar shi,
Dan tsohon da ya taimakane ya fado mai a rai saboda yana da bukatan yayi ko ya jikin nashi
Kira na biyu aka daga wayan da sallama bayan ya karba ne,
Yagabatar da kan shi a gare su nan da nan suka sheda shi,.
Godiya suke mai shikuma yana kokarin tambayar su lafiyan tsohon su,
Nan dai yai masu alkawarin cewa zai dawo ya ziyarce su zuwa gobe idan ya rarage abinda yakeyi,

Maryam tana zaune duk tunanen rashin jin muryan Yusuf kwana biyu da batayi yana daga cikin abinda ke dan damun ta,
Bata san may yasa ba yanzu take yawan jin shi a jikin ta fiye da tsan manin ta,
Muryan Anty Dije ce taji a kan ya tana tambayar ta Maryam lafiya dai ko ?
Bakomai tace wa yar nata,
Bakomai nagan ki haka a zaune cikin damuwa maryam,?
Yar mursmuhin mai kama da yake ta sake kawai,
Kodai Yusuf kike tunane tunda naga jikin ki dai kin ji sauki yau,
Mamaki ya cika maryam din don jin abinda yar nata tafadi,
Kai tagirgiza tace haba dai Anty may zan yi tunane gare shi,
Anty dije wace bawai ta yarda bane tace bam san may yasa wayoyin shi suke a rufe ba,
Duk layin shi nakira akashe suke tun jiya da safe,
Don haka nima ina tunanen ko lafiya yake amma barin kira Jibrin muji,
Jibrin din ne ke sheda ma su cewa yatafi kano gurin wani meeting ne amna zuwa gobe zai dawo Insha Allah,,
Sai alokacin maryam tai dan ajiyan zuciya har yar nata taji,
Amma sai bata ce mata komai ba wucewa kawai tayi zuwa cikin gida abin ta,
Gurin da take zaune tadan kai kwance anan barci ya dan kwashe ta, batare da tasani ba,
Anty Dije wace ke kitchen tana tuka tuwo muryan maryam dake barci a falon ya katse ta daga tukin tuwon da takeyi,
Wani irin kakakari da shure, shure takeyi kamar wace ake zarewa rayuwar ta,
Sosai Anty Dije ta razana saboda ganin yanayin maryam din, a lokacim,,,

ZEEE MAKAWA YELW@
[4/28, 5:40 PM] ‪+234 902 951 1701‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
8⃣2⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI

Ina rokon Allah ya nuna mu na, wanan Watan mai Albarka da Darajja, Ni,ima Gafara da Rahama,
Ya Allah ka sa damu da Albarkokinan na shi, lafiya RAMADAN KAREEM👏👏👏👏👏
AMEEN YA ALLAH👏👏👏👏👏👏👏👏👏
Chapter 137 · 0% Book details