← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 171

Sashe 22

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Aisha tayi farin ciki sosai da jin cewa Joseph yana gari don tun cikin dare ya kirata yake sheda mata cewa ya shigo,
Tasan cewa ita kan kakanta ta yanke saka kenan don ba karamin abu take samu gurin shi ba,
Duk dai iyakar ta dashi kawai yan wasan ni kuma ba wani mai yawa ba,
Sosai ta shirya ma wanan zuwan nashi saboxa gana da yan bukatoci akan shi da yawa,
Shiko tunda safe ya fita zuwa wani kauye shida KB don yana gari,
Basu dawo ba sai zuwa dare marance,su ka , iso, garin ,
Bayan yai wanka ya shirya zuwa ganin little friend din shi,
Wanda kusan ko yaushe yana tuna yaron haka kawai son Assalam ya shiga zuciyar shi,,
Tsaraba sosai yakawo ma Anty Dije da yaranta don gaskya saida Anty ta kasa yin godiya,
Ita kanta Anty wasu materials madu kyau da tsada yasako mata ciki tare da dogayen riguna,
Issalam tana gama ganin kayan tace ina na little mummy din mu,
Da sauri Anty Dije tace mata ai nawa tare da natane zamu raba,
Wani inji Maryam dake kokarin bude fridge a lokacin don ta debo kayan miya,
Kai ta girgi,za wa Anty tace a nutse na yafe nikan gaskiya ban so,,
Issalam tazo har inda take gaban fridge tace kina so mana little mummy bake ki,kace mama tasaya maki anko ba,
Hannun yariyar maryam ta hado guri guda tace Issalam nagode ban so nace maki
Anty ce tace ke kyale zata karba ai wasa take yi,
Cikin mamakin maganar anty dije ta dago kai kalle ta, da niyar magana,sai kuma ta shiru kawai don irin kallon ki shiga taitayin ki da anty tai mata,a lokacin,
Assalam ne yace mama don ba,a sayo mata nata bane wai bata so ko,???
Nace maku bana so kawai simply ta fadi a nutse daidai lokacin da take kojarin barin gurin,
A hankali yabita da kallon mamaki saboda sai yanzu yafara fanin tsana karara a cikin idon wanan yarinyar,
Ya rasa dalilin wanan tsanar da yar karamar yarinyar ke mashi haka,?
Bayan tafiyan shi Anty taima Maryam fada sosai har takai maryam din yin kuka don dai ita gaskiya bata ra,ayin wanan mu,amular da su anty keyi da wanan Arnen sam,
Washe gari maryam na tsakar gida zaune da farantin shinkafa akan cinyar ta, tana gyaranwa tana raira kira,ar ta, ahankali,
Joseph yai sallama suka shigo tare da Aisha
Wacce tai kwalliya cikin wasu irin haddadun buje da riga masu kyau,
Kallo guda tai masu ta kau da kai gefe guda don bata son kara daga kai,
A hankali tace masu bata nan amma tace indan kazo ga abinci a falo,
Daga haka bata kara wani zance ba sai kokarin ci gaba da aikin gabanta tayi kawai,
Aisha ce cikin magana kamar rada tace wanan yarinyar na lura bata da kirki wallahi,
Ji yadda takewa mutane magana wani iri kamar tana jin warin su,
Baice mata komai ba asali ma kamar bai jita ba,
KB ne yai sallama sosai irin ta musulunci duk da bawai ta sake mai fuska bane amma dai ta karba mai cikin girmamawa da nuna kula,
Daga inda take tanajin suna hira akan wani guy wanda cikin su yake saidai yanzu mahaifin shi bai bari yana binsu sosai,
Wai yana zuwa aikin a gonar mahaifin shi ko yaushe ,
Joseph ne ke cewa gaskiya Umar na ban tausayi don ranan da na ganshi bazaka ce yataba rike biro ba arayuwan shi,,
KB yace Umar din ai yace zai zo zuwa anjima don yana son ku hadu dashi,

Cikin dan lokaci jibrin yai suna a cikin gari wurin yan kasuwa da sauran manyan mutane,
Don jibrin mutum ne wanda ya iya business so sai da jama,a,
Ga kuma tausayi da sanin ya kamata, akan harkokin shi,
Musan man dayake yana kara samun taimako daga gurin ubangidan nashi a asarice,
Ta yadda mutane bazasu iyagane cewa business din shi bane,
Saidai su dauka na company ne kawai,
Joseph ya koma gurin wanan matar abokiyar mahaifiyar shi mai manja,
Inda yake sa ana kawo mata kayan masarufi tana sayar wa talkawa cikin sauki,da rahusa,
Ta yadda tallaka ba zai yi mugun wahala ba, sosai wurin samun abinci,
Tuni sunan su ya fara fice ga al,umma tun mutane suna zargin su har aka gane cewa business ne sukeyi tsantsar ta don ci gaban mutane,
Matasa da dama sun samu abin yi yanzu wanda hakan yasa emirate taji dadin zaman Joseph a tare da al,uman su,
Wani abin sha,awa kuma shine idan ya samu labarin cewa a unguwa suna samun matsalar ruwa ko wuta sai yasa sai yasa a tona masu famfon burtsatse ko kuma ya sauke masu transformer,
Ya sayo motoncin noma birjit ya tura kauyo ka mafi kusa don tallafawa,
Dalilin da mutane suka sa mai furen juji ke nan,don dai yanzu yan kwamintin su na chu sunkirashi mitin yafi a kirga amma yaki halarta,,

ZEEEE MAKAWA,,,,
[2/20, 9:21 PM] ‪+234 806 595 8685‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
1⃣5⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
Chapter 22 · 0% Book details