← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 163 OF 171

Sashe 163

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Duk yadda yake son kasan cewa da Maryam din kamar da yanzu bai samun haka,
Tun yana daurewa har yakai yau bayan yadan shawo kanta ne komai ya kammala,
Sai kawai yaga har barci ya kwashe ta ko yanzu sam bata son bashi hadin kai kamar farko,
Saman dining table suke kowa na kokarin karyawa amma banda maryam wace tasa ruwan tea din ta gaba tana kallo
Yusuf ne da kanshi ya matsa mata har tadan sha rabi,
Abuguda ke damun maryam yanzu kamar yadda su Ruth da Grandma ke damun su da waka tun da asuba ko tana son yin addu,oi basu bari saboda ihu da kuma suraitan su,
Yau ma kamar kullun bata samu barcin dare da dadi ba takai wani lokaci a kwance, saboda masu wakan church dake tashi cikin dare suyi tayi,
Wanka maryam din tafito tana zaune gaban mirrow Yusuf yashigo dakin yana kokarin daura cliffs a hannun rigan shi,
Tun daga nesa tace mai ina kwana uncle ya ki ki beauty, nashigo na samay ki kina ta barci ai,
Murmushi maryam tayi tace yanzu sai da safe nake dan samun barcin don hayaniyan nan na dare bai bari inyi barci,
Baiyi magana ba sai ido da yadan tsura mata tausayi tabashi acikin rashi don yasan cewa dama hakkuri takeyi kawai,
Don irin yadda suke yi da wata ce yasan da yanzu an kwashi yan kallon dan abin nasu harda gaiyya aciki,
Sallama yai mata yace zai dan shiga gari don ba aiki a ranan,
Bayan fitan shi tadan sha fruit don shi abincin ta ita saboda ko da bata damu da abinci ba ita,
Saida taga tadan kara kwantawa don ji tayi still barcin bai isheta ba ,
Anty ce tafado mata arai don shi baba yace ya yafe mata tadaina kiranshi idan yaso shida kanshi zaiwa mijin ta magana abata waya,
Anty ta,dauki wayan cikin wani murya wanda maryam din bawai tasan ta dashi bane,
Gaisawa sukayi sama sama batare da tasakewa maryam din ba,
Sai maryam dince ke cewa abata su Assalam su gaisa,
Bayan sun gama wayan ne sai tunanen yadda yanzu yarta ke mata yadamay ta,
Daga gurin ta koma barci abin ta har akai sallah azuhur maryam bata farka ba,
Yusuf yadawo daga massalaci yaganta a kwance shi da kanshi yata da ita,
Ido ya tsura mata kamar mai son ya gane wani abu acikin ta,
Maryam ya kira sunan ta inda ita Maryam din ta ansa mai a hankali,
YUSUF yace wai mai ke samun kine haka naga duk yanzu kin koma wata iri jiki babu kwari,
Sai barci all the time, may yasa hakane wai, ?
Maryam tadan langabe kan ta tace nima ban sani ba uncle haka kawai nake jin ba dadi ko da yaushe,
Gaskiya anjima zakai ki kiga likita don yadiba min ke ko baki da lafiya ne,
Tana kokarin mikewa,zaune ne tace to aini lafiya na kalau uncle,
Gaskiya ban yarda ba inji uncle yace wa maryam din,
Dole ne aduba minke don duk kwanan nan an hana min, samun wanan ni,imar da aka saba bani
Din yanzu kusan manaji kawai nakeyi ban samu ina kashe kishin sha,awata kamar da,,
Kunya ya kama maryam din wace ta boye fuskan ta cikin filin dake kusa da ita,
Kwana biyu maryam taki yarda,su je gurin likata ta dage wai ita lafiyan ta kalau gajiyan tafiyan jirgine ke tambayar ta,
Shiko Yusuf ya kasa barin ta ta huta kullun sai kokarin diban rabon shi yake yi gare ta,
Hakan yasa jikita yai weak sosai har saida takai kwance,
Bashiri dole suka tafi asibiti don adibata, saboda yadda take jin jikin ta,
Awon farko likita yagane cewa cikine a jikin maryam na wata uku,
Gashi kuma saboda rashin samun hutu har cikin shima yana son samun problem,
Yusuf tun agaban doctor ya rungumay maryam cikin hamdala ga ubangijin shi

Mutum na farko da Yusuf din ya fara kira itace Ànty Dije tanuwa Yusuf din farincikin ta sosai a fili,
Amma sai dai abinda ya kula dashi bata tambayi lafiyan maryam din ba,
Amma kuma sai bai dauki zancen da muhinmanci ba,
Ita ko maryam safiya ce takira ta sheda mata duk yadda,sukayi da likita da bed rest din da aka bata,
Anan sadiya tai wa maryam alkawarin zuwa ta diba ta,
Saboda sanin irin mutanen da maryam din kezaune da su,
Mahaifiyan safiya bata da matsala indai har al,amari na maryam ne,
Aikuwa washe gari safiya tafara shirin tafiya,Abuja inda tayowa maryam din tsaraban kanyan miyan hausawa na gargajiya,
Motar farko tabiyo zuwa Abuja din inda suka iso musalin karfe biyun rana,
Maryam taji dadin wanan ziyaran da aminiyar ta takawo mata,
Ita ko safiya sai kallon mamaki takewa kawar ta ga kuma irin daulan da Allah yaba ta,
Gaskiya Allah miskaraziratin ne, ga bayin shi,
Kamar ba maryam wace ke ta aikin wahala agidan yar uwar taba,
Gashi duk wahalan nan da tasha don Allah yaba maryam din gurin zama mai kyau gashi kuma Anty tafara kushewa,
Yusuf yadawo daga gurin aikin yasa mu maryam tare da,abokiyar ta,suna hiran su gwanin sha,awa,
Nan ya zauna tare dasu ya gaisa da Safiya din, inda yake tambayan ta labarin mutanen kwantagora,
Yaso ya tambaye ta zancen Jibrin amma sai fasa saboda ko shi bai son ya tuna da maganar ,
Maryam daga inda take kwace suka hada ido da Yusuf yai mata,wani irin kashe ido
Wanda ita kadaice tasan ma,anan wanan kashe idon ,
Kafadar ta tadaga mai alamar a,a yakara dan langabe kai maryam tai mai da nuni da Safiya wace tabada baya tana kallon TV,
Ya juya yana fara tafiya jiki ba kwari yadan juyo yana cewa ai na manta gobe zamu yi baki daga Niger state,,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA

🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
9⃣7⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI

YA ALLLAH KA KARAWA ANNABI DARAJJA KA KARAWA MUSULUNCI DARAJA 👏👏👏👏
Chapter 163 · 0% Book details