← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 171

Sashe 14

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yau kwansn iliyasu biyu da dawo wagarin don kusan sati guda yake yi idan ya zo garin,
Zaune suke suna hira shida Anty Dije bayan fitan wasu mata yan uwan shi da suka shigo
Wani almajiri ne yai, sallama a kofar gida ya ce ana kiran Assalam wai a waje ,
Daga Anty Dije har mai gidan ta, saida suka kara tambaya cikin mamaki,
Maryan wace ke kitchen tana kokarin gyara kitchen din
Zuwa tayi tadan leka don taga kowaye ya aiko kiran Assalam haka,
Tsaye suke jingine da wata mota mai kamar ruwan kakin soja,
Dan lekawa,tayi kadan daidai yadda basu ganinta tadawo cikin sauri ,
A,kofar shiga falo ta hadu da ya iliyasu, da ke kokarin fita waje don yadiba,
Duk kan su maryam suke kallo don jin ko waye a wajen,
Inda Anty Dije take tsaye ta nufa tace cikin murya kasakasa wanan mutumin ne fa wanda Assalam yake lakewa,
Iliyasu da ke tsaye ke tambayar maryam waye ne a wajen wai,
Murya cikin taushi anty Dije tace wanan abokin jibrin din gidan baba bala dana fadama,
Kasancewa duk wani abu mai muhinmanci sai anty ta fadawa mijn ta don gudun zargi,
Dan shiru yayi can kuma sai yakama hanyar wajen
Basufi minti koda uku ba sai gasu sun shigo cikin gidan duk kan su,
Shi maigidan shi ne gaba, sai su biyu a bayan shi,,
Ya iliyasu nacewa jibrin nadauka ma ko wani bako ne da naga ka tsaya a waje kana cewa wai akira ma Assalam,
Bayan sun zauna a falo ne suka dan taba hira a tsakanin su inda aka gabatar masu da abinci,
Duk da Joseph baiso cin abincin ba am a saida ya illiyasu yasa shi ci
Sannu sanu daga hiran su yafara sake jiki har zuwa lojacin da Assalam suka dawo daga gidan kakan nin su,
Dagudu Assalam ya fada jikin Joseph yana murna,
Batare da yai magana da kowa ba ya mike tsam rike da hannun Assalam zuwa gurin motar shi waje,
Sai a lokacin Ya Illiyasu yake tambayan jibrin ko waye Joseph din,
Nai yai mai kwatance da mahaifin shi da kuma mahaifiyar, shi,
Saidai bai fada mai ko waye Joseph din ba ayanzu
Yadai bashi labarin haduwar su da Assalam har yadda jinin su ya hadu,
Lokaci guda don yace ma ya illiyasu kusan ko yaushe su kayi waya sai yatambaye shi labarin sturbonboy,
Abinda da da mahaifi, duk mai son mutun akace yaso dan shi,
Hakan yasa ya illisu jin dadi har a cikin zuciyar shi,
Ganin su mukayi Assalam da kaya nike nike sun shigo harda keken yara,
Gaba daya muma fito waje muna kallon wanan irin shakuwar
Bayan sun aje kayan ne yaya yagaiyace su cin abin cin dare a gidan shi,
Joseph din yaso ya doje yaki zuwa saboda yana son ya shiga evening services yau,
Amma ba yadda ya iya kawai sai ya amsa gaiyatar yaya din,
Saidai su uku suka zo tare da KB akazo wanan karon,
Abincin hausawa mukayi yau tuwon shinkafa fara da miyar Alaihu da yakuwa, sai yar kabewa da mukasa da busashen kifi,
Mundauka cewa baza suci abincin ba sai gadhi duk an cinye sai kwano kawai,
Duk kan su sunyi mamakin ganin anyi girkin mutanen da a gidan matashi kamar ya iliyasu,
Saboda sanin da sukayi yanzu kiuyya bai bari mata suyi girki mai kama ciki, da dare,
Saidai kawai aima namiji taliya ko indomie da dare ko dafa duka,
Saboda kiuyyuya kawai, don kada a motsa jiki,
Hira sosai sukeyi yan sungama cin abincin kamar sun dade da sabawa da junar su,
Shiko Assalam yana manne a jikin Joseph har yai barci,zuwan wanan lokacin,
Ganin haka ya iliyasu yaba Joseph bakin cewa duk lokacin da yazo kuma yana son ganin Assalam yashigo kawai gurin anty Dije,
Kuma miyar da yace yana so na hausawa yadinga fada mata ai mai, irin da yake so,
Wanan shine silar kara shakuwar yan gidan su Anty Dije da Joseph,

ZEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
1⃣0⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,

Zaune suke a majalisar su,inda suke hira duk marance ( yamma ) akantitin B C G titin da ya mike zuwa kaduna , minna Abuja tare da,wasu yan kauyu kar dake hanyar,
Duk marance a nan su KB ke yada zangon su, suyi ta hira ko aita shan matar juna a tsakanin su,
Wanan abin ko yaushe yana kara burge Joseph don saman yan yaren su basu da lokacin hakan ,
Ko yaushe ana cikin kasu ko bakin titi gurin bidan kudi,
Yan zun kuma sai dai in har yaso shiga taro saidai ya yaje koda clubs ko kuma wani park ire iren wuraren sheke aya amma ba irin haka ba da hausawa ke yi,
Shiyasa shi har gobe yana sha,awar tarbiyan bahaushe,
Joseph jin shi yakeyi kamar bai da wani harkan komai a gaban shi,
Zuciyar shi na mashi fes a duk lokacin da yake cikin irin wanan yanayin,
Wani matashi mai suna sulaiman ne yazo sama wata mashin rober,rober yanata,washe baki,
Ya sayo sabuwar abin hawa, sai sam barka kowa ke mai a lokacin saboda ya huta da yawo a kasa ko saman kabukabu,
Kowa sai zuwa yakeyi yana duban man shin din cikin kulawa, da yiwa Suleiman fatan alheri,
Joseph dake waya a lokacin kuma yana kallon su sai abin ya daure mai kai so sai
Don saboda mashin kawai da ko gabadayan su zai iya sai masu wanda ma yafi wanan tsada suke ta ma suleiman murna haka,
Sai kawai yaji tausayin su yakara kamashi duk da sunan wai suna aiki gwaunati ke nan amma gashi yar mashin kawai na basu sha,awa,
Jesus crisis yace a zuciyar shi don ba karamin sa,a ya taka ba shi da Allah ya maishe shi haka cikin su,
Don ai a da duk tare suka taso kuma yan zun ne yasamu wanan ci gabar duk da dai basu san ko shi waye ba to amma dai sun san yana da shi,
Muryan Nasir ce tadawo da shi inda yaji Nasir na fadin cewa
Allah yasa ko yar Suzuki yasamu ya saye shima, hakadai duk sukayi ta hira a tsakanin su inda kowa ke fadin albarkacin bakin shi,
Har zuwa goma na dare suka kai agurin suna hira sannan KB yadauke shi sama wata rubaban mashin din shi zuwa gida,
Tun da safe yabar gari ya ko gurin harkokin shi don ci gaban shi,,
Tunda yadawo yadawo da kudin tallafawa mutane da dama aran shi,
Din shi a ganin shi duk wanda kuka wahala tare har Allah yabaka samu daga cikin ku to bai kamata ka manta da yan uwa ba,
Sanar,ar da suka fara shigo da dan yar Gas dama ainihin pure Gas din,
Gani harkan ta karbu yasa shi yin kokarin gani sun gyara system din business din yadda ya kamata,

Shigowa da mai din kasar arewa yasa shi kawo KB daga cikin wa yanda za,aiwa interview din zama members nan gaba,
Waya yai ma KB yace su hadu Abuja next week Wednesday, don su dan tatauna, akai,
KB duk da bai sam komaiba bai yi kasa a gwaiwa ba ya shirya zuwa Abuja din, don ansa kiran da joe ya mashi,,
Cikin lokaci ya samu isa Abuja inda yasamu, har Joseph ya cika mai duk wani form da ya kamata,.
Briefly Joseph yai mai bayani sai gashi kawai, ankira shi don yashi ga ciki duk da bawasu tambayoyi bane masu tsauri amma dai Joseph din yana darrr kada kb ya kasa amsawa duk da baida shakku akan shi, don yasan cewa yana da kokari,,
A cikin ikon Allah KB yai nasaran lashe interview din ,,,a cikin masu yi harda Joseph a cikin su,
Murna da farin ciki a gurin su baa musalintawa, duk da har yanzu bawai KB ya gamsu da kowace irin aiki bane,
Amma dai gani masu taron ya tabbatar mai da ba karamin aiki bane,,
Wanan abin ya jawo ma Joseph surutu acin abokan harkan shi,
Don sai cewa suke yi ya dauk hausa ya sa acikin harkan shi ya bar yan uwan su sun fadi,
Wanan damar a cikin sune ya kamata wani ya samu ba,a cikin northern side ba,
Suko hausawan dake cikin su sun yi mamaki kwarai daganin Joseph ya kawao candidate din shi bahaushe,
Tun a wurin akaba KB sabuwar mota da kuma gida inda zai dinga besing a Abuja
Sai sabuwar office da aka bude masu washegari,
Kabiru gani al,amarin yakeyi kamar a mafarki wai yau shine da wanan abin da bai taba tunane samu ba,
Sai gashi Allah ya bashi cikin dan lokaci guda, don haka bakaramin nasiha Joseph yai mai ba don ya fada mai cewa sai yasa ido ga harkan so sai kuma ya rike gaskiya don akwai bata gari wa yanda zasu iya batasgi cikin dan lokaci,
Don zasu iya hada mai tracks kalakala don kawai ama wani hanya,shi a kore shi,
Chapter 14 · 0% Book details