← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 171

Sashe 15

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kwantagora ta dauki zance kwaaaaa cewa KB yadawo da sabuwar mota, ya samu aiki,
Amma ba,a san kowace irin aiki bane haka da har ya samu wanan cigaban cikin lokaci guda,
Wasu suka fara cewa ai yafara irin harkan Joe ne Joe din ya jefa shu cikin kungiya,
Wanan zancen har ya fada a kunen KB da yan uwan shi,
Inda mahaifin shi yakira yin mitin tare da duk wani dan uwanshi tare dashi KB din,,,,
Anan KB ya fada masu cewa wallahi har ka ce ta sanar man Gas wanda duk wani Gas da zai shigo nan arewa saida sa hannun su a ciki,
Nan dai yai masu bayani har suka fahinta suka kuma yi mashi fatan alheri a harkan,,,
Saodai cikin gari kan wasu sun yarda wasu ko ba su yarda ba har yanzu,,,
Sadiya Mohammad jodi wata sabuwar matashiya ce mai tashen budurci a cikin gari
Tun ranan da taga Joseph tare da su Aisha Allah yasa mata son shi a rai saidai kawai matsalar ta da akace mata ba musullumi bane shi,
Don har ta kasa boyewa a zuciyar ta saida ta samu jibrin tai mai magana akai,
Dayake akwai wasa a tsakanin su yasa Jibrin duk inda ya ganta sai yace mata ta Joseph ita kuma sai tace aa, saidai Yusuf,
Wanan wasa ko yaushe jibrin kewa sadiya, indan sun hadu ita ko bata gajiya da bashi ansa kamar kullun,
Maryam ce zaune tana wanki a bakin famfo gidan su.
Wayan Anty Dije yai kara alamar kira ya shigo mata, a lokacin
Maryam tamike cikin tafiyar ta maikama da rangwada kasan cewa ba wani jiki gareta ba,
Daukar wayan tayi don ganin bakon noba ke kira, cikin yar siririyar murya tace Assalamu Alaikum,
Hello Anty kuna lafiya ya yara da gida,
Wayan ta dan daga ta kalla,sai kuma ta kara manna wayar a kunen ta,
Wake magana ne tace ?
Anty Hadiza nake nema pls aka bada ansa,
Bata nan ta,shiga makwabta yanzu, dan shiru yayi sai kuma yace Assalam na kusa pls,?
Baya nan shima tare suka tafi, ok in tazo ki fada mata Joseph ya bugo mata,
Joseph kuma ? Joseph fa, kai is wrong noba pls
Kada ka kara bugowa nobar matar aure ce pls
Dan murshi yayi har tana iya jin shi, alokacin yace ba nobar maman Assalam bane?
Tsuki tayi tana fadin mukan ina muke da wani arne wai Joseph da zai kira Anty
Daidai lokacin da ta gama fadi ta kashe layin,
Tana ta faman fada wai kawai don suyi magana da matan mutane suke kiran wrong noba,,,
Shiko joseph dake zaune a saman wani leda cushion ya rike wuyan shi da hannu bibiyu ya furzar da iska, daga bakin shi,
In akwai abinda yafi mai munin ji shine ace mai arne, ko kafiri,,,,
Tun yana yaro yai hating din wana kalman a rayuwan shi,
Don in mutane suka ga su jibrin ko kabiru tarrme dashi lokacin sai yaji sun ce baku barin yawo tare da dan kafirai ko ko dan arna ko,
Wani bukin Christmas daya kawo masu abinci kamar yadda su ma suke bashi abinci sai cewa wasu mata sukayi
Ku fita mu na da abincin kafirai a cikin gida kada muyi amai
Wa zai ci abincin arna jagwagwalen banza kawai babu ko tsarki,
Shikuma yadai san cewa duk wani tsabta a lokacin mamanshi tanayi,
Kuma shi har gobe idan ya kewaya yana tsarki kamar yadda ya ga kowa nayi,
Amma sai ake ce mai wai baida tsarki haba mutane ne,????

Anty Dije tana shigowa tare da su Assalam daga makwabta ko daki bata shiga ba,,,
Maryam ke fada mata cikin fada cewa wani kafiri ya bugo mata waya wai sunan shi Joseph nikan nace wrong noba ne
Dan rainin wayo kawai Anty Dije dake tsaye sororo tana kallon yadda maryam ke ta faman halako fada,
Tace kafirin banza kafirin wofi don ma bakiji hausan shi ba wallahi kamar fa hausan mutum kwarai,
Anty Dije tace maryam ina fatan duk wanan zancen baki fada a waya ba dai ko,
To may ye Anty in ma na fada mai kawai ina aikina kafirin banza ya kirani, ya bata min lokaci,
Saida Anty ta zauna take cewa maryam mutumin nan ne fa abokin Assalam,kike ta surfa ma masifa,
Barin wankin tayi tana kallon Anty Dije tace Anty ce min fa maishi yayi sunan shi Joseph fa,
Shine mana Anty takara ce mata da dan karfi wai anty shi kafiri ne dama ba musulumi ba,
Ke baki sani bane dama
Hmmmm lalai mishon bat da musulumi,
Wallahi anty ni na dauka cewa musullumi ne shi duk ganin da nake msi,
Dan guntun kara dake gefe anty tadan duka ta dauko tana cewa wallahi ke dai kamar ace mai musulumi
Don dai gaskiya ya duk halin shi na kwarai ne, wallahi,
Daga inda maryam take tsaye tace furen juji kenan shi,
Ga halin kwarai amma ba alkiblan kwarai,
Dama malamin mu na islamiya ya fada muna ce wa akwai irin wa yan nan mutane acikin yan Ahal,kitab,
Saidai basu da yawa so sai daga cikin su, masu halin rayuwa irin na mumunai
Daga haka ta tabe baki taci gaba da wankinta tana cewa Assalam abokin Christian, shiko sai dariya yake mata don bai san ma,anar maganar ta ba,,,
Yinin ranan sai maganar ta dan tsaya mata a rai kawai tausayi yabata mutum kamar wanan ace baya sallah Allah ya kyauta kawai take cewa aranta
Sai ma daga karshe takama jin haushin shi, da takaicin kawai,,
Mr Emanuel yanzu girma ya fara kama shi don haka yanzu iyakar shi zama gixan man su ya daina yawan harkoki kamar da
Kamar su saida manja, saida robobin aiki irin na mata duk suna da shagunar su acikin garin kwantagora,
Yau ma kamar kullun zaune yake saman wata far kujera kamar kulun da yamma haka yakeyi sai zuwa shidda yake wuce wa church wani lokaci,,
Wani musa mai aski ne yazo inda yake don sun saba da musa,wanzami tun tuni
Saboda zaman uguwa guda, da suka taba yi ada,
Shine sabon su yai karko har zuwa yan zu
Musa yakan dan biyo ya samu dan abin ihisani akai akai
Bayan sun gaisa ne yake kokarin zama gefen da Ema mai manja yake, daidai lokacin yake cewa
Ashe taimakon da yaron ka yayi wa dan gidan Tanimu kafinta ke nan
Mr Ema ya ce taimakon may ke nan fa, acikin hausar su irin ta IBO,,,
A, ba ance ya samo mai babban aiki a Abuja ba har ma yai kudi lokaci guda,
Wani yar Mr Ema yaji kamar an datsa mai mashe a zuciyar shi,
Sai da yai kokarin boye ma musa wanzan da halin da ya shiga tukun sanan yace har ya fara aikin ne ko,
Musa wanzan yace kai tun yaushe aiki kan har mun fara cin moritar ta,
Don nafito zan wuce kauye nagan shi yana magana da wasu masu aikin gina wai yana son ai masu katangar gidan su,,
Wani iri mr Ema yakaraji a ran shi watau ke nan har maishi yadan fara karfi da tai makon Joseph din,
Alhalin ga yaran su cikin gari birjit da suka gama karatu suna ta bin shi yasamo masu aikin yi yana cewa ba aiki yanzu,,,
Musa na ta zuba shi bai ko jin may yake cewa a lokacin,,,
Kai musa pls zan tofi wani anguwa ka tafi kawai zamu hadu gobe ke nan,
Daga haka ya tashi sai gurin motar shi ya nufa rai bace
Gidan shi ya nufa cikin fada yake kwada ma Samuel kira
Ya wurgat da sandar da yake yawan rikawa mai alamar sandar sarauta,
Lokacin Samuel yafito daga cikin gida inda yake daka sakwara,
Call your brother for me pls,
Cikin mamaki Samuel din yace ok Dad,
Kira daya na biyu ya dauka
JOSEPH da kakausar murya yakira shi hakan yasa Joseph din sani wani muhinmin magana ya faru
Don haka yai shirin sauraren baban na shi,,
How may time D I warn you about dis hausa boy's,,, ??
Baba what's going on. Sai kuma yace cikin yaren su maya faru baba,
Ya akayi ka samo ma yan gidan hausawa aiki bayan nayi ma warnings akan MAKu da su,
Sosai yake mai masifa shi dai sauraren shi ya keyi batare da ya ce uffan ba,,
Daga karshe kuma sai ya sasauta muryan shi zuwa lalashi,
Yace You have to be,careful with dis people they are very dengerous,
Haka dai yai ta ma mai nasiha shiko yai shiru kamar mai saurare,
A karshe ya sheda mai cewa yana jin kunya abokan shi da yan churches din su su ji cewa yai eanan aikin,,,,

ZEEEE. MAKAWA. 👏👏
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
1⃣1⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
Chapter 15 · 0% Book details