← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 133

Sashe 99

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha jin muryar Baffa a bayanta sai ta miƙe tana murmushi ta ce, "Ni ce Baffa."

Baffa ya zauna yana kallon ta da fara'a ya ce, "Islaha saukar yaushe?."

Ta zauna aƙasa ta ce, "Tun ɗazu na dawo, ina gidansu Safeera. Ya ƙarfin jiki Baffa?."

"jiki ya warware Islaha, na ji sauƙi kamar ban yi ba."

"Allah ya ƙara lafiya Baffa."

"amin Islaha. Ina kwance sai na nemi ki na rasa, sai da na dawo nake jin labari mara daÉ—i. Me yaasa ki ka biyewa zuciya ki ka bi shanun sarki? Meyasa ki ka amince dar huÉ—ubar waÉ—anda basu cancanci a ji kalaman su ba balle a É—auka?."

Islaha ta san Baffa da Mama yake maganar, sai ta É—an yi murmushi ta ce, "Baffa wani abu ne ya kaini, kuma shine ya dawo dani."

Baffa ya ce, "na ji daÉ—i da ki ka dawo lafiya, daga ganin ki an san ba ki sha wahala ba. Ki shiga ciki ki kwanta."

Mama ta ce, "tunda ni ce shanun sarkin, baza ta shiga ta kwanta ba, ta tafi wani wajan amma ba nan ba."

Baffa ya ce, "a nan zata zauna, in kin ga Islaha ta bar gidan nan to ta yi aure, in kuwa bata yi aure ba bata da wani gida in ba nan ba."

"Bazan ajjiye wacce ta je ta gama wayon duniya a gidana ba. A ina ta samu kuÉ—in da ta biya kuÉ—in da aka kaita harda na dawowa gida da tsaraba?."

"Cewa ki ka yi a gidan ki, kin ga nan ai ba gidan ki bane. Sai ki jira ki gina na ki, daga lokacin sai ki hana duk wanda ki ka dama zama a cikinsa, dan wannan kam ba gidan ki bane."

Baffa ya kalli Islaha ya ce, "Safeera jeki ki rakata É—aki."

A sanyaye suka wuce zuwa ɗakin Islaha suka tarar dashi yana nan yadda yake, sai dai ya yi ƙura sosai.

Safeera ta ce, "ki fita, bara na gyara miki, na ji har kin fara tari."

Islaha ta ce, "Bara na miƙawa Baffa wannan ɗin sai na dawo." Safeera ta fara gyara mata ɗakin ita kuma ta fita da tsarabar Baffa.

Da sallama ta shiga wajan Baffa, ya amsa yana kallon ta da murmushi, ta durƙusa ta ce, "Baffa ga tsarbar da na siyo maka."

Ya klli kayan ya ce, "Tsaraba kuma Islaha! Ke da ki ka je aiki maimakon ki adana kuÉ—in ki sai ki yi tsaraba?."

Ta yi murmushi ta ce, "Babu yawa Baffa."

Baffa ya ce, "Na gode Islaha, Allah ya yi miki albarka."

"Amin Baffa."

"Ki cigaba da haƙuri, kar ki biyewa Maman ku, ki kau da kai ki cigaba da zama jiran lokaci. Tunda kin dawo auren ku bazai wuce sati biyu ba, gwara ta daina ganin ki a huta."

Ta yi murmushi ta ce, "Babu komai Baffa."

Baffa ya ce, "Jeki ki huta."

Ta miƙe a sanyaye, Baffa ya ce, "Ina Labiba da Maimuna?."

Gaban Islaha ya faɗi, ta dawo ta duƙa ta ce, "Duk suna gaishe ka."

Baffa ya murmusa ya ce, "gwara da ki ka yi dawowar ki, ni zuciyata bata amince da zaman nan ba, kuma ban taɓa zargin za ki aikata wani abu mara kyau ba, ko yaushe kyakykyawan fata nake yi miki. Tashi ki je ki huta, Allah ya cigaba da dafa miki."

Islaha ta amsa da amin, sannan ta miƙe ta fita ta koma wajen Mama. Tana shiga falo suka haɗu da Mama, ta bita da kallon sama da ƙasa ta ce, "ya ba ki goyan bayan zama a gidan nan, kina zaune kina zaman jiran Saheer ya aure ki ko?."

Islsha ya sukuyar da kai bata ce lomai ba, Mama ta ce, "indai ni na haifi Saheer wallahi bazai aure ki ba, in kuwa ya zaɓi ya aure ki sai dai ya nemi wata uwar bani ba."

Islaha ta É—aga ido ta kalle ta jin abinda ta ce, Mama ta buÉ—e idanu waje ta ce, "kalle ni da kyau, buÉ—e idonki cikin nawa. Wallahi bazai aure ki ba, in kuwa ki ka ga kin aure shi to ki tabbatar bana numfashi!."

Islaha ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, ta ɗan motsa zata bar wajan Mama ta riƙo ta ta ce, "ki daina ganin yana ba ki goyan baya, ga dai gida nan ki zauna, amma ban da auren ɗana."

A hankali ta bar wajan ta shiga É—aki, ta tarar Safeera ta gyara shi ta zauna akan gado ta yi shiru.

Safeera ta ce, "Ya dai?."

"Kwana biyu na fara mantawa da damuwar Mama, hankalina ya kwanta, kunnena ya daina ji min baƙaƙen maganganu irin na Mama. Daga dawo ta yau na fara fuskantar ƙalubalen da na bari. Ya zan yi da Mama? Me na yi mata bata sona?."

Safeera ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ina jinta, duk abinda ta faÉ—a na ji, amma bata isa ta hana abinda Allah ya nufa ba."

Islaha ta yi shiru bata ce komai, Safeera ta gama yi mata abinda zata yi sannan ta kalle ta ta ce, "zan koma gida, zan bar ki ki sake hutawa. Amma gobe ki tabbatar sai kin ƙarasa bani labari."

Islaha ta kalle ta ta ce, "Gobe za kiraka ni opharnge, ina da buƙatar yin bincike akan inda Zainab ta tafi."

"Allah ya kaimu. Aiki fa?."

"Ba gobe zan koma ba, sai na huta." Safeera ta É—aga kai ta yi mata sallama ta fita.

Ya ku ke ganin rantsuwar Mama? Zata karye ko baza ta karye ba?.....

_Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_

Nana Haleema.
[7/21, 12:05 PM] KRBBK: RDB2P73
Nana haleema.

Washe gari Islaha bata bari sun haÉ—u dasu Mama ba ta bar gidan ko karyawa bata yi ba. Islaha da Safeera suka haÉ—u suka tafi gidan marayu kamar yadda ta ce.

Tun da suka je gate take gaisawa da da ita har ciki gidan. Office É—in Mama suka je, aka ce ta fita bata nan, hakan ya saka Islaha ta tsaya ta rasa abinda zata yi.

Tana na tsaye sai ga É—aya daga cikin ma'aikatan gidan, ganin Islaha a tsaye sai ta ce, "Æ´ata Islaha."

Islaha ta kalli matar, sai ta yi dariya ta ce, "Baba Tabawa, ina kwana."

Baba Tabawa ta ce, "Yaushe ki ka dawo? Ance min da bakya nan."

"Jiya na dawo Baba Tabawa, na zo neman Zainab ne."

Baba Tabawa ta ce, "Zainab dai ta ki?."

"Ita fa, nazo ina neman ta ance bata nan, kuma naga Mama bata nan."

Baba Tabawa ta girgiza kai ta ce, "ai Zainab ta kwana biyu bata nan, an nemi inda take an rasa, har maganar an kai gaban hukuma amma babu ita babu labarinta."

Islaha ta sauke numfashi cikin wani irin yanayi ta ce, "Don Allah Baba Tabawa babu wanda suka yi magana da ita kafin ta bar gidan nan?."

Baba ta girgiza kai ta ce, "gaskiya ba mu yi magana ba, amma...." Sai ta yi shiru, ta kalli Islaha ta ce, "ku zo mu je."

A hankali suke bin bayanta, suna tafiya Islaha tana gaisawa da waÉ—anda suka sani har ta ja su kitchen inda Baba Tabawa take aiki.

Baba tabawa ta ce, "Na jawo ku nan ne saboda akwai saƙon Zainab da ta bawa Yafindo, Yafindo ta faɗa min ta ce ta bata saƙo ta ce mata don Allah duk ranar da ki ka dawo ta ba ki."

Islaha da zumuÉ—i ta ce, "bara na je wajan Yafindon na same, ba Yafindon kitchen É—in nan ba?."

Baba Tabawa ta yi saurin riƙo hannun Islaha ta ce, "Islaha tsaya."

Islaha ta tsaya tana kallon Baba cikin wani irim yanayi. Baba ta ce, "Yafindo bata nan, ta je ƙauyensu."

Islaha ta dafe kai ta ce, "Kuma bata ba ki saƙon ki ajjiye ba?."

"bata bani ba Islaha, ita kanta wannan maganar cewa yi kar na faɗawa kowa, kema kawai na faɗa miki ne. Dan ba mu yi tunanin dawowar ki nan kusa ba, shiyasa itama ta tafi ƙauye."

Islaha ta ce, "Ina ne ƙauyen na su?."

Ta girgiza kai ta ce, "ba a cikin garin nan take ba gabaɗaya." Islaha ta yi ajiyar zuciya mai ƙarfi, ta jingina da bango ta yi shiru bata ce komai ba.

"Amma ta faÉ—a min a yadda Zainab ta bar gidan nan akwai matsala a tare da ita."

Islaha ta girgiza kai ta ce, "Ina Hafsa da Fadwa?."

Ta girgiza kai ta ce, "waɗnanan sun zama ƴan kansu, sai abinda suka ga dama suke yi a gidan nan, kuma da yake sun samu goyan baya babu abinda ake yi musu. Fadwa itace shugaba, duk abinda suke yi a ƙarƙashin Fadwa suke yi."

Islaha ta kalli Baba Tabawa ta ce, "na gode Baba, zan dinga shigowa akai akai, dan na duba ko Yafindon ta dawo."

Ta girgiza kai ta ce, "Duk da dai tana jimawa in ta tafi, amma na san zata dawo nan kusa." Islaha ta gyaa kai suka fita daga gidan.

Suna fitowa Islaha ta ga motar Saleem a ajjiye tana jiransu, Islaha ta kalli Safeera, Safeera ta ce, "Ni ce na kira sa." Bata ce komai ba suka shiga motar.

Suna shiga Salewm ya ce, "Hajiyan Jedda, sai ki ka dawo babu labari ko?."

Ta É—an yi murmushi ta ce, "Dawowar ce ta zo a haka, amma na so na faÉ—a mu ku Allah bai yi ba."

"Ba wani nan, kin tafi kwatsam babu labari, kin dawo babu labari."

Ta É—an yi murmushi dan bata cikin yanayin wasa, suka gaisa ya ce, "ina fatan komai ya zama normal ko?."

Ta É—aga kai ta ce, "Alhamdu lillah!."

"Haka ake so. Ina zamu je?."

Islaha ta ce, "Safeera wajan wankin kai zani, kaina ya dame ni."

Safeera ta ce, "mu je sai ayi mana."

Tunda suka fara tafiya bata ce komai ba, ta yi shiru tana tunanin halin da ta jefa Zainab a ciki. Safeera ce ta waiwayo ta kalle ta ta ce, "Yanzu ya ki ke ganin za a yi?."
Chapter 99 · 0% Book details