← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 133

Sashe 44

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana fitowa yarinyar cikinsu ta zubar da lemo a kan tiles har kan carpet. Aka ɗauko abinda gyara waje aka bawa Umma ta goge tiles ɗin, aka bata ƙramin towel alamun ta goge wajan ta duƙa tana gogewa.

Tana gamawa aka nuna mata wata yarinya, ita dai ta kalli yarinyar amma bata san me ake faÉ—a ba.Cikin tsawa matar take yiwa Umma Magana, duk ta ruÉ—ata dan ta kasa gane me take nufi balle ta yi.

A lokacin aka buɗe ƙofar aka shigo, matar gidan ta kalli wacce ta shigo ta hauta da bala'i ita dai Umma ta yi shiru bata san me suke faɗa ba.

Hajiya Shafa da aka damƙa Umma a hannunta ta kalli Umma da ta yi tsuru-tsuru ta ce, "ki riƙe yarinyar ki yi mata wanka, wannan matar bala'i ne da ita sai kin yi da gaske, in ba haka ba tsaf zata dake ki wallahi."

Da mamaki Umma ta ce, "Duka kuma?."

"Kina mamaki kenan? Lallai baki san larabawa ba. Ki riƙe yarinyar nan ki je ki wanke ta."

Umma ta riƙe hannun yarinyar ta ce, "ina ne wajen wankan?."

Hajiya Shafa ta ce, "mu je na nuna miki." Tare suka tafi yarinyar tana turjewa tana ƙwalla ihu, duk ta cika musu kunne da magana.

Hajiya Shafa ta kalli Umma ta ce, "ki ɗauke ta, basa jurar ɗansu yana kuka fa, a kan haka zaku ɓata dasu wallahi."

Umma ta kalli yarinyar ta ga a taƙaice zata yi shekara goma, sannan gata lukuta ce, ta kalli Hajiya Shafa ta ce, "ta ya zan iya ɗaukar yarinyar nan, kalle ta fa?."

"Haka zaki gwada, in wacce ta fita aka ce ki ɗauka haka zaki ɗauka. Kamar baiwa ki ke a gidansu, ko taka ki suka yi suka wuce haka zaki yi haƙuri." Umma ta duka ta ɗauki yarinyar daƙyar tana hakki.

ÆŠakin yaran ta raka ta, suna shiga ta gansa kaca-kaca, an ci abubuwa an watsar ga toys an zubar kamar É—akin mahaukata.

Hajiya Shafa ta ce, "gashi nan, kije kiyi mata wanka sai ki saka mata kaya. Sannan ki gyara waÉ—annan kayan da suka watsar. Maimuna kwana da sanin baza ki yi bacci ba, domin kuwa zasu je makaranta."

Umma ta kalle ta cikin firgici ta ce, "Baiwar Allah zuwa na kenan fa, ko hutawa ban yi ba, ko ɗan abinci ban ci ba balle bacci. Wallahi ƙafafuna a gajiye suke, zaman motar nan gabaɗaya ya sagar min da ƙafafu. Tun safe muka taso, aka samu matsalar mota muka kwana a hanya, yanzu gashi har gari ya yi haske. Kuma ace bazan kwanta ba? In ban kwanta ba ai sai na faɗi."

Hajiya Shafa ta bi Umma da kallo ta ce, "aiki kika zo yi ai ba hutu ba, kar ma ki saka a ranki wai zaki huta a gidan nan, wallahi aiki zaki zage ki yi kamar jaka, dan kaf aikin gidan nan a kan ki yake, ga kula da yaransu. Su basu san uzuri ba, kuma basu san ɓata lokaci ba, in suna so sai an yi kawai babu na gaji."

Umma ta sauke numfashi tana jinjina kai ta ce, "to bara na yi mata wankan."

Hajiya Shafa ta ce, "ya fi miki dai. Sunana Shafa, ni ce waccce suka faÉ—awa suna neman mai aiki a kawo musu, ni kuma na faÉ—awa Oga Musa, shi kuma ya saka aka nemo ki. Duk abinda zaki aikata a gidan nan ni zasu nema su faÉ—awa, dan haka ko rufa min asiri ki zauna dasu lafiya, bana so a É—aga min hankali."

Umma ta shiga banɗakin tana kallon banɗakin, yarinyar ta ƙarasa cikin bathtub ta kunna ruwa alamun a ciki ake yi mata wankan.

Umma bata tsaya ƙarewa banɗakin kallo ba, dan a gajiye take matuƙa tana so ta huta. Ta kunna ruwa ya fara zuwa sai yarinya ta ƙwalla ƙara mai ƙarfi.

Umma ta firgita ta taɓa ruwan dan ta ɗauka ƙonata ta yi, saita ji ruwan sanyi ne kuma bai yi sanyin da zata yi wannan ƙarar ba.

Kafin ta tsayar da ƙarar har an shigo banɗakin, da uwar da uban da yayyenta duk sun hallara an nufe ta ana tambayar abinda ya faru.

Tana gani yarinyar tana faÉ—a musu ita dai tana tsaye bata san me ake cewa ba. Matar gidan ta juyo tana yiwa Umma bala'in da bata san me take faÉ—a ba, ta dai zuba masa ido tana kallo bata fahimci ko kalma É—aya ba.

A lokacin Shafa ta shigo, suka koma kan Shafa suna faÉ—a mata itama tana mayarwa. Suka fito da Æ´ar tasu daga ciki suka fita da ita.

Shafa ta bi Umma da kallo ta ce, "Na faɗa miki wallahi Allah ba a taɓa musu yaransu, ba a taɓa yayansu a zauma lafiya. Ƙauna ƴaƴansu suke yi kamar su ɗiga musu sabon rai, akan ƴaƴansu zasu iya yi miki komai wallahi. Na yi miki bayanin nan, amma daga fita ta har kin canja. Akan cutar musu da yara zasu iya kama ki, kuma a ƙasar Saudia ki ke ba Nigeria ba, kulle ki zasu yi a gidan yari, babu ruwan su dake ba ƴar ƙasa bace."

A sanyaye Umma ta ce, "ban san ruwan sanyi na kunna mata ba, wallahi ban san ya yi mata sanyi ba."

"Waye ya ce ki bari ta shiga ciki? Ai sai kin fara haÉ—a mata ruwan sannan zaki bari ta shiga ciki. Yanzu da na zafi ki ka kunna mata fa?."

"Wallahi ban sani ba, da na san me sanyi ne bazan kunna ba. Tunda kin ga ban san kan gidan ba, ko awa É—aya ban yi da zuwa ba, sai a hankali zan saba."

"Wallahi da ruwan zafi ki ka zuba mata da yanzu sun kira ƴan sanda sun tafi dake. Basa jurar ƙaramar matsala, son jikinsu ne dasu."

Umma ta yi shiru bata ce komai ba, Shafa ta ce, "akan yaran nan sai zaman ki zai ƙare a gidan nan, kin ga dai yau ki ka zo ko? To zaki iya komawa yau. Kinga ke ce da asara, kafin a sake samun wani gidan kin galabaita, gashi baki san gari ba, kuma baki da ko sisi."

Umma ta ce, "to ya zanyi?."

Shafa ta ce, "mu je."

Umma ta biyo ta a sanyaye tana ji kamar ta kifa saboda gajiya mai nauyi, ga kanta yana ciwo, ga yunwar da take ji mai ƙona ciki.

Shafa tabi É—akin yaran da kallo ta ce, "ki gyara É—akin nan, sannan ki je ki dafa musu abinci, lokacin cin abincin su ya kusa."

Umma a galabaice da rauni ta ce, "Hajiya Shafa na gaji, wallahi bazan iya aikata komai a yanzu ba, ina buƙatar hutu. Gaɓoɓina ciwo suke yi min, ga kaina yana ciwo, ga yunwa, ga gajiya. Tafiyar Jeddah zuwa madina ba kusa bace kin sani, tafiya muka dinga yi kamar zamu bar duniya. Gashi mota ta lalace, haka muka zauna a daji ana gyarawa. Don Allah ki ce musu a bari na huta zuwa anjima sai nayi."

Hajiya Shafa ta gyaÉ—a kai tana bin Umma da kallo tana buÉ—e ido tace, "Hajiya meye ma sunan ki?."

"Maimuna nake."

"Maimuna buÉ—e kunnen ki dakyau ki ji abinda zan faÉ—a miki, dan na ga alama baki san inda ki ka kawo kan ki ba...."

"Ina so ki san a inda ki ke, nan ba Nigeria bace, a ƙasar Saudia kike, a cikin garin Madina. A cikin Madinan ma ba ziyara ki ka zo ba, ba hutu kika zo ba, a gidan larabawa kike kuma aiki zaki yi su biya ki."

Ta yi ƙwafa irin baki san dawar garin ba ta ce, "Maimina ina sake faɗa miki basu san ɗaga ƙafa ba, basu san kara ko wani abu hutu ba. Mai aiki akwai sunan ki a wajensu, a haka suke kallon ki ba wacce tazo ta huta ba. Kamar baiwa haka zaki koma a gidan nan, tunda kuɗi zasu baki ba kyauta zaki yi musu ba. Dole ki yi abinda suke so a yanzu, babu ruwansu da yanzu ki ka zo ko kin gaji. Indai kina son samun kuɗin dole ki buɗe ido ki san a inda ki ke."

Umma a gajiye ta ce, "ina son samun kuɗi, kuma na san aiki zan yi, amma tsakani da Allah a bari na huta zuwa gobe ko zuwa dare mana. Tun da muka ɗauko hanyar garin nan a zaune nake, wallahi na gaji, gajiya mai yawa. Babu abinda zan iya yi yanzu, ko sallah da akwai dama yi min za a yi, ƙafafuna jinsu nake kamar ba nawa ba."

Shafa ta ce, "zancen ki ke so, wannan maganar hutun ki haƙura sai dare. Mu je na nuna miki kitchen ki dafa musu abinci, lokaci yana gudu."

Umma ta bi bayanta a sanyaye tana ji kamar zata kifa saboda gajiya da tashin hankali. Suka shiga kitchen É—in, Umma taga babban kitchen ne mai kyau da tsari irin na larabawa.

Ta nunawa Umma komai ta ce, "ki É—auki kajin nan ki gyara su sannan ki gasa a nan" ta faÉ—a tana nunawa Umma oven.

Shafa ta ce, "sai ki dafa shinkafar nan, basa son yaji, basa son ɗanɗano ya yi yawa. In ki ka saka musu yaji mai yawa wallahi babu ruwana. Ga kayan ƙhamshin, sai ki yi amfani dashi yadda ya kamata."

Umma dai tana ji ne kawai ba wani fahimta take yi sosai ba, kanta juyawa yake yi tana ji kamar ta faÉ—i a wajen. Da taimakon Shafa suka fara dafa abincin, dan bata san me

Tana cikin dafawa sai ga budurwar yarinya ta ƙaraso, ta yiwa Shafa magana da larabci ta amsa bayan ta bar wajan ta ce, "wai tana da wanki a ɗaki, ki je ki wanke musu."

Umma ta tsame hannunta daga wanke shinkafar, ta bi inda aka nuna mata. ÆŠakin wanki ne wanda yake É—auke da injinan wanki guda biyu, sai wajan goga da kayan gugar.

Umma ta sauke numfashi ganin kayan tuli masu yawa sosai, gashi sun yi kaca-kaca kamar kayan ƙananun yara masu rarrafe.

Umma ba iya amfani da komai sosai ba, amma bata fita ta tambayi Shafa ba ta dinga bi a hankali har ta kunna ya fara wankin. Ganin ta fara wankin sai ta samu waje ta zauna tana lumshe iso bacci yana figarta sosai.
Chapter 44 · 0% Book details