Sashe 55
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ji na yi yana neman ɗora min laifi, dan Islaha ta bar ƙasar nan ta hannuna sai ya zama ni na kaita?. Ban san ta yi ba, ban ce zo mu je ba, ta je ta yi fasko ta kawo min ta ce na kai ta. Ni kuma a lokacin kanfanin mu yana buƙatar mace irinta, dan na ɗauke ta sai ya zama laifina?. Meye nawa? Me na yi da za a ce ni ce na kai ta?. Dan kawai akuyata ta yi kuka kan waccen tsintacciyar?."
Baffa ya nuna mata ƙofa ya ce, "jeki in baza kinyi shiru ba."
Ta yi shiru tana ɗauke kai ya kalle ta ya ce, "baki da adalci, baki san karamci ba, ba ki san saka alkhairi ga alkhairi ba, ba ki san mai ƙaunar ki ba, ba ki san wanda ya kamata ki so ko kar ki so ba."
Ya ɗan yi shiru saboda ciwon da yake ji sannan ya ce, "yarinyar nan itace ta dinga faɗi tashi akan rashin lafiyata, abinda ta yi ƴaƴan da ki ka haifa da cikin ki basu yi ba. Ita kuwa sai dai ace na riƙe islaha na wani lokaci, amma bazan amsa sunan mahaifi a gare ta ba, dan bani na haife ta ba. Su kuwa kaf ɗinsu ni na haife, basu da wani mahaifi sai ni ɗin. In na kwanta na mutu su aka yiwa mutuwa, domin su suka rasa mahaifi, daman ita Islaha marainiya ce a haka ta tashi, su kuwa in na mutu su aka yiwa mutuwa ba ita ba. Yarinyar nan ta ba da duk wani ƙarfinta da kuɗin ta akan ciwona, ta ruɗe ta fita daga hankalin ta saboda kawai bani da lafiya."
Ya yi shiru yana kallon Mamq na wani lokaci kafin ya ce, "Kuma a haka kina nuna mata ƙiyayya, amma ita bata nuna miki ƙiyayya akan wanda ki ke aure ba. Ta sadaukar da kuɗinta da lafiyar ta da lokacinta saboda ni, ni kuma ke nake aure...."
Ya girgisa kai ya ce, "Islaha bata cancani wannan abun daga wajan ki ba, ko bakya kallon ta a matsayin wacce zata auri ɗanki zaki iya kallon ta a matsayin marainiya wacce bata da iyaye. Kuma ƙarya aka yi ba ke ki ka kaita ƙasar wajen ba? Sau nawa kina so ki kaita, bani nake hanawa ba?. Da yake kin ga bani da lafiya ban san me aka yi ba gashi kin kai ta ai. Wa za a ce in na ke ba? Ba dole ace kece ki ka kai ta?."
Mama ta sassauta murya ba kamar É—azu ba ta ce, "Ni fa ban saka Islaha ba, itace ta kawo kan ta."
"wajan wa ta kawo kanta?."
"Wajena."
"Waye ya kai ta?."
"Ni za a ce na zama sila."
Baffa ya ce, "gashi kin amsa da kan ki. Ba na faÉ—a miki indai ina da rai yarana baza su wannan aikin ba? Meyasa ki ka yi dan kin ga ina kwance?."
Mama ta wani kalle sa ta ce, "Islaha ce fa."
Baffa ya dafe kai jin duk jawabin da ya gama yi mata a banza, gashi tana maimaita masa Islaha ce ai ba Æ´arsa bace.
Ya É—an yi shiru na wani lokaci, ya É—an sauke numfashi ya ce, "wato ita ba Æ´ata ba ce ba ko?."
Ta yi shiru bata amsa ba, Baffa ya kalli Saheer ya ce, "meyasa ban san maganar ba?."
"Nima ban sani ba Baffa, sai bayan ta tafi aka faɗa min. Cewa aka yi kar a faɗa min, kuma ba ita bace kaɗai ba ce, harda Labiba da babar Safeera ƙawar Islaha ɗin."
Baffa ya sauke numfashi ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Harda Labiba?." Saheer ya É—aga kai bai ce komai ba.
Baffa ya zubawa Mama ido ya kasa cewa komai, ta ƙi kallonsa ta ɗauke kai bata ce komai ba tana ji yana kallon ta.
Baffa ya ce, "Harda Labiba ki ka kai?."
Ta ce, "To ai na ji na ta ita ka ke yi ba ai, ta ƴat riƙo ka ke yi tunda ita ka fara tambaya."
Baffa ya lumshe ido ya buɗe ya ce, "Yanzu sai da ki ka kai Labiba ƙasar waje aiki? Me ta nema ta rasa a gidan nan, me ki ka nema ki ka rasa a gidan nan da zaki saka ta fita daga ƙasarta zuwa wata ƙasa aiki?."
Mama ta yi shiru bata ce komai ba, Baffa ya ce, "duk kashedin da na dinga yi miki akan hakan sai da ki ka aikata?."
A sanyaye Adda ta ce, "Ka yi haƙuri Baaffa, ka ga baka da lafiya. A bar maganar don Allah, in ka warware sai a samu mafita in sha Allah."
Baffa ya ce, "wacce mafitar kenan? Ta ɗauki ƴan mata har biyu ta kai wata ƙasar da basu da kowa ki ce a bar maganar? Ban san inda suke ba, ban san a hannunwa suke ba, ban san a inda suke kwana ba. A wajen kirki suke ko a wajen na banza duk bamu sani ba. Kuma ki ce na kwantar da hankalina?."
Saheer ya ce, "kayi haƙuri ka bar maganar Baffa, zamu yi magana daga baya in sha Allah."
"Ta ya zan bar maganar? Ƴaƴana ƴan mata suna wata ƙasar da ba tamu ba, ku dinga cewa na kwantar da hankalina? Ƴaƴana har biyu kuma ƴan mata da basu taɓa aure ba, an ɗauke su an kai su wani waje ba tare da na sani ba. An yi amfani da rashin lafiyata an yi abinda bana so. Yanzu da raina da lafiyata ace yaran nan basa nan? Don Allah ya ake so a dinga kallona a garin nan?."
Saheer a sanyaye ya ce, "duk da haka ka yi haƙuri Baffa, ya riga ya faru sai mu yi haƙuri."
"Dan baka san irin maganar da za a dinga faɗa a kaina ba. Mu fa fulani ne, fulani ne gaba da baya. Fitar wannan maganar babban abin kunya ne a gare ni da dangina. Ace ƴaƴana mata guda biyu sun bar ƙasar nan sun tafi aiki a gidan larabawa, ba fa wajen Yola suka tafi ba, ba wani garin suka tafi ba Saheer, wata ƙasar suka tafi ban sani ba. Saheer in ban damu ba me zan yi?."
"Baffa likita ya gargaÉ—e mu akan gujewa abinda zai saka jinin ka ya hau, ka ga iya wannan maganar zata iya jawowa jinin ka ya hau. Don Allah don Allah ka bar maganar, ni zan san abinda zan yi in sha Allah."
Baffa ya kalli Mama da bata ce komai ba ya ce, "yadda ki ka ɗauke su ki ka kai su ki saka a dawo min dasu, in ba haka ba kuma zan yi miki abidna baki taɓa tunani ba."
Adda ta ce, "babu batun dawowa Baffa, dole sai sun zauna sun biya kuɗin da aka kashe aka kai su. Ka san kuma Mama itama aiki kan aiki take yi, ba wai itace shugaba, tana da na sama da ita. Ƴar sallamar da ake bata in ta samo matan bata taka karya ta yi ta karya ba. Dole sai sun biya kuɗin da aka kai su sannan zasu samu ƴancin da zasu dawo."
Baffa ya yi shiru ya dafe kansa cikim yanayin da bai san meye ba.
Saheer ya ce, "Don Allah Baffa ka yi haƙuri, a bar magnar don Allah."
Baffa bai ce komai ba Mama ta miƙe ta fita, Baffa ya bita da kallo kafin ya kalli Saheer ya ce, "wani abu nake dubawa akan mahaifiyar ku, wani abu kawai nake kallo shiyasa duk abinda take yi min nake ƙyalewa. Amma naga ta kasa ganewa, tana neman ta kai ni bango na kasa ɗauke kai na yi abinda zuciyata take faɗa min nayi."
A tare suka haɗa baki suka ce, "Ka yi haƙuri Baffa."
Baffa ya ce, "Kun yi magana da Islaha? Dan na san Labiba bazata neme ku ba."
Adda ta ce, "ɗazu ma mun yi magana da ita, ta tabbatar min da bata da wata matsala ta samu gida na kirki. Na dinga yi mata faɗa akan meyasa ta tafi, sai ta ce na tambayi Saheer dalilinta na tafiya, wallahi ba a son ranta ta tafi ba. Kuma ta ce na baka haƙuri, tasan ta yi maka laifi mai girma."
Baffa ta kalli Saheer ya ce, "FaÉ—a min dalilin."
Adda ta kalli Saheer ya yi mata alama da ta yi shiru kar ya faɗa, Adda ta ce, "ai bamu yi maganar dashi ba, yanzu zan tambaye sa in sha Allah. Ka huta Baffa, bara mu je, Saheer mu je" ta faɗa tana miƙewa, shima ya miƙe suka fita suka bar Baffa cikin tunanin da ya kasa barin zuciyarsa.
Ya sauke numfashi cikin wani irin yanayi, ko kaÉ—an bai ji daÉ—in maganar nan ba, zuciyarsa zafi take yi akan hakan. Amma bai ga laifin Islaha ba, dan ya yarda da ita, ya tabbatar akwai dalilin tafiyar ta.
Nana Haleema.
[7/3, 5:36 PM] KRBBK: RDB2P38
Nana Haleema.
Adda suna fitowa ta tsayar da Saheer ta ce, "FaÉ—a min wacce matsala ce ta kai Islaha tafiya aiki Jeeda, bayan ni da kai mun san ta tsani aikin nan?."
Ya É—an sauke numfashi cikin takaicin hakan ya ce, "nima ban sanar mata ba, ki tambaye ta."
Adda ta ce, "ka faÉ—a min Saheer, na san ka san komai."
"Raina min hankali kawai take yi, ta aikata wani abu a ɓoye sannan ta tafi ban sani ba. Lokacin da aka sace ta, ta faɗa min komai akan sace ɗin da aka yi, tun lokacin zuciyata take rawa. Nayi-nayi ta faɗa min dalilin ta na so a rufe case ɗin ɗauke ta ɗin taƙi. Kwatsam sai na ji ta tafi Saudia, bayan ta tafi sai nake jin labarin ashe itace ta biya kuɗin aikin Baffa gabaɗaya. Ta ya hankalina zai ɗauki maganar nan? Ya ki ke so na kalli Islaha a wannan maganar?."
Adda da mamaki ta ce, "kamar ya ita ta biya kuÉ—in aiki?."
"Kamar yadda ki ka ji. A lokacin ƙin faɗa min ta yi, sai yanzu Safeera take cewa wai ɗauko kuɗin ta yi a gidan da aka ɗauke ta. Just imagine, wacce aka sace ita ita a ɗauko kuɗi? Sace ɗin da aka yi daɗi ne da shi kenan, tunda har ta iya gani ta ɗauka."