← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 133

Sashe 117

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba ya ce, "Rehaan yadda Mamy ta isa da kai haka na Daada ta isa dani, tana da ikon yiwa kowa a cikin ku hukunci. Na tabbata ko me Mamy zata yiwa É—an da ka haifa baza ka ji komai a ranka ba."

So yake ya faɗawa Abba shi Mamy baza ta taɓa yiwa ɗansa dole akan abinda ba ya so ba, amma sai ya kasa ya sunkuyar da kai kawai.

Abba ya ce, "nima ita ta haife ni, kana ji tana rantsuwa, zan karya mata rantsuwa ne?."

A hankali ya ɗago ya ce, "Amma Abba bana so, meyasa sai ni?. Wallahi Abba ban taɓa jin tsanar abu kamar auren nan ba."

Abba ya ce, "ina ba ka haƙuri a madadinta, ina ba ka haƙuri matsayina mahaifinka, dan na san bamu kyauta maka ba. Don Allah ka yi haƙuri ka karɓa. " Rehaan ya ɗaga kai a hankali yana ji kamar ya yi kuka.

Abba ya ce, "na faÉ—a maka in ka aure ta kana da damar auren duk wacce ka ke so daga baya." Ya sauke nunfashi ba tare da ya yi magana ba.

Abba ya sake tausasa murya ya ce, "ka yi min alƙawari za ka bar auren nan ya yu, ka ɗaukar min alƙawarin baza ka lalata auren ba, ka yi min alƙawari baza ka sake yin wata magana a kai ba."

Ya kalli Abba ya ga shi yake kallo, Abba ya É—aga ka alamun haka yake nufi. Ya yi shiru ya kasa amsawa, bai san ya zai yi da Abba ba.

Abba yace, "alfarma ta farko da na taɓa nema a wajanka wannan ce Rehaan, na san ban kyauta maka ba, amma mahaifiyata nake yiwa biyayya. Ka yi min alƙawari akan hakan?."

Ji yake kamar ya yi kuka, Abba ya saka shi a tsaka mai wuya, Abba ya ɗaure sa da jijiyoyin jikinsa. Tsakani da Allah ta ya zai ɗauki alƙawari akan abinda ba ya so, ta ya zai ɗauki alƙawarin da ya san bazai iya cikawa ba?.

Abba ya ce, "ina jinka, za ka yi min Rehaan abinda na nema?."

A hankali ya ɗaga kai alamun zai yi, Abba ya ce, "ka yi alƙawarin?." Ya jima a haka bai motsa ba, sai kuma ya ɗaga kai alamun ya yi.

Abba ya murmusa ya ce, "Na gode sosai, kar ka zama mai saɓa alƙawari a wanann lokacin, a duk lokacin da ƙin auren ya taso maka a zuciyar ka, ina so ka tuna alƙwarin da ka yi min."

Shi dai bai motsa ba yana zaune yana ji kamar an saka shi a cikin wuta sbaoda zafin da yake ji.

Abba ya ce, "Za ka yi taron biki ne?."

Ya É—ago kai ya ce, "Bana so, inda zai yu bana so kowa ya san za a yi auren nan Abba, in dai ba a cikin gidan nan ba, don Allah kar a sani. Ka yi min wannan alfarmar nima!."

Abba ya ce, "ta ya auren ka zai ɓuya? Kaima ka san bazai yu ba."

"A saka ya yu, a rufe shi ya zama babu wanda ya sani. Ko a falon nan ne ku É—aura auren ba sai a masallaci ba."

Abba ya bisa da kallo ganin da gaske yake maganar ya ce, "Meyasa ba ka so a sani."

"Saboda bana so."

"Ba ka yi haƙurin ba?."

"Na yi Abba, yin haƙurin ne ya saka na ce bana so a sani."

Abba ya ce, "shikenan Rehaan, tunda ba ka so a sani zan san abinda zan yi a kai in sha Allah."

Rehaan ya ce, "ka san wacece yarinyar?."

Abba ya É—aga kai ya ce, "eh na sani, har na turawa Jafar adireshinta, sai ku je ku gaisa. Tana da kirki sosai, sai da na tabbatar da nagartarta sannan na amince ka aure ta.

Rehaan ya yi wani murmushin takaici jin ana yabon yarinyar da ya san wacece ita, wai tana da nagarta. Ya buÉ—e baki zai yi magana sai ya fasa, ya yi shiru yana jin Abba.

Abba ya ce, "ka kwantar da hankalin ka, nima da ace yarinyar bata dace dakai ba bazan amince ba. KuÉ—i ne kawai bata kai ka ba, amma komai nata da na haÉ—a shi da naka iri É—aya."

Ya kawar da kai yana mamakin ya aka yi halinta na banza ya ɓuya ne?.

Abba ya ce, "tashi ka je, Allah ya yi albarka. Ina so ka tuna da alƙawari kaya ne." Ya amsa da amin ya tashi ya fita, ɓangarensa ya koma sai kuma ya sakko ya shiga mota aka ja shi ya fita.

••••••

Islaha tana gidansu Safeera a kwance kamar mai zazzaɓi, gabaɗaya jikinta babu ƙarfi sai kwanciya take yi a duk inda ta samu dama.

Safeera ce take ta rarrashinta, ita dai sai dai ta ɗaga kai amma Allah kaɗai yasan yadda ta damuwa ɓatan masoyinta.

Sai da ta yi sallar magrib sannan ta fito, a hankali suke tafiya babu wanda yake yiwa wani magana dan bata da nutsuwa balle ta ce wani abun.

A lokacin wata baƙar motar ta wuce su ta yi parking gab da ƙofar gidansu Saheer, basu kula da ita ba suka cigaba da tafiya a nutse har suka zo inda motar take.

Suna zuwa wajan aka buÉ—e motar murfin motar ta tare musu hanta, suka kalli motar a tare suka É—auke kai.

Wani mutum sanye da baƙaƙen kaya ya fito ya ce, "Barka Islaha."

Ta ɗan tsaya ta kalle sa, ganin bata san shi ba sai ta sake ɗaure fuska a daƙile ta ce, "barka" ta faɗa tana niyar barin wajan.

"In ba za ki damu ba ina so zan yi wata ƙaramar magana dake."

Ta É—an juyo ta ce, "gaskiya zan damu, na gode."

Ya yi murmushi jin amsar da ta bashi ya ce, "magana ce akan ɓatan Saheer."

Cak ta tsaya tare da waiwayowa ta kalle shi ta ce, "me ya faru?."

Ya kalli Safeera ya sake kallon Islaha ya ce, "Ina so ki shiga motar nan, akwai inda nake so mu je, in sha Allah za ki samu mafita akan matsalar ki."

Islaha ta kalli Safeera da take kallon mutumin ta ce, "kamar ya ta shiga mota?."

Ya kalli Safeera ya ce, "yi haƙuri Safeera, ba cutar sa ita zan yi ba."

Safeera ta buÉ—e ido jin ya kira sunanta, sai ya yi murmushi ya ce, "Babu abinda zan yi mata na cutarwa, kawai ina so ta shiga motar ne, ni kuma zan kai ta inda zata samu maganin damuwarta in sha Allah."

Islaha ta kalle sa a kaikaice ta ce, "sai aka ce maka ina buƙatar taimakon ka ne?."

Ya ɗan murmusa dan kafin ya zo an karanta masa halayenta ya ce, "ko ba ki ce ba kina da buƙata, ki shiga kawai."

Ta harare sa, hararar up and down ta ce, "Bazan shiga ba, da kai da maganin damuwar ta ka ku je bana buƙata."

Ta juya zata bar wajan ya ce, "in ba ki shiga ba za ki yi danasani Islaha, zai fi miki ki zo ki shiga mu je."

"Sai maimaitawa ka ke yi kana cewa baza ka cuce ni ba, yadda ka ke faÉ—a ya tabbatar min da kai É—in macuci ne. Bazan shiga ba, in ka ga za ka É—auke ni ka saka a motar sai ka yi. Aikin banza kawai, baka san me yake damun mutum ba ka zo ka ishe sa da surutan banzada wofi!" Ta faÉ—a a fusace tana kallonsa.

Maimakon ya ji haushi sai ya yi murmushi ya ce, "ki yi haƙuri, ban faɗa dan na ɓata miki rai ba. Amma don Allah ki shiga motar nan mu je." Ta ja wani dogon tsaki ta yi gaba abinta.

Safeera ta kalle shi ta ce, "to kai akan me ka takura sai ta shiga motar ka ne? Ka ƙyaleta mana, ko ana dole?."

Ya ɗan yi murmushi ya ce, "Ba a dole, amma ana buƙatar ta shiga ɗin." Safeera itama ta yi tsaki ta bi bayan Islaha da ta shige gida abinta.

Waya ya ɗauko yana dannawa kafin ya saka a kunne, cikin ladabi da gimamawa ya ce, "ta ƙi shiga motar Sir."

Ya yi shiru alamun ana bashi amsa kafin ya ce, "Okay Sir" ya faÉ—a yana kashe wayar ya shiga mota ya bar unguwar.

Nana Haleema.
[7/27, 11:49 AM] KRBBK: RDB2P88
Nana Haleema.

Washe gari har aka yi sallar azahar bata fito ba, tana ɗaki a kwance ko breakfast ta kasa yi. Tana ji ana zancen za a siyar da gidan da ake ciki a karɓo Saheer bata iya fitowa ba, sai daga baya ta miƙe ta yi wanka ta shirya ta fito daga gidan. Gidan radio ta yi nufin zuwa dan ta kai koken ta ko Allah zai saka mutane su ji su taimaka mata, bata so ta je gidan radion da take aiki, shiyasa kawai ta hau napep ta tafi ko Safeera bata faɗawa ba.

Kallon window napep É—in take yana tafiya a hankali, a haka ya É—auki passenger maza guda biyi ita dai tana zaune bata ce komai ba, dan inda sabo an saba haÉ—a mata da maza a napep guda É—aya.

Islaga sai ta ga ya canja hana, gabaÉ—aya bai É—auki hanyar da ta ce masa zata je ba.

Kasancewar bata da duhun kai sai ta ce, "A'a, Malam ina za ka je ne? Ni ba nan na yi ba."

Ya yi shiru bai ce mata komai ba sai cigaba da tafiya da ya yi bai motsa ba.

Islaha ta ce, "magana nake yi maka fa, ina za ka kai ni?..."

Nan ma ya yi shiru bai ce komai ba, ta fusata ta ce, "Wallahi zan yi....."

ÆŠiff maganar ta tsaya, yi jin wani abu kamar bindinga daga gefenta.

Ta buÉ—e ido ta kalli wajen a hankali, ta ga bindinga ce wanda yake zaune a gefenta ya saka mata alamun ta yi shiru.

Ta kalli fuskarsa ta ganta a buÉ—e bai rufe ba, amma ba ita yake kallo ba titi yake kallo. Ta yi É—if, duk rashin kunya da tsiwar sai ta yi shiru gabanta yana faÉ—uwa.
Chapter 117 · 0% Book details