← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 133

Sashe 114

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Magaji ya amsa ya bar wajen, su dai sun ji ihunn matan wajen, sai tsawar da Magaji yake yi musu, ashe har ya murÉ—e kan jaririn an cilla shi cikin rami. Wannan rashin imanin ya ja zuciyar mai jegon ta buga, itama ta bi É—anta.

Saheer sai da ya yi kuka, shi kuma Likita tuni an sallame shi shida ɗan uwansa sun tafi. Haka aka tattare su aka shiga dasu wani waje, Sudaisa da Sudais da Saheer a waje ɗaya aka bar su, saboda baza a takura masu ba saboda Sudaisa. Duk an kwashe su an ɓoye a cikin bukka saboda su ɗin jari ne, ana jiran shigowar sojojin da aka samu masaniyar zuwansu.

•••••••

Mamy tunda aka yi kiran sallar asuba take kallonsa Rehaan, ta kasa tashinsa ya yi sallah saboda ta san bai jima da yin bacci ba.

A hankali ya buÉ—e ido, sai ta kunna hasken É—akin tana kallonsa ta ce, "Good morning Rehaan, lokacin Sallah ya yi."

Ya ɗan miƙe zaune daƙyar yana saule numfashi a hankali, sai ya ɗan nutsu sannan ya kalle ta ya ce, "Morning Mamy."

Mamy ta ce, "Ya ciwon cikin?."

Ya girgiza kai ya ce, "da sauƙi."

"to tashi ka yi alwala kar a tayar da sallah, an yi kira."

Ya miƙe a hankali ya sauka daga kan gadon, Mamy ta zuba masa ido tana kallo har ya miƙe tsaye sosai yana runtse idonsa. Bai kalle ta ba ya shjga bathroom ɗin ita kuma ta fita daga ɗakin.

A falo ya same ta bayan ya fito ya ƙarasa inda take ita kuma tana kallonsa ta ce, "za ka iya zuwa masallaci?."

Ya girgiza kai alamun bazai iya zuwa ba, shinfiÉ—a masa sallaya ta ce, "To ka bi jam'i daga nan." Bai musa ba ya hau kai ya tsaya ya tayar da ra'akatal fijir. Yana idarwa aka tayar da sallah suka yi sallah tare da masallaci.

Bayan ya idar ya jingina da kujera idanunsa a lumshe, ya jima a haka kafin ya buÉ—e ido ya kalle ta ya ce, "Good Morning Mamy."

Ta É—ora hsnnunta a gashinsa ta shafa ta ce, "Ya jikin ka?."

Ya yi murmushi ya ce, "na ji sauƙi."

Ta yi murmuahi ta ce, "za ka sha tea ko?."

Ya É—an rausayar da kai ya ce, "Kar ki wahalar da kan ki."

Bata ce komai b ta miƙe ta sauka ta shiga kitchen ta kawo masa black tea mai zafi, dan ta san ba ya shan madara.

A kan kujera ta same shi, iyama zauna ta ce, "ka yi azkhar?."

Ya ɗaga kai alamun ya yi, ya miƙa masa tea ɗin ta ce, "ka sha sai ka koma bacci."

A lokacin Abba ya shigo falon da sallama, duk suka ɗaga kai suna kallonsa har ya ƙaraso. Ya zauna gefensa, ya zama sun saka shi a tsakiya sannan ya ce, "ni ai ban san ya dawo ba, sai yanzu Riyya take faɗa min......" Ya kalli Rehaan ɗin ya ce, "Sannu Rehaan, ya ciwon cikin?."

A sanyaye ya ce, "Na ji sauƙi Abba. Lokacin da na dawo je zan gaishe aka ce baka nan, shine na shigo nan."

Ya kalle shi cikin tsananin tausayi ya ce, "wannan ciwon ciki yana wahalar da kai, kalli yadda ka rame lokaci É—aya. Na rasa wanne irin ciwo ne wannan, an yi duban duniya ba a ga komai ba."

Rehaan ya É—an sauke numfashi bai ce komai ba yana sipping tea a hankali. Sai kuma ya ce, "Ina kwana Abba."

"Lafiya lau. Yanzu ya daina yi maka ciwon?."

"Ba ya yi sosai, sai kaÉ—an."

"Allah ya ƙara lafiya."

"Amin Abba."

"Ka kwanta in ka gama shan tea É—in, in ka sake yin bacci za ka ji daÉ—i sosai."

Abba ya kalli Mamy da take gefensa a zaune ya ce, "Nadira mu bar shi ya huta, mu je ko?" Ya faɗa yana miƙewa, babu yadda Mamy zata iya haka ta miƙe ta fita ba dan ta so ba, in a son ranta ne yadda suka kwana tare a haka zasu yini.

Suna fita ya ajjiye tea É—in hannunsa ya kwanta kan kujerar ya lumshe idonsa.

Bacci ya yi sosai har bayan sallar azahar yana bacci, sai ƙarfe biyu na rana sannan ya farka, kuma sai ya ji daɗin baccin dan babu sauran ciwon kamar ɗazu. A haka ya tashi ya yi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya ya zauna a falon.

A lokacin Mamy ta shigo ita da Riyya da Banishs da kuma Jafar. Ya É—aga kai yana kallonsu kamar yadda suke kallonsa.

Mamy ta yi murmushi ta ce, "Lallai jiki ya yi kyau."

Ya yi murmushi ya ce, "na ji sauƙi Mamy. Ina yini."

"Lafiya lau, ka tabbatar ka ji sauƙi?." Ya ɗaga kai yana kallon Banisha da take kallonsa.

Ya miƙa mata hannunsa ya riƙota ta zauna a kusa dashi, ta kallesa ta ce, "ya daina yi maka ciwon?." Ya ɗaga mata kai yana murmishi.

Ya kalli Riyya da take riƙe da tray a tsaye, ganin yana kallonta sai ta ajjiye ta riƙe hannunsa ta ce, "Ya jiki?."

"Na ji sauƙi Riyya."

Ta ce, "Ga lunch na kawo maka."

Ya É—aga kai ya ce, "Na gode."

Ta ta yi serving ɗinsa white rice da vegetable sauce wacce aka yi ta da chicken breast. Maimakon ya karɓa ya ci sai Mamy ta karɓa, ita ta dinga bashi abincin har sai da ya ci da ɗan yawa sannan ya ce ya isa.

Jafar dai yana tsaye yana kallonsu cikin burgewa, gabaɗaya ahlin Mamy abin sha'awa ne, suna son junansu sosai, suna ƙaunar farin cikin juna, suna son kowa ya rayu lafiya ba tare da wata lalura ba. Babu kamar Rehaan, kamar duk sun fi son Rehaan akan kansu, in Rehaan babu lafiya su kan iya kasa bacci, su saka shi a gaba suna kuka har gari ya waye.

Jafar ya ce, "Mamy ki ƙyale sa ya ci da kansa, sai wahalar mana dake yake yi."

Ta yi murmushi ta ce, "kaima zo ka zauna na ba ka da kaina."

Ya yi dariya dan shi wallahi Mamy burge shi take yi matuƙa, bata wani siriki dashi kamar Rehaan take kallonsa. Tsaf in ya zauna zata bashi abinci a baki kamar yadda ta bawa Rehaan, sai dai shi ya ji kunya ba dai ita ba. Yana ganin banbanci sosai tsakanin iyayensu da suka kasance jinin fulani, da kuma Mamy da take yar wata ƙasar, yana ganin yadda ake jan yaro a jiki ana nuna masa soyayya a zahiri, ba kamar fulani da suke yin fulako ba. Mamy bata jure rashin lafiyar Rehaan ko kaɗan, ko a gaban waye tana nuna Rehaan ɗanta ne, sai dai ka ce duk abinda zaka ce.

Ya zauna yana murmushi sannan ya ce, "na ƙoshi Mamy."

Rehaan ya karɓi tea ɗin hannun Mamy ya ce, "zan sha da kaina Mamy." Ya cigaba da shan tea ɗin suka yi shiru suna kallonsa.

Jin an yi sallama ya saka duk suka juya suna kallon Abba da ya shigo. Abba ya ƙaraso ya ce, "lallai Rehaan jiki ya warware, na yi tunanin bacci ka ke yi, na leƙo ɗazu na ga kana ta bacci."

Rehaan yana murmushi ya ce, "na ji sauƙi Abba."

"Na ga alama kam, gashi nan ka yi kyau abin ka." Rehaan ya yi murmushi yana kallon tea É—in hannunsa kamar mai ganin wani abun a ciki.

Mamy ta ce, "zamu fita ni da Riyya, zamu je mu taro baƙi."

Abba ya yi murmushi ya ce, "mutanen India sun fara sauka kenan."

Ta É—an gyaÉ—a kai tana murmushi ta ce, "Eh sun fara, zan kai su guest house su zauna."

Da mamaki Abba ya ce, "baza su zo nan ba?."

Ta ɗan girgiza kai ta ce, "gwara su zauna a guest house ɗin." Bai ce komai ba ta miƙe ita suka fita dasu Banisha da Riyya.

Abba ya kalli Rehaan ya ce, "ka dawo bikin Jafar ko bikin Riyya?." Shi dai murmushi yake yi amma bai ce komai ba.

Abba ya sauke numfashi ya ce, "Rehaan maganar auren ka ta tabbata, da gaske dakai za a haÉ—a aurenku ranar juma'a in sha Allah. In Allah ya kaimu jibi saura sati É—aya."

Nana Haleema.
[7/27, 11:49 AM] KRBBK: RDB2P86
Nana Haleema.

Rehaan ya ɗago ya kalli Abba sai kuma ya sauke kai ƙasa bai ce komai ba. Abba ya tausasa murya ya ce, "Ka yi haƙuri Rehaan, na san za ka ji ba a kyauta maka ba, amma ka yi haƙuri baka san me Allah ya ɓoye ba."

Calmly ya ce, "Abba amma ban san yarinyar ba, kawai sai na aure ta? A jira ni na kawo matar da kaina mana, duk daren daÉ—ewa ai zan yi auren."

Abba ya ce, "haka ne Rehaan, amma ka yi haƙuri kamar yadda na ce, ka karɓa da zuciya ɗaya, kar ka kalle sa da wani abun daban. Na san za ka ce meyasa sai kai kaɗai, kaf ƴan uwanka babu wanda aka yiwa haka sai kai. Ina so na tuna maka tabbacin kai ɗin na daban ne kenan, ɗaukakar da Allah ya yi maka ce ta kawo haka. Babu yadda zan yi, mahaifiyata nake yiwa biyayya, kaima ka yi min biyayya ka amince."

Ya É—an sauke nunfashi bai ce komai ba dan bai san me zai ce ba, wanne irin aure ne wannan kamar na wasan yara.

Abba ya kalli jafar ya ce, "ga Jafar nan, ya yi bincike mai yawa akan yarinyar, kuma ya tabbatar tana da ilimin addini dana zamani. Ƴar jarida ce cikakkiya, kuma tana da tarbiyya da kamewa, in Allah ya amince baza ka yi danasani ba."

Rehaan ya É—aga kai ya ce, "To."

Abba ya ce, "yauwa Rehaan, Allah ya yi albarka, yadda ka ta ya ni yiwa mahaifiyata biyayya Allah ya sa ka ga amfanin yi min biyayya."
Chapter 114 · 0% Book details