← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 133

Sashe 119

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru ya yi bai ce komai ba, zata sake magana ya buɗe idanunsa cikin nata ya ce, "shut up! Bana buƙatar ki yi magana...."

Ya nuna ta da yatsa ya ce, " Kin yi nasarar shiga rayuwata, kin yi nasarar da ki ka saka iyayena suka amince dake, kuma kin yi nasara ina yia iyayena biyayya akan duk abinda suka ce na yi."

Zata sake magana ya katse ta ya ce, "I will marry you for five months as a contract, because of my father's command."

Banzan kallo ta yi masa sannan ta ce, "bana buƙata, bani da ra'ayi balle har na aure ka na zauna da kai a ƙarƙashin contract. Ka je ka samu wata amma ba Islaha ba, ita tace bata yi ka haƙura ko ka yi danassani. She's not your type, and she's not your class. An kawo min talla na ce kuma bazan siya, a kai wani gidan zasu iya tayawa!."

Ta kalli Jafar da yake kallon ikon Allah, duk da ba ɗaga murya take yi in tana maganar ba, amma ya san maganar tana shigar Rehaan. Shi dai yana so ya ga an yi auren nan dan ya ga ya abin zai kasance, amma ya san abu ne mai wahala matuƙa wajan yuwar auren.

Islaha ta kalli Jafar ta ce, "please ka saka a mayar dani, bana son tsayuwa a nan ko kaÉ—an."

Jafar ya miƙe yana murmushi ya kalli Rehaan da kamar bai san abinda aka yi ba.

Ya buɗewa Islaha ƙofa ya ce, "ki je mota, zasu mayar dake Miss."

"Na gode....."

Ta ɗan waiwayo tana kallo Jazy, ta nuna masa Rehaan da hannu sannan ta ce, "Ka faɗa masa kar ya sake gangancin sace ni, ni ba toy ba ce da zai ɗauko duk lokacin da ya ga dama, ni ba sa'arsa ba ce, ya sace wasu ya zauna lafiya, amma ban dani. Maganar aure kuma a kai tallah social media, a rabawa bloggers details ɗinsa wataƙila a dace, baza a rasa masu buƙata ba. Wannan Islahan ta Saheer ce, ya je ya dage ya cigaba da advert, zai iya dacewa wata ƴar wahalar ta gani ta ya, amma ba da nan" ta faɗa tana nuna kanta sannan ta juya ta fita da sauri.

Wai ta ya auren nan zai yu ne? Rehaan ya ɓullo da auren yarjejeniya, ya abin zai kassance ne?💃🏻🤣
[7/28, 12:20 PM] KRBBK: RDB2P89
Nana Haleema.

Jafar ya kalle shi bayan ta fita ya ce, "Rehaan wanne irin auren yarjeniya kamar a america? Meye hakan?."

Bai kalle sa ba sai shiru da ya yi ya zubawa waje É—aya ido, yana tuna kalamanta yana jin zafi a ransa, kuma ba kowa ya jawo masa wannan rainin ba sai Abba.

Jafar ya É—auki takardar da ya ajjiye ya ga takardar contract É—in ce, har ya tsara rules da komai, an yi printing, ga inda zata saka hannu ga inda zai saka hannu.

Jafar ya kalle shi cikin fusata ya ce, "wani lokacin in ka yi wani abun kamar a rufe ka da duka wallahi, yanzu meye wannan don Allah? Kana musulmi gaba da baya za ka wani ƙirƙiri auren yarjejeniya?."

Ya ɗago ya kalle shi ya ce, "Na yiwa Abba alƙawari, Abba bai taɓa neman abu a wajena ba sai wannan lokacin, kuma na ce zan yi. Ka fi kowa sanin bana son auren nan, kuma bazan so ba, bana son yarinyar, kuma bazan so ta ba. Gwara a gina auren a ƙarƙashin contract, in na san auren yana tafiya akan lokacinsa zai fi min sauƙi."

Ya girgiza kai ya ce, "hakan bai kamace ka ba ko kaɗan, bai kamata ka gina auren a ƙarƙashin yarjejniya ba. Kuma in na yarjejeniyar ne, ina laifin na shekara ɗaya, sai ka saka wata biyar?."

Ya ɗago ya kalle sa ya ce, "kwana na yi ina tunanin maganar nan, ban taɓa tunanin wani abu a rayuwata kamar wannan ba. Wata biyar ɗin ma ya yi min yawa, in kwanakin basu yi ƙasa ba bazai yi sama ba."

Jafar ya ce, "to ga shi nan ai ta ƙi yarda."

Ya ɗan girgiza kai ya ce, "daman saboda Abba nake yi, kuma ya ce baya so ya ji wata matsala daga side ɗina, in daga ɓangarenta ne wannan bai dame ni ba daman ba so nake yi ba. Me zan yi da wannan abar?."

Jafar ya murmusa ya ce, "Ikon Allah, ni dai zan ga ta wannan abin nan zai yu."

"Shiyasa nake ji kamar na je na matse tsohuwar can na zuba mata poison ta haɗɗiye ta mutu. Allah ban taɓa jin haushinta kamar wannan lokaci ba."

Ya yi dariya ya ce, "gaskiya dai, haka kawai ta É—auko maka aure."

"Auren ma da wannan yarinyar, wacce ta gama...." Jafar ya yi dakatar dashi ya ce, "za ka yi bayani da larabci a gaban Allah, babu ruwana."

Ya girgiza kai Jafar ya cigaba da karata rules É—in takardar, ya kalle shi ya ce, "auren ka bazai zama na sirri ba fa, dole za a sani."

Ya girgiza kai bai ce komai ba Jafar da yake kallon abinda yake cikin takardar ta ce, "wannan aure dai za ku gina shi akan abinda ku ka ga dama ne, babu ruwan wani da wani kenan?."

Rehaan bai ce masa komai ba, Jafar ta gama karanta takardar kafin ya ajjiye masa ya miƙe ya shiga ciki. Shi kuma Rehaan fita ya yi daga gidan yana so ya je inda dangin Mamy suka sauka.

Islaha tana fitowa ta ga baƙar motar tana jiranta, ta kalli mutumin da ya tare ta a daren jiya yana cewa ta shiga motarsa. Ba dan bata san hanya ba wallahi babu abinda zai saka ta shiga motar, ta yi ƙwafa ta shiga suka tafi.

A ƙofar gidan suka ajjiye ta, tana sauka daga motar suks haɗa ido da Sadik shi da Safeera sun fito daga gidan.

Ta ƙaraso wajan duk kallonta suke yi Safeera ta ce, "Daga ina haka?."

Islaha ta kalle su ta ce, "wani waje."

Safeera ta ce, "ina ne wajan?."

Ta kalle ta sannan ta kalli Sadik ta ce, "in na faɗa mu ku ba yarda za kuyi ba, za ku ce ƙarya nake yi. Gwara na yi shiru da maganar."

Safeeta ta ce, "baza mu ƙaryata ki ba, ki faɗa kawai."

Ta É—an shiru kamar mai tunani sannan ta ce, "ina zuwa, bara na yi sallar la'asar" ta faÉ—a tana shiga gidan suka bita da kallo.

A zauneta same su a harabar gidan cikin inuwa, ta ƙaraso ta zauna ta ce, "Hamma Sadik ya batun mutanen nan? Sun sake yin wayar ne?."

Ya girgiza kai ya ce, "basu yi ba, har yanzu shiru."

"Batun kuÉ—in fa."

"To an dai saka gidan nan a kasuwa, har yanzu ba a samu masu siya ba wallahi. Gona dai an taya, muna jira mu ji ko zasu siya."

Islaha ta ta yi shiru bata ce komai ba. Safeera ta ce, "muna jin ki."

Ta É—ago ta ce, "Ban san me yasa ba, amma ina ji a raina akwai wani abun ba daidai ba."

Safeera ta ce, "na me kenan?."

"Akan Baffa nake magana, washe garin ranar da aka rasa Hamma ya kira ni wai wasu sun zo neman aurena kuma ya amince musu, dan kar ya bada ni ne naga kamar bai kyauta min ba, amma da yanzu ya ce ya basu ni."

Sadik ya ce, "Nima ya faÉ—a min maganar."

Ta É—an kalle sa ta ce, "ashe ka sani ma. Ban san meyasa Baffa ya yi haka ba, kamar ya manta da Hamma? Kamar ba shine yake cewa zai aurawa Hamma ni na kusa ba."

Safeera ta ce, "wai Baffa da kansa ne ya ce haka?."

"Shine."

"to ya batun auren ki da Hamma?."

"Nima ban san meyasa ya ce haka ba, ban san meyasa Baffa ya canja ra'ayinsa akan aurena da Hamma ba. Abinda na sani ko waye bazan amince ba, auren Hamma ya fi min auren kowa a duniyar nan. Duk kuÉ—in mutum ba ya gabana, indai Hamma yana da rai ni mallakinsa ce."

Sadik ya numfasa ya ce, "abin ne da É—aure kai, ba a satin nan Baffa ya ce zai É—aura auren ku ba?."

Islaha ta ce, "juma'a mai zuwa ya ce, amma yanzu an canja ya koma wani daban ba shi ba."

Ya É—aga kai ya ce, "Kuma na tabbatar Saheer É—in bai sani ba, kuma wannan maganar cutar dashi zata yi ba kaÉ—an ba."

Islaha ta ce, "shine abinda nake ji, tsakani da Allah ta ya za a ce haka?."

Safeera ta ce, "Wai waye wanda za ki aura É—in? Su waye suka zo neman auren ki?."

Ta É—an kalle su sai kuma ta ja tsaki ta ce, "Lokacin da ya faÉ—a min bai faÉ—a min sunan waye ba, ya dai faÉ—a min sunan mahaifinsa mutumin. ÆŠan gidan Alhaji AbdulAziz Yola ne."

A tare suka zaro ido waje cikin mamakin sunan wanda ta faÉ—a Sadik ya ce, "kai! Wai shi ne da kansa ya aiko nemawa É—ansa auren ki?."

Islaha ta ce, "abin kamar plan ko? Ni kaina ina ganin abin kamar tsarawa aka yi."

Sadik ya ce, "Gaskiya akwai ayar tambaya a kan maganar nan."

"Ni dai taimako bai yi min rana ba, haka kawai na tsinci wata tsohuwa a hanya na taimaka mata, ashe wai itace babar AbdulAziz Yola É—in."

Safeera ta ce, "Gaskiya dai lamarin nan kamar plan, kawai dan kin taimaka mata sai a aura miki jikanta?."

Sadik ya ce, "Wanne ɗan nasa a cikin yaran? An ce yaransa kaf suna da aure, wanne daga ciki ne zai ƙara aure a cikinsu?."

Ta É—an yi jimm tana tunanin ta faÉ—a musu ko ta yi shiru, ta kalle su ta ga duk ita suke kallo alamun suna jiran amsa.

Sai ta É—an ja tsaki ta ce, "ku share kawai, sanin waye ba shi da mahimmaci a halin da mu ke ciki. Yanzu ma da ku ka ga an sauke ni a mota shi mutumin ne ya saka aka kai ni can...."

Sai ta kalli Safeera ta ce, "Jiya da wani yake bina yana cewa na zo na shiga mota?” Ta faɗa da sigar tambaya.

Safeera ta ce, "eh."
Chapter 119 · 0% Book details