← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 133

Sashe 96

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba bai ce komai ba ya miƙe ya shiga ɗaki, ta bi sa da kallo ta ce, "Wallahi sai auren nan ya yu, sai na tabbatar da auren nan ya tabbata ko da zan rasa wani abu nawa. Bazan bari a yi binciken ba, ni na san abinda zan yi" ta faɗa tana tashi ta fita cike da mugunta a ranta.

Nana Haleema.
[7/20, 10:27 AM] KRBBK: RDB2P70
Nana Haleema.

    Riyya suna tare da Ikram da Janan, suan ta zaɓen fabrics na biki, ga kaya nan a gabansu a jibge kamar ba a so, ana ta haɗawa ƙawaye packs ɗinsu, dan bikin manya ne, bikin ƙanwar Rehaan Yola komai na package ɗin ƙawayen amarya kyauta za a bayar, babu batun siyan anko. Bayan kayan sakawa a pack ɗin, harda kuɗin ɗinki za a sakawa ko wacce a cikin pack ɗinta.

Janan ta ce, "Ya batun musician É—in ne? An gama komai?."

Riyya ta ce, "an gama yin komai, babu abinda ba a yi booking ba. Indian night ma an gama yin komai, kuma ba ki siyi outfit É—in ki ba."

Ikram ta ce, "waye ya ganni a kayan india, ban taɓa sakawa ba fa."

Riyya ta cee, "kuma dole ki saka. Kin ga nawa nan" ta faÉ—a tana buÉ—e musu wani milk kaya mai kyau.

Janan ta ce, "Wow, amma ya yi kyau. Zai yi miki kyau sosai. Ina na Hamma Rehaan?."

Janan tana faɗar hakan gaban Ikram ya faɗi, amma bata nuna ba ta ce, "zan so na gansa cikin kayan india, na tabbatar ba ƙaramin kyau zai yi ba."

Janan ta ce, "ba ki taɓa gani ba? Ni na taɓa gani ya saka sau ɗaya, yana sakawa ya cire wai babu daɗi."

Riyya ta yi dariya ta ce, "bara na kirasa yanzu, bai faÉ—a min gift É—in da zai bani ba" ta faÉ—a tana É—aukar waya ta kira sa ta saka a speaker.

Yadda wayar take yin ringing da bugun zuciyar Ikram, ta É—an yi shiru tana jira ya É—auka amma sai ta katse bai É—auka ba.

Riyya ta ce, "Mr busy, Matarsa ta shiga uku, ko yaushe yana kan waya akan kasuwanci, in ba waya ba laptop, ki rasa inda zai kai kuÉ—i."

Janan ta ce, "ya za a yi ya yiwa matarsa? Ai duk wannan abubuwan nasa sauke sa zai yi a sha love."

Riyya ta yi dariya ta ce, "Kuma fa haka ne." Zata sake yin magana kiransa ya shigo wayar.

Ta É—auka ta saka a speaker ya ce, "Riyya."

Ta ce, "Na kira ba ka É—auka ba."

"Ina ganin kiran, kawai dai na kira ki ne yanzu.
Ya aka yi?."

"Ba ka bani gift ba."

"Wanne gift?."

"For my wedding."

Ya É—an yi dariya ya ce, "oh amarya."

Ta É—an yi dariya kaÉ—an bata amsa ba, sai ya ce, "ni ban san me zan ba ki ba Riyya, amma ki tura min abinda ki ke so."

Ta ce, "ka san me nake so?."

Ya yi shiru bai amsa ba, Riyya ta san jiran ƙarshen maganar yake yi sai ta ce, "ni kawai ka zo bikin, shine kyautar da zaka yi min."

"Riyya abun babu sauƙi, ina da aikin da zan yi, zuwana zai zama under probability."

Cikin shgwaɓa ta ce, "Ni dai don Allah ka zo, bazan ji daɗin ace bikina baka nan ba."

Ya É—an sauke numfashi ya ce, "Okay. Ina Kiddo?."

"Tana wajan Mamy."

"ke kina ina?."

"Ina tare da Ikram da Janan."

Ya É—an yi shiru kamar bazai yi magana ba sannan ya ce, "suna ji babu wanda zai yi min magana?."

Janan ta ce, "ni fushi nake da kai, na kira ka har sau huÉ—u baka kira ni ba."

"Sorry Jan, amma kin san bana so a tara min kira."

"Zan kiyaye."

"Good gal."

Ikram ta ce, "Yaya Rehaan."

A hankali ya ce, "Ikram."

Ta ce, "Uhum, ya aiki?."

"Alhamdu lillah, ki gashe da Mummy." Yana gama faÉ—ar ya kashe wayar gabaÉ—aya.

Janan ta ce, "wai kuwa yana da budurwa?.•

Riyya ta ce, "bashi da kowa, Hamma Jazy ya faɗa min bashi da wata budurwa har yanzu. Sai dai wannan aure da Daada take so ta ƙaƙaba masa."

Janan ta kalli Ikram da ta ƙi cewa komai, ta taɓa ta ta ce, "Sis kin yi shiru."

Ikram ta É—an yi murmushi ta ce, "Kawai ina tunanin wacce lucky gal ce zata É—auki Ya Rehaan a matsayin miji."

Riyya ta yi yar dariya ta ce, "gaskiya kam sai dai lucky É—in. Amma kuma ga shi nan zai yi auren, duk da ba ya so amma dai matarsa ce."

Janan ta kalli Ikram ta ce, "Iky ni wallahi na jima ina ji ina ma ya aure ki, tunda Hamma Jazy ya É—auki Riyya, na san shima zai iya auren ki, nikam ina so ya aure ki sosai."

Ikram ta É—an yi murmushi ta ce, "rufa min asiri, ina ni ina shi?."

Ta harare ta ta ce, "ka ji wata magana, Akwai aibu da kin aure sa ne?."

Ta girgiza kai ta ce, "Babu, kawai na san ba abu ne da zai yu ba."

Riyya ta ce, "zai iya yuwa mana, ki ka san me Allah ya rufe?. Mu zamu so ki aure sa É—in, saboda
kowa ya san wacece ke balle azo ana wata magana, ko bakya so?."

Ta kalli Riyya ta ce, "Riyya kenan, Wacce mace ce zata ce bata son Hamma ne? Sai dai in ta san bazata samu ba."

Janan ta ce, "ke kam za ki samu, daman na lura kamar you have stong feelling for him."

Ikramta É—an yi murmushi kawai bata ce komai ba, she wish abinda suka faÉ—a ya zama gaskiya, da sai ta yi azumi guda goma na godiya ga Allah.

      •••••••••

Islaha tana ta shirye shiryen dawowa gida, har an siya mata ticket, har ticket É—in jirgin da zata hau zuwa Adamawa ta siya.

Ranar da zata bar ƙasar tun bayan sallar i'sha ta shirya, da taimakon Sunaira da Maleek ta yi komai yadda ya kamata. A lokacim ta fita zuwa wajan Labiba, dan ta ji ko akwai saƙon da zata kai wa Mama.

Falon gidan babu kowa shiru, Islaha ta É—an zauna tana jira ko za a fito amma ba a fito ba.

A lokacin Aysha ta shigo falon ta ga Islaha a zaune, Islaha ta kalle ta ta ce, "Don Allah ina Labiba?."

Aysha ta ce, "in ki ka shiga ciki, ɗaki na biyu" ta faɗa tana ɗaukar wayarta ta fita. Islaha ta miƙe ta shiga ciki kamar yadda ta ce mata.

Islaha a hankali take takawa a nutse, gidan ya yi mata kyau sosai, tana ta mamakin su haka gidanjensu yake manya ga kyau.

A hankali ta tuea ƙofar ta shiga da sallama tana kiran sunan Labiba.

Gaban ta ya yanke ya faÉ—i, ta yi saurin ja baya, tana jin kamar wata ta ja tasaboda shock É—in da ta ji ya ratsa ta, ta fara zare ido tana so ta tuna abinda ta gani, amma bata so ta gasgata abinda ta gani ba gaskiya ne, ta fi so ta bar shi a hasashe ko mafarki.

Ta jima a haka cikin rashin nutsuwa, kafin ta firgita ta dawo hanlalin ta, ta kalli É—akin sai kuma ta zabura ta bar wajan a guje cikin kuka.

A wannan yanayi ta koma, ta faÉ—a kan gado tan kuka kamar ranta zai fita, ita kanta bata san kukan me take yi ba, kawai dai ta ji tana kuka ne wanda yake zuwa daga zuciyarta.

Abinda ta gani bata taɓa gani ba ko a film balle a zahiri, mace da namiji a tare suna aikata wani abu mara kyau bata taɓa gani ba ko da wasa.

Ganin da ta yi ya saka zuciyarta ta tsinke, jikinta yana rawa, zuciyarta tana rawa, cikin wani irin yanayi mara daɗi wanda bata taɓa jin kanta a ciki ba. Ita dai bata san adadin lokacin da ta ɗauka a wajan ba, sai ji ta yi an buɗe ƙofar an shigo.

Tunda ta shigo ta zuba mata ido kawai tana kallon ta, ganin ta normal da ita kamar ba ita ta gani ita da namiji a É—aki ba.

Labiba ta dake ta ƙarasowa inda take ta ce, "Kin je nemana, lafiya?."

Wani irin abu Islaha ta ji yana taso mata daga cikin kanta yana mamaye duk jikinta, ji take kamar ta tashi ta shaƙe Labiba har sai ta mutu.

Labiba ta ce, "Sai wani kallona ki ke, meye baƙo a abinda ki ka gani ɗin? Kin saba yi fa, ina jin farar fatarsa ce ta ruɗa ki. Amma wannan a wajan ki ai....." Islaha bata san hannunta ya sauka a akan fuskar Labiba ba, sai ganin kanta ta yi a tsaye a kusa da ita tana nuna mata yatsa ta rasa abinda zata ce.

"Kai! Ni ki ka mara?" Ta faɗa tana kai mata mari  amma Islaha ta riƙe hannun, ta sauke hannunta tana jin ƙyanƙyamin Labiba yana shiga zuciyarta.

Kasa ce mata komai ta yi, kawai ta shiga bathroom tana jin fitar Labiba.

Ruwa ta dinga zubawa kanta kamar itace ta aikata, haka ta jiƙe gashinta jagab, a sanyaye ta sake shirya ta fito falon tana zare idanunta. Sama sama suka yi sallama da mutanen gidan, duk ta karɓi lambobinsu dan zasu dinga gaisawa a whatsapp, aka kai ta har airpot.

Ita dai a sanyaye take yin komai, Sunaira ce mai taimaka mata tana nuna mata abinda bata sani ba, a haka har ta gama komai ta yi boarding.

Sai da ta shiga boarding room sannan ta samu ta sha tea, ta yi tagumi tana tuna abinda ta gani da abinda kunnenta ya ji mata.

Gabaɗaya ta ruɗe ta fita daga hankalinta, ita dai ta san tana zaune kawai sai gani ta yi an fara shiga jirgi. Ta miƙe a sanyaye ta shiga itama ta zauna tana kallon window.

Sai ta fara tunanin ko tana da rabon dawowa ƙasar ko babu Allah ne ya sani. Ga shi ta shigo ta fita bata je ta ga ka'aba ba, babban abinda yake yi mata daɗi ta shiga madina har ta kwana biyu. A haka jirgi ya ɗaga zuwa ƙasa nigeria.
Chapter 96 · 0% Book details