← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 133

Sashe 25

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ce, "meye a zuciyar ki ne? Ban yarda da wannan shiru shirun naki ba, duk wanda ya san halin ki in yaga yadda ki ka koma a yanzu ya san kina da damuwa. Meyasa ki ke keɓe kan ki cikin yanayi na damuwa har haka?."

Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, ta sunkuyar da kai ta rasa amsar da zata bashi. Sai wasa take yi da hannunta, ta rasa abinda zata faÉ—a da zata kare kanta a wajensa.

Saheer ya ce, "ina jin ki, faɗa min abinda yake damun ki. Kin san duk girman matsala, duk girman damuwa, zan taimaka miki mu yaƙe ta ni da ke. Dan haka faɗa min damuwar ki, kar ki ji komai, ki faɗa min ko meye zan fahimce ki. Wani abu suka yi miki da bakya so mu sani?."

Islaha ta yi ajiyar zuciya, tana ji gwara kawai ta faɗa masa, gwara ta faɗa masa abinda ya faru ta huta da nauyin da zuciyarta take yi mata. In ta faɗa masa zata ji sauƙi, zata ji sassaucin abun da yake damunta. Amma kuma ya zai ɗauki maganar? A wanne ɓangare zai ajjiye ta? Zai ɗora ta akan ma'aunin fahimta ko zai kalle ta a akasin haka?. Ta ɗago suka haɗa ido, ta buɗe baki a sanyaye zata yi magana......

Nana Haleema.
[6/23, 11:47 AM] KRBBK: RDB2P17
Nana Haleema.

Islaha ta ɗauke kai daga kallon sa, ta ɗan sauke kai ƙasa a sanyaye ta ce, "Hamma babu komai fa" ta faɗa tana ɓoye masa dan bata san a yaya zai fahimci maganar ba.

Ya yi shiru bai amsa ba yana kallon ta, jin shiru sai ta É—ago suka haÉ—a ido, ya É—aga mata gira ya ce, "Ba dani ki ke ba ko?."

"Da kai nake mana Hamma."

A'a, da wani Hamman ki ke ba ni ba, dan kin san ni baza ki faÉ—a min wannan tatsuniyar ba ko?."

Ta shagwaɓe fuska ta ce, "Allah babu komai, kawai ina tuna abinda ya faru a lokacin da bana nan ne."

Ya zuba mata ido ya ce, "faÉ—a min me ya faru?."

"Ina tuna a inda aka ajjiye ni, da baturen da ya sace ni, da yadda ya dinga..." sai ta yi shiru bata ƙarasa ba.

Saheer ya ce, "ya dinga mene? Ina jin ki, ƙarasa."

"Yadda ya dinga sakawa a kawo min abinci, shine abin yake É—aure min kai. Na rasa dalilinsa na sace ni."

"Iya abinda ya dinga yi miki kenan?."

"Eh shikenan."

Ya zuba mata ido yana kallo, dan shi zuciyarsa faÉ—a masa take yi ko dai sun yi raping É—inta ne shiyasa take a sanyaye? Dan yawanci waÉ—anda aka sace da wahala su dawo ba a yi musu wani abu ba, sai waÉ—anda Allah ya kiyaye.

Ya ce, "akwai abinda ki ke ɓoye min wanda bakya so na sani. Amma babu komai, tunda an fito daga tiyatar ki tashi mu tafi wajan ƴan sanda a cigaba da bincike."

Ta kalle sa taga ya haÉ—e rai alamun babu wasa, ta buÉ—e baki zata yi magana, ya dakatar da ita ya ce, "kar ki ce min komai, ki tashi muje kawai, dan ba za a rufe maganar nan ba na faÉ—a miki."

Bata iya musu da Hammanta, ta yi shiru tana turo baki gaba dan ita kam babu abinda zata ce wallahi, sai ranar da ta biyasa kuÉ—in da aro daga nan sai ta san abinda zata yi a akai.

Saheer miƙe tsaye  yana kallon ta ya ce, "tashi muje." Ba yadda ta iya haka ta bi bayansa jikinta a sanyaye.

Yana tsaye ya jingina da bango yana duba file É—in hannunsa, ya É—aga ido ya kalli tv da take nuna masa masu shige da fice a asibitin na ko ina. Ya É—auke ido yana tuna wacce ya gani a zaune lokacin da suna magana tayi daidai da mara kunyar yarinyar nan da ya É—auke, kamar wanda aka bawa umarni ya saka remote ya buÉ—e inda take zaune, ya zuba mata ido yana ya sake tabbatarwa da ita É—in ce.

Ya taɓe baki a bayyane ya ce, "shine mahaifinta" ya faɗa yana sake kallon file ɗin hannunsa, yana kuma karanta sunan Baffa a zahiri.

Ya É—aga kai ya sake kallon ta, a lokacin da Saheer ya zauna kusa da ita, ya É—auke kai ya ajjiye file É—in ya zauna a akan kujera a lokacin kiran Jazy ya shigo wayarsa. Kamar bazai É—auka ba, sai kuma ya É—auka ya saka a speaker ya ajjiye wayar a kusa dashi.

Jazy ya ce, "kai wai me ka mayar dani ne? Ɗan aikin ka ko a ƙarƙashin ka nake aiki kana biyana albashi?. Dan ma ina taimaka maka ina yi maka abubuwa da baka san sai ka dinga raina min wayo, har ni na kira ka ƙi ɗauka sai yanzu da ka ga dama zaka amsa kirana?. Yaronka ne ni ko ɗan aikinka?."

Rehaan ya lumshe ido ya buÉ—e ya ce, "Jazy kana da matsala."

Sai ya sake harzuƙa Jafar ya ce, "ni ne ma kai, in ina da matsala kai meye da kai?. Tun safe nake kiran ka a waya, yanzu na tabbatar azahar ta yi a inda ka ke, amma dan ka raina ni sai yanzu zaka ɗauka?."

Rehaan ya yi shiru bai ce komai ba, Jafar ya ce, "na samu labarin ka sallami yarinyar nan, wallahi ina gargaÉ—in ka akan kar ka sake É—aukar wata yarinya ka kai gidan ka, in ba haka ba wallahi sai na faÉ—awa kowa na gidanku. Tunda kai naga har yanzu baka yi hankali ba, baka san ya kamata ba."

Ya lumshe ido ya buɗe, ya ɗaga ido ya sake kallon screen ɗin daidai lokacin da Saheer ya miƙe tsaye yana riƙo hannunta. Ya jingina da kujera yana kallonsu kamar ya samu wani film a hankali ya ce, "kaine ka haife ni da ka ke yi faɗa min haka? Kar ka manta, na girme ka."

"Ban haife ka ba, amma na isa da kai. In aure ka ke so daman kakar ka ta ce zata yi maka aure ai, wataƙila ma alamomin iskanci ta gani a tare da kai ya saka ta yanke wannan hukuncin a kanka. In ba ɗan iska ba, waye yake ajjiye mace a gidansa? Allah kaɗai ya san me ka yi mata. Banza kawai."

Murmushi ya yi ya shafa fuskarsa yana kallon screen É—in gabansa har lokacin da suka bar wajan, ya É—an yi ajiyar zuciya ya ce, "Ka saka maids É—in Al Hamra su gyara min apartment? Da safe zan shiga Jeddah."

Jazy ya ja tsaki ya ce, "da yake ga É—an aikinka ko? Ni zan saka maids su gyara maka apartment dan zaka je ko?. Kar ka je, don Allah ka zauna indai har sai na yi magana dasu."

Rehaan ya ce, "kashe wayar sai na tura a gyara min, ka cika ni da maganar banza,  gabaɗaya baka da amfani."

"Kai ka sani kuma. Sannan ka faÉ—awa budurwar ka, ta daina zuwa inda nake, wallahi zan saka a kamata. Ni ba É—an iska bane, kai ka san ni ba irin ka bane."

"Ni shine Jazy."

"Har sai ka maimaita? Duk wanda ya kai mace gidansa har ta kwana biyu ai É—an iska ne." Rehaan bai ce komai ba ya yanke wayar, yana ganin kiran Alma yana shigowa ta snapchat amma bai duba ba.

Ya rasa meyasa Alma ta fi tasiri a wajansa in yana England, da zarar ya dawo Nigeria shikenan sai ya dinga mantawa da labarinta. In yana can sai yaji a ransa zai iya aurenta ya zauna da ita.

Ya taɓe baki kafin ya ɗauki waya ya kira wanda zai kira, ya miƙe a hankali ya sauka ya fita daga asibitin gabaɗaya.

Islaha kamar yadda Saheer ya ce wajan Æ´an sandan suka nufa, da ita dashi da Sadik dashi. Tana zaune a bayan mota ta yi shiru, shi kuma shida Sadik suna gaba suna tafiya.

Safeera ce ta kira ta a waya, ta É—auka suka yi magana kafin ta ce, "Hamma Sadik zamu É—auki Safeera a hanya." Ya amsa suka cigaba da tafiya har suka je inda take, ta shiga motar suka nufi police station É—in gabanta yana tsannanta bugawa, dan bata san amsar da zata bayar wacce zata gamsar da Hamma ba.

A can suka samu Ummi da danginta, aka zauna ana tattauanwa akan batun case É—in sace ta.

Islaha ta ce, "babu hannun Ummi a sace É—in da aka yi."

Dpo ya kalli Ummi ya ce, "Wannan case É—in dai na yanzu, kin bar cikinsa. Amma kina cikin duk wanda zai iya afkuwa nan gaba, dan ko ciwon kai Islaha ta yi zamu nemo ki."

Saherr ya ce, "ni ban gamsu da wannan maganar ba, ina so a yi mata tsakani da Islaha, ko ciwon kai Islaha tayi wallahi sai na É—aure Ummi. Domin ta furta kalmar sai ta ga bayanta a gaban shaida, kuma ta amsa da bakinta ta ce ta san ta aikata."

Dpo ya ce, "ba ina nufin rufe case É—in Ummi ba, ina magana akan case É—in sace Islaha babu hannunta a ciki. Tunda ga Islaha a zaune ta tabbatar mana da Ummi bata da hannu a ciki."

Ya kalli mahaifin Ummu ya ce, "Alhaji wannan case ɗin babu ita a ciki, amma kamar yadda Saheer ya faɗa ko cuwon kai Islaha tayi da saka hannun Ummu a ciki. Domin kalmar da ta faɗa ba ƙaramar kalma bace, tun kwanaki na faɗa maka wannan kalmar zata iya sakawa a ɗaure ta a gidan yari, ita ake kira da baki shi ke yanka wuya."

Mahaifinta ya ce, "na sani, na kuma san duk abinda ka faÉ—a gaskiya. Na gode da karamcin ka sosai."

Dpo ya ce, "yanzu hukuma ta shiga tsakanin wannan kalma da Ummi ta faɗa, muna tsakiya akan kalaminta, dan haka ko yaushe in wani abu ya samu Islaha za a wayi gari Ummi tana wajan nan mun riƙe ta."

Ummi tace, "wallahi bazan sake aikata komai ba, bazan yi mata komai ba."

"Hajiya Ummi wannan daga baya ne, kin É—aure kan ki da kalaman ki. A yanzu dai babu ke a case É—in, amma nan gaba zaki iya shigowa. Alhaji zaku iya tafiya.." Godiya ya yi musu sannan suka yi sallama suka fita.
Chapter 25 · 0% Book details