← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 133

Sashe 121

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aka zuba mata ruwa ta farfaɗo, ta gigice ta miƙe ta yi wajensa tana girgiza shi, ganin da gaske ya mutu sai ta sake suma. Sai da ta suma sau huɗu tana farfaɗowa, kafin ta koma kamar mahaukaciya, ko magana bata iya yi, saboda alfarmar Sudaisa sirikin black ne aka binne shi da kayana jikinsa ba a cillar dashi ba.

Sudaisa ta zamarwa Saheer kaya, ko yauahe tana kusa dashi bata iya magana, bata cin abinci bata shan ruwa sai kallo kawai. Har lokacin Black bai dawo ba, kuma Arɗo ya ƙyale ta akan nufinsa. Shi kansa Saheer ya ji mutuwar Sudais, ya yi kuka sosai, yana tuna amanar da ya bar masa.

Har washe gari Sudaisa tana cikin wanann yanayin, ana bawa Saheer damar rarrashinta amma ta ƙi ko magana bata yi. Saheer ya yi iya yinsa amma ya kasa taimaka mata, dole ya haƙura yana yi mata addu'a.

A ranar suka yiwa kowa duka, sannan suka ɗauki  video suka turawa ƴan uwan kowa dan su ga halin da suke ciki.

•••••••

Sadik da Baffa suna zaune suna tattaunawa akan kuɗin fansar Saheer, suna ƙoƙarin nemo mafita akan abinda yake damunsu. A lokacin Mama da Hanan suka shigo har Islaha.

Kamar jira ake yi su ahigo sai ga kiran waya ya shigo wayar Baffa. Baffa ya kalli wayar gabansa ya faÉ—i, ya kalli Sadik ya ce, "sune fa."

Kowa sai da ƙrijinsa ya buga saboda ba a san da abinda suka zo ba, Baffa ya ɗauka ya saka a amsa kuwa ya ce, "Assalamu alaikum."

"Wa'alaiki salam. Yauwa na ce Æ´an uwan Saheer ne ko?."

Baffa ya ce, "su ne."

"Mun turo mu ku video, ku buÉ—e" ya faÉ—a yana kashe wayar.

Sadik ya kunna wayarsa sai ya ga shi nan suka tura video, ya kunna musu suka ga yadda ake dukan Saheer da bulalai ga hannunsa a É—aure. Suka dinga kuka, hankalin kowa ya sake tashi.

A lokacin suka sake kiran wayar, Baffa ya É—auka ya ji sun ce, "Mun ga kamar bakwa son É—an ku, in bakwa sonsa sai mu kashe sa."

"Muna sonsa, kuÉ—in ne suka yi yawa."

"Daman mun faÉ—a mu ku yau za mu kira mu faÉ—a mu ku inda za ku kai mana kuÉ—i, an gama haÉ—a kyÉ—in?."

Baffa a sanyaye ya ce, "Ba a haÉ—a ba, kamar yadda muka yi magana da ku bamu da halin waÉ—anan kuÉ—in da ku ka ambata. Mun nemi inda za mu samu kuÉ—in mun rasa, har gidan da mu ka ciki mun saka a kasuwa amma har yanzu ba a tayawa."

"Bakwa son ganin yaron ku kenan?."

"Muna so, amma muna neman alfarmar a rage mana kuÉ—in, baza mu iya biya ba."

"Mun rage miliyan ashirin, za ku ba da miliyan tamanin ranar alhamis. Kun amsa za ku kawo ko mu kashe shi?."

Baffa ya ce, "wallahi su ma ba mu da hanyar su."

"To ai shikenan, za mu kashe shi mu ƙona gawarsa...." Sai ya dakata ya ce, "ku zo min dashi."

Baffa ya ce, "ku yi haƙuri, kar ku kashe shi don Allah."

"naga kun É—auki abin wasa ne ai, bara ku ji daga bakinsa. Kai zo ka yi magana da yan gidan ku, ka faÉ—a musu mutane nawa mu ka kashe a gaban idanuna."

Saheer saboda wahala da tashin hankalin da yake gani, da damuwa rauni da yunwa, ruɗewar mutuwar Sudais, tashin hankali da damuwar da ƙanwar Sudais ta shiga, cikim gajiya da sanyin jiki ya ce, "Baffa na san ba ku da hanyar wannan kuɗin da suka faɗa, na san babu inda za a same su. Kar ku tayar da hankalin ku, kawai ku bari su kashe ni ɗin daman lokacina ne....." dakata ya yi da magana saboda bindigar da suka buga masa a kai. Saheer ya yi ƙara wacce ta ratsa kunnensu gabaɗaya.

Arɗo ya ce, "Mu za ka yiwa wannan maganar? Sai mu karɓi kuɗin kuma mu kashe ka, kuma mun kaahe banza da wofi."

ArÉ—o ya ce, "Ba ku ga irin dukan da mu ka yi masa ba ko?."

Baffa murya tana rawa ya ce, "Mun gani."

"Kuma har yanzu ku kasa haÉ—a miliyan tamanin?."

"Ba mu da ina zamu samu."

Arɗo ya ce, "Shikenan, mun dawo hamsin, daga nan ba za mu sake rage mu ku komai ba. Za ku kawo kuɗin ko mu kashe sa, baza mu ƙara mu ki lokaci ba, in dai ba a kawo kuɗin nan ba zamu kashe shi. Ba mu ɗauko shi dan mu dinga ciyar dashi a banza ba, da kun ba da kuɗi da yanzu ya dawo.”

Baffa zai yi magana Islaha ta firgita ta fizge wayar daga hannunsa, jikinta yana rawa, muryarta tana rawa, hannunta yana karkarwa ta ce, "Kar ku kashe sa, za mu kawo mu ku in sha Allah. Kar ku kashe Hamma, ku ƙyalesa zan nemo kuɗin na kawo."

Ya yi dariya ya ce, "Yauwa Yarinya, ke kaÉ—ai ki ke son É—an uwan nan na ki. Za mu sake kiran ku." Ya faÉ—a yana yanke wayar.

Islaha ta cillar da wayar, jikinta yana rawa kamar wacce aka jonawa wutar lantarki, ta rasa inda zata saka kanta, ta rasa me zata yi ta ji daÉ—i, sai kai kawo take tana tunanin mafita.

Muryar ta tana sarƙewa, numfashin ta yana barazanar barin jikinta, yana sarƙe mata maganar da take kan harshenta.

Ta kalli Baffa a wannan yanayi ta ce, "Baffa zan nemo kuɗin, zan yi komai saboda Hamma, zan je na nemo miliyan hamsin a duk inda take a kai  musu, in dai za su saki Hamma, zan nemo."

Baffa ya riƙe kafaɗunta ya ce, "ba ki da hanyar Islaha, ba naira dubu hamsin aka ce ba, ba dubu ɗari biyar aka ce ba, ba miliyan biyar aka ce ba, miliyin hamsin suka ce. Miliyan ɗay ɗay sau hamsin. Islaha ba ki da hanyar da za ki samu waɗanan kuɗin, ki karɓi ƙaddara ki cigaba da yi masa addu'a, in yana da sauran kwana a duniya Allah ya kuɓutar dashi, in kuma babu Allah ya sa ƙarshen wahalarsa kenan."

"Bazan iya ba Baffa, zan nemo kuɗi ne a ko ina suke, na yarda zan yi ko meye indai zan samu kuɗin. Bazan iya bari rayuwar Hamma ta salwanta ba, bazan iya zuba ido Hamma yana cikin wani hali na ƙyalesa ba, bazan iya ganin Hamma yana neman taimako na ɗauke kaina ba......"

Ta girgiza kai tana ja da baya tana kallonsu tana hawaye duk a lokaci É—aya ta ce, "Zan nemo miliyan hamsin, ko raina ne zan bayar indai shi zai dawo" ta faÉ—a tana fita daga falon da sauri.

Baffa ya kalli Sadik ya ce, "Sadik ka bi bayana don Allah, kar bari ta je ko ina, ka dawo da ita."

Da sauri ya bi bayanta ya samu zata fita daga gidan, ya yi sauri ya cimma ya ce, "ina za ki je?."

Muryarta tana rawa tana kuka mai tsanani ta ce, "zan je na samo kuÉ—in ne."

"A ina za ki samu? Ba ki da hanyar da za ki samu wannan kuÉ—in."

Sai ta sake fashe masa da sabon kuka ta ce, "haka zan bar Hamma kenan a kashe sa a banza? Haka zan bari Hamma yana neman taimako na ƙyalesa? Haka zan bari suna dukan Hamma na kasa yin komai?. Meye amfanina a duniya in ban sadaukar da farin cikina akansa ba, meye amfanina a duniya in ban fito da Hamma daga cikin halin da yake ciki ba?. Ni bazan iya ƙyale Hamma a wanann yanayin ba, babu amfanin zamana a duniya bayan na kasa taimaka masa, wallahi bazan iya ba" ta faɗa tana rufe fuskar ta da hannunta, ta durƙushe a wajen tana kuka sosai.

Sadik ya ce, "haƙuri za ki yi, babu abinda za ki iya a kan hakan."

Bata ce komai ba sai kuka, sai da ta ga ji sannan ta miƙe zunbur ta kalle shi ta ce, "ina da mafita, ban sani ba ko za ka bani goyan baya akan abinda zan faɗa maka."

Ya kalle ta ya ce, "in dai hanyar bata saɓawa Allah ba ce zan amince, ina jin ki."

Ta ja numfashi mai tsaho ta sauke shi a hankali, ta rufe ido tana tunanin yadda zai É—auki maganar, ta buÉ—e iso ta ce, "Ahlin gidan AbdulAziz Yola suna da kuÉ—in da za su bani miliyan hamsin?."

Ya É—an kalle ta cikin mamaki abinda ta ce ya ce, "su za ki je su ba ki kuÉ—in?."

Ta girgiza kai ta ce, “ka amsa min Hamma Sadik."

Ya ce, "Suna dashi mana, meye miliyan hamsin a wajansu?."

Ta yi shiru na wani lokacin, ta rufe ido ta buɗe tana furzar da iska. Ta kasa magana, ita kanta bata son furta abinda zata ce, amma kuma ya zamar mata dole ta yi, dan ita kaɗai ce hanyar da zata bi dan karɓo Hamma, akan Hamma zata iya ba da ranta.

Ta sake rufe ido ta buɗe, ta kalle shi ta ce, "Ai daman na faɗa mu ku batun aurena da suka zo nema, kuma shi wanda za a aura min ɗin da kansa ya kawo maganar auren contract na wata biyar…..”

Ta dakata tana ji zuciyarta tana bugawa, ta ja numfashi da ƙarfi ta ce, “Zan karɓi auren contract ɗin da ya yi min tayi, zai aureni saboda mahaifinsa, ni kuma zan auresa inda zai bani kuɗin fansar Hamma!."

Sadik ya bita da kallo ganin kamar bata cikin hankalinta ne ya saka ta ke wannan maganar. Ya tausasa murya ya ce, "ki É—an samu waje ki zauna Islaha, kamar ba nutse ki ke ba."

Ta ce, "a nutse nake, ina faɗa ma ka ne kar na je na yi a bayan idonka daga baya kai da Hamma ku dinga ganin laifina har ku dinga zargina da mummunan abu, shiyasa na sanar da kai abinda zan yi. Ba wai shawara nake nema ba, na faɗa maka ne dan ka sani, na riga na gama yanke hukunci a zuciyara. Zan amince na yi auren, shi kuma ya bani kuɗin da za a karɓo Hamma. Bayan wata biyar in muka rabu, sai na dawo na auri Hamma."
Chapter 121 · 0% Book details