← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 133

Sashe 62

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuwa farin cikin fara samun kuÉ—i ya mamaye mata zuciya, ta fara converting saudi riyal to naira tana lissafa riyal dubu bakwai.

Ƙaramar ƙara ta yi ganin kuɗin da ya bata a kuɗin nigeria, daɗi ya mamaye mata zuciya tana ji kamar ta taka rawa.

Ta rufe baki da hannunta ta ce, "anya ya san kuÉ—in da ya bani? Ya san dubu bakwai ce kuwa?."

Ta yi dariya ta ce, "ni da zai karɓa ma dana bashi wallahi, da na fara rage masa bashinsa da na ci, a hankali sai na ƙarasa bashi."

A wannan yanayin ta yi abinda ya ce É—in, ba tayi kuskure ba saboda murna. Lokacin da ta fito aiki yake a laptop, sai yatsine fuska yake yi shi a lallai ya gaji.

Islaha ji take kamar ta tsinka masa mari, dan bata son ta ga namiji mai saurin nuna gajiyarsa akan komai kamar sa. A ganinta mata ne ya kamata su nuna sun gaji ba namiji ba, maza jarumai ne, kuma da juriya aka san su.

Ta ajjiye masa a kusa dashi, bai motsa ba kamar bai gan ta ajjiye ba, ita kuma bata ce komai ba ta juya a hankali ta fita daga falon.

Tana fita ya kira Jazy yana ɗauka ya ce, "Jafar wata housemaid Ubaid ya aiko min, kamar mai taɓin hankali fa, sai ka ga tana magana ita kaɗai."

Jafar ya yi dariya ya ce, "ina ruwan ka da maganar ta, kai dai ba tana yi maka abinda ka ke so ba? Shugaban masu son jiki da shagwaɓa na africa."

Rehaan ya ce, "uhum ba laifi, tana da ɗan ƙoƙari."

"Shikenan sai ka haƙura. Zuwa next week zan shigo in sha Allah."

"Zaka shiga Yola before ka zo nan?."

"i think so."

"Okay, in ka shiga ka taho da Kiddo, na yi mata alƙawarin zuwa amma bana so ta zauna ita kaɗai."

"Ga housemaid É—in ka nan, ba sai su zauna tare ba?."

Kamar Jafar yana ganinsa ya wani ya wara ido ya ce, "god forbid, ta ya zan bar kiddo da wannan yarinyar mai taɓin hankali? Infact ni fa manage nake yi, in na tuna abinda suke aikatawa da Ubaid sai na ji kamar bazan iya cin abincinta ba."

"Rehaan ka shiga uku, kai a ina ka ga suna aikata wani abun? Ka kiyaye harshen ka fa, kar wata ran ka yi danasani mara amfani."

Rehaan ya ce, "babu yadda za a yi Ubaid ya ajjiye housemaid Æ´ar Nigeria irin wannan bai yi mata komai ba, na san waye Ubaid. So zan iya rantse maka itana irinsa ce, dan da kuÉ—i yake siye matan Nigeria, duk abinda yake so suna yi. So bazan iya barin ta tare da Kiddo ba."

Jazy ya ce, "rayuwarta ce, babu abinda ya shafe ka da abinda take aikatawa. Ka iya harshen ka akan irin wannan maganar, in ma tana yi É—in ina ruwan ka? Babu ruwanka da abinda take yi, ita ta ga zata iya."

Ray lokaci ɗaya ya ji ransa ya ɓaci, loaded fries ɗin maya ji bazai iya ci ba.

Ya ture sa daga gabansa ya ce, "na tsani É—auko mata daga Nigeria a kawo nan suna wannan shirmen, bana so Jazy, kuma yana jin haushin hakan sosai."

"Ka ji mai kishin ƙasa. Kai fa ba ɗan nigeria bane, haifaffen ƙasar Uk ne ne kai, Mamy haifaffaiyar ƙasar india ce. So meye na damuwa akan ƙasar da ƙafar ka ɗaya ce a ciki?."

"I was born in England, but I'm Nigerian by blood...... Jini ba wasa bane malam, na fi ka kishin ƙasar tanka" ya faɗa da hausa saɓanin da da yake magana da turanci.

Jazy ya yi dariya ya ce, "An gaishe da mai kishin ƙasa. Ka fara gyara ƙasar taka tukunna, ka mayar da hankali ka samarwa da kowa aikin da zai ishesa ya riƙe kansa iyalansa. In ka yi haka ka tabbatar kowa ya samu, sai ka ji haushi in sun je wata ƙasar nema."

"Ni ba shugaban ƙasa bane."

"Dan haka sai ka yi kamar baka gani ba, tunda ka san baza ka iya canjawa ba meyasa zaka damu kan ka?. Wallahi basu da laifi, in basu bar ƙasar su sun nema ba mutuwa ka ke so su yi ne Ray? Kai ka san yadda ake cikin talauci a Nigeria kuwa?."

Ray ya yi masa banza bai tanka ba, Jazy ya ce, "ya maganar auren ka? Ance an kusa ko?." Jin yana yi masa dariya sai ya kashe wayar.

Ya bi bowl ɗin da kallo, haka kawai ƙyanƙyaminta ya mamaye masa zuciya, ya ɗauka ya kai dusbin ya zubar ya haɗa har bowl ɗin, ya hau sama yana jin haushin kasancewar ta a gidan Ubaid kamar wata ƙanwarsa.

Islaha lokacin da ta koma tana shiga kiran Hajiya Shafa ya shigo. Ta zauna a gefen gado ta É—auka ta ji Umma ta yi sallama.

Islaha ta amsa ta ce, "Umma ina yini, Islaha ce. Ina ta kiran wayar ki bana samu."

Umma ta ce, "Lafiya lau Islaha. Da yake ban siyi layin ƙasar nan ba."

"Ai ya kamata ki siya Umma saboda kiran gida."

"Ina samu ina kiran su ta whatsapp in na samu hutu. Ƙawarki ce dai har yanzu taƙi bani dama na yi magana da ita."

Islaha ta ce, "Kuma tana tambayata ina ki ke, sai na ce mata ai ba tare muke ba."

"Don Allah ki ce mata ko sau ɗaya ta karɓa mu gaisa, ina so na ji muryarta."

Islaha ta É—aga kai ta ce, "To Umma, zan faÉ—a mata in sha Allah. A wacce unguwa ki ke a madinan?."

Umma ta cr, "wallahi ban sani ba, ban taɓa fita ba tunda na zo, aiki ne nake yinsa kamar inji."

Islaha ta ce, "To Umma ki tambayi mai wayar sai ta faÉ—a miki sunan Unguwar, ina so na zo na ganki."

A sanyaye Umma ta tambayi Hajiya Shafa, ta faÉ—a mata itama ta faÉ—awa Islaha.

Islaha ta ce, "In Allah ya yarda zan zo na ganki, duk da nima bana fita amma zan san yadda zan yi na zo."

Umma ta ce, "to Islaha, amma ki cewa ƙawar ki ta daure ta yi magana dani kin ji?." Islaha ta amsa sannan suka kashe wayar.

Bayan sun gama wayar Hajiya Shafa ta bi Umma da kallo ta ce, "ya naga kin rame haka?."

Umma ta ce, "kullum a cikin fargaba nake kwana a gidan nan, kwana biyu hankalina ya kwanta saboda mai gidan baya nan, amma yanzu gabaÉ—aya a ruÉ—e nake saboda ya dawo yau."

Hajiya Shafa ta yi tsaki ta ce, "ke baki san yadda za ki kare kan ki daga wajan ba? In baki kame kan ki ba, kin nuna masa ke ba irinsa nace wallahi bazai ƙyale ki ba wallahi."

Umma ta ce, "to ya zan yi?."

"Sai ki san abinda zaki yi. Kuma ki tashi na raka ki kije ki yi layin waya saboda Æ´an uwan ki, bazai yu na dinga zarwa a kan ki saboda waya ba."

Umma ta ce, "ai bani da kuÉ—i."

"Mu je na ranta miki, in aka baki albashin ki sai ki biya ni." Babu yadda Umma ta iya haka ta tashi suka fita.

Tunda ta zo sai ranar ta fita, Umma sa kallon unguwar take yi cikin burgewa, ko ina shiru sai larabawa kaÉ—an-kaÉ—an kafin ta ce, "Hajiya a ina masallacin annabi yake?."

Ta kalli Umma ta ce, "da tafiya, sai kin hau mota."

Umma ta ce, "Allah ya bani iko wata ran na je na gano kabarin Annabi."

"Kina saka ran zaki je kenan?."

"Eh mana Hajiya, na zo har garin ace ban je ba, ai na yi asara babba."

"Ai ba ziyara ce ta kawo ki ba, aiki ne ya kawo ki."

"Duka biyun ne suka kawo ni wallahi."

"Ki cire ran zuwa wallahi, dan fitowa daga gidan nan ma babu lallai ki sake yi."

Umma ta yi shiru tana tunani, kenan burinta na zuwa masallacin bazai cika ba, gata a Madina amma ace kar ta saka ran zuwa ta yi ziyara? To meye amfanin zuwan ta ƙasar in bata je ta ga masallacin ba? Ita da buri biyu tazo ƙasar, ta tara kuɗi kuma ta yi ziyara, gashi duka biyun basu yu ba. Bata ce komai ba suka je aka yi mata layin waya suka dawo gida ita kuma ta wuce.

Umma jin gidan shiru sai ta kwanta da niyar hutawa, bacci yana É—auke ta ta ji ana tashin ta, ta buÉ—e ta ga matar gidan a tsaye tana yi mata nuni da tashi.

Umma ta miƙe tsaye ta biyo bayanta zuwa kichen. Abinda ta gani ya saka gabanta ya faɗi, kaji ne masu yawa sosai, ta nuna mata alamun ta gyara.

Umma ta ji kamar ta kurma ihu saboda takaici, ta bi kajin da kallo dan a ƙalla zasu kai hamsin. Matar ta ware wanda in aka gyara za a saka a fridge, da wanda Umma zata gasa.

Umma ta ƙarasa ta fara gyarawa, tana yi tana hawaye saboda gajiya. Tana tsaka da yi aka ce ta zo ta gyara waje an ɓata. Ta fito ta gyara ta koma ta cigaba da aikin.

Aikin sai da ya ɗauke ta awa biyu da wani, ta gaji matuƙa, bayanta kamar zai ɓalle saboda gajiya mai tarin yawa. Daƙyar ta ke jan ƙafa ta shiga ɗaki, ta cire kaya ta shiga wanka dan khamshin gashin kaza kawai take yi. Tana fitowa daga wanka ta ji an rufe ƙofa, tana juyowa ta ga mutuminta a tsaye yana kallon ta.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Umma ta faÉ—a hawaye cikin tashin hankali.

Ya fara takowa zuwa inda take a hankali, Umma ta fara ja baya tana kalle kalle tana so ta samu wani abun da zai zamar mata makami.

Babu komai a wajan sai ta É—auki wayar ta tana muna masa, cikin turancinsu na manya ta ce, "Police, zan kira Police zu zo su kama ka wallahi, kar ka matso kusa dani." Jin ta ambaci police sai ya tsaya, kafin ya juya ya fita daga É—akin.

Umma ta zube a kan gado kwai ta fashe sa kukan takaici da sanasani. Whatsapp call É—in Atika ne ya shigo, tana É—auka kawai ta fashe da kuka.

Atika daga can ɓangaren ta ce, "Maimuna me ya faru ki ke kuka?."
Chapter 62 · 0% Book details