← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 133

Sashe 48

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A falo suka haɗu da Sunaira ta yi mata murmushi, Islaha ta ɗan yi yaƙe sannan ta wuce ɗakin ta tsaya tana kallon closet ɗinsa.

Ta taɓe baki ta buɗe ta saka kayan ta fito dan ta gaji da wannan azabar, daga girki sai shara da wanki. Ta manta rabon da ta yi wanki, tunda ta baro gidan marayu Hamma ya shagwaɓata, wanki indai ba na undies ba bata yi. Shi yake biya a wanke a goge mata, a kawo mata ta ajjiye sai dai ta saka kawai. Amma daga zuwan ta ta fara yiwa wani ƙato wanki, ga kayan duk sun yi dauɗa kamar ƙaramin yaro.

Ganin Sunaira a zaune ya saka itama ta zauna, sai kuma ta tashi ta haÉ—a tea ta sha ta É—auki wayarta tana duba messgaes.

Gabanta ya faÉ—i ganin messages É—in Saheer har guda biyar sun shigo a jere.

Ta zubawa saƙon ido amma ta kasa buɗewa balle ta ga abinda ya ce, ta kalli ƙasan sunansa ta ga saƙonn Adda, sai na Maman su Safeera, sannan na Safeera harda Saleem da Sadik.

Na safeera ta fara buɗewa ta ga vn ne na sakan talatin, ta buɗe ta ji Safeera ta ce, "Islaha ya ki ke, ina ta kiran wayar ki kiran baya zuwa. Ina fatan komai lafiya lau. Hamma ya san kin tafi, ransa ya ɓaci sosai. Ban taɓa jin rauni a muryarsa kamar yadda naji ba, yace min baki kyauta masa ba, kin karya masa zuciya."

Islaha ta sauke numfashi cikin damuwa, ta lumshe ido tana tuna tazarar da take tsakaninta da Hamma, ta san yana can ransa a ɓace, gashi bata nan bata san lokacin da zata koma ba balle ta bashi haƙuri.

Ta buɗe ido ta kira Safeera ta audio call amma baya yi, ta kalli Sunaira ta ga tana waya, sai kuma ta tuna itafa ƴar ƙasar ce.

Sunaira tana kashe wayar, sai Islaha ta shiga google ta yi english to arabaic ta miƙawa Sunaira dan ta karanta. Sunaira ta karɓa ta karanta sannan ta yi murmushi, ta yiwa Islaha downloading botim, ta koma google ta yi mata rubutu ta sake bata.

Islaha ta kalla ta ga ta ce, "Ki faÉ—awa wanda zaku yi waya, ya É—auko botim ya buÉ—e sai ku yi waya."

Islaha ta gyaɗa, ta yiwa Safeera voicenote ta faɗa mata, ba jimawa sai ga message ɗin Safeera tace mata ta buɗe.  Islaha ta shiga app ɗin ta kira Safeera, sai gashi tana ringing har Safeera ta ɗauka.

"Islaha ya ki ke?."

Isalaha jin muryar Safeera ya saka ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Safeera har yanzu baki da lafiya? Muryar ki bata yi daidai ba."

"Gani nan dai kawai, ko aiki ban je ba. Ina fatan komai normal ko?."

"Eh to kusan hakan. Gidan da nake babban gida ne sosai, kuma mai gidan balarabe ne. Allah ya taimake ni akwai wata balarabiya itama tana aikin, tana da kirki sosai, itace take É—an nuna min wasu abubuwa. Sai dai aikin na su babu hutu, komai kai zaka yi musu. Abin takaicin ma wai har wanki."

"To ya za a yi, Allah ya taimaka."

"Amin. Hamma ya yi miki waya ko?."

"Sadik ne ya fara zuwa, sannan ya kira Saheer ɗin, ransa ya ɓaci sosai, bai ji daɗi ba. Ya ce min ƙawata ta yi abinda bai yi zato ba, ƙawata ta karya masa zuciya. Gaskiya bai ji daɗi ba, a muryarsa kaɗai zaka fahimci ya ji ciwo sosai."

"Na san hakan zai faru, na ga messages É—insa bazan iya buÉ—ewa ba, dan ban san me zan ce masa."

"Saleem da Sadik ma ransu ya ɓaci sosai. Sadik yana ta masifa, shi wai wallahi bai yarda dake ba. Shi kamar zargin ki yake yi, wai komai ke ki ka shirya."

"Shi tun farkon abin nan abai yarda dani ba, gani yake kamar kaina na bayar aka bani kuÉ—in aikin Baffa. Bai san ina da hankali ba, kawai sai na lalata rayuwata?."

"wallahi É—azu ma ya faÉ—a, yana ta cewa wai kin bayar an baki, Sai da Saheer ya taka masa burki akan hakan."

"Hmmm na fisu tsanar aikin nan wallahi."

"Ki samu ku yi magana da Hamma ko zai ji daÉ—i, dan gaskiya bai ji daÉ—in wannan hukuncin nan naki ba."

"Sai ya huce, yanzu in na kira shi bazai fahimce ni ba, sai zuwa jibi sannan zan kira sa, yanzu yana dokin fushi bazai ji me zan ce masa ba."

Safeera bata ce komai ba, Islaha ta ce, "baki ce min ina Umma ba, ko kun yi waya?."

Safeera ta ce, "hmm to me zan ce? Abinda yake so ne fa Islaha, dan ta tafi neman kuÉ—inta ni neman ta É—in me zan yi kuma?."

"Duk da haka Bestie, Uwa ce fa, ko babu komai zaki so ki ji ya ta sauka ko?."

"tafiya ta yi ta bar mu, ta zaɓi yiwa larabawa bauta akan gidan auren ta. Yau ko aiki ban je ba, ina gida ban san waye zai dinga kula da gidan in bana nan ba. Ina tunanin ma aikin kawai zan ajjiye saboda dafawa Baba abinci. Kin ga tafiyar ita ta yiwa kyau, tambayar ta ɗin me zan yi."

"Umma tana Madina, ni ina jeddah ni da Labiba. Amma zan kira ta in sha Allah."

Safeera ta ce, "Bestie zamu yi magana anjima" ta faÉ—a tana yanke wayar, Islaha ta bi wayar da kallo tana sauke numfashi tana kallon message É—in Hmmanta amma ta kasa buÉ—ewa.

••••••••

Yana zaune yana kallon screen É—in laptop É—insa, murmushi yake yi yana kallon kyakykyawar budurwa wacce kallo É—aya zaka yi mata ka san bahaushiya bace.

Kana ganinta ka san bata jin hausa ko fulatanci, dan ko kaɗan bata yi kama da ruwa biyu ba, ita ruwa ɗaya ce. Ta saki gashinta har baya tana ta dariya tana kallon Rehaan. Fatima kenan, ƴar autar su Mamy kuma age mate ɗin Rehaan. Sun saba da Rehaan sosai, ya kan ɓata awa ɗaya suna hira da Fatima, ta zama kamar ƙawarsa, baya kallon ta a matsayin ƙanwar Mamy.

Ya ɗan taɓe baki yana kallon ta ya  ce, "ni babu wani aure da zan yi."

Ta yi dariya ta ce, "Mamy ta faÉ—a min auren ka ya kusa, shine na ce yaron nan ashe aure zai yi babu labari."

Ya yi murmushi ya ce, "sai ki aurar dani. Baki tafi aiki ba?."

"Sai anjima kaÉ—an zan tafi."

"Okay byee" ya faÉ—a yana niyar katse kiran.

Ta yi dariya ta ce, "Mr Busy, za a tafi aikin ne?." Bai bata amsa ba, sai ta ce, "ka gaishe da matar ka."

Ya harare ta ya ce, "you are not serious" ya faÉ—a yana kashe laptop É—in yana jingina da kujera idonsa a rufe.

Tashi ya yi ya buɗe ido, ya miƙe zaune yana kallon wani wajen daban dan bai sam me zai yi na kwata-kwata. A yadda yake zaunen nan kamata ya yi ace yana shan tea ko coffee, dole ya samo housemaid ko dan haka. Ranar da ya yi nufin kiran Maleek a waya fasawa ya yi, amma a yanzu yana jin zai yi ko dan taimakon kansa.

Kiran Jazy ne ya shigowar wayarsa, yana É—auka Jazy ya ce, "Mr Man how far?."

"Fine. Ya ka ke?."

"Yau hausa ka ke ji da ita kenan, lafiya lau. Ka yi magana da Maleek É—in?."

Ya É—an sauke numfashi sannan ya ce, "ban yi ba, bana so a kawo min wacce bazan iya cin abincinta ba."

"Kai ma ka san duk housemaids ɗin ƙasar nan they are very neat wallahi, ba su da ƙazanta ko kaɗan."

"Ni yaushe zaka zo?."

"zan zo, amma ba yanzu ba."

"ka hanzarta ka zo, akwai lissafin da zaka ta ya ni mu yi."

"Alright. Amma kafin nan ka fara magana da Maleek ko Ubaid a baka housemaid É—aya, na san halin ka, kafi son komai a yi maka ba wani abincin kirki ka ke ci yanzu ba. Ni kuma Mamy ta bani amanar ka, shiyasa na damu."

Ya É—an murmusa kaÉ—an ya ce, "ka raina ni, wai an baka amanata, kana mantawa ni yayan Riyya ne ko?."

Jafar ya ce, "Tunda ba kai ka haife ta ba ai shikenan. Sai wani lallaɓa ka nake yi kamar cikina abincin zai je. Rehaan kar ka yi magana dasu, nan ba Yola bane balle kace Mamy zata dafa maka."

Ya ɗan taɓe baki ya ce, "zan yi waya Shams ya kawo min chef daga can."

"Har sai an kawo maka chef daga nigeria? Dan dai kawai kana da kuÉ—in biya ko?."

"Ya ka ke so na yi ne?."

"yadda ka ke so Rehaan."

Rehaan ya kashe wayar, ya miƙe ta fita daga falon kai tsaye ya nufi gidan Maleek da niyar tambayarsa ya bashi housemaid face to face....

Nana Haleema
[7/2, 10:42 AM] KRBBK: RDB2P34
Nana Haleema.

Labiba tunda suka tashi da safe suke aiki, duk ta jigata amma haka ta daure suna yi tana sauke numfashin wahala. Aisha ta kalle ta ta ce, "Duk kin gaji, kamar kin yi wani aiki mai yawa."

"A haka babu yawa aikin?."

"Na ki wasa ne. zan je na zubar da sharar nan a waje, ina zuwa." Labiba ta É—aga mata kai ita kuma ta fita. Labiba ta zuba abinci ta fara ci, kanta har sarawa yake yi saboda gajiya ga yunwa.

Hannu ta ji a sako ta bayanta an riƙo ƙugunta, ta firgita sosai ta juyo suka haɗa ido da Ubaid yana binta da wani shegen kallon kamar zai cinye ta.

Duk da ba yau namiji ya fara yi mata haka ba, amma gamin Ubaid sai ta diririce ta ta rasa abinda zata yi, ya ja ta a hankali zuwa jikinsa, yana shaƙar ƙhamshin humar da ta shafa a wuyanta.

Labiba jikinta ya fara rawa, ta É—an daure bata nuna ba, tana jin yadda yake yawo da hancinsa a wuyanta yana sake haÉ—a bayanta da jikinsa.

A hankali ya kai hannunsa wuyanta yana shafawa a hankali kafin ya ce, "Labiba." Yadda ya faÉ—i sunan ya burge ta, dan yadda ya faÉ—a É—in ya yi mata daÉ—i har bata san ta lumshe ido ba.

Ya yi mata kiss a wuyanta sannan ya ce, "meet me in my room, now" yana faÉ—a ya sake ta ya juya ya fita.
Chapter 48 · 0% Book details