← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 133

Sashe 86

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga can ɓangaren yana kashe wayar ya nufi wajan Baffa, da ya shiga falon Baffa ba ya nan sai Mama kaɗai a tsaye. Tunda ya shiga yake binsa da kallo, ganin sabuwar farar shadda ya saka sai ɗaukar ido take yi, kai da ka gansa ka ga ango ko wanda yake shirin angwancewa, bai taɓa yi mata kyau kamar ranar ba, bai taɓa yi mata haske da annuri kamar na wannan lokacin ba.

Suna haÉ—a ido gabansa ya faÉ—i sosai, ya daure cikin dakiya da dauriya ya ce, "Mama Baffa yana ciki?."

Mama ta girgiza kai tana ƙwafa ta ce, "Saheer yanzy kenan ka zaɓi tsinuwata akan ka rabu da Islaha? Ka amince na tsine maka ka bi duniya akan ka rabu da ita ko?." Saheer ya sunkuyar da kai bai ce komai ba, amma ƙirjinsa har ɗagawa yake yi saboda tashin hankali, ya rasa me zai yi.

Mama a fusace ta ce, "ina magana ka sunkuyar da kai kamar wani mutumin kirki, ka zaɓi na tsine maka akan a fasa auren nan ko!?."

"Ya zaɓi yiwa mahaifinsa biyayya ne, dan kin tsine masa babu abinda Allah zai yi masa, dan ba wani abun mara kyau ya aikata ba!" Baffa ya faɗa yana shigowa yana kallon ta.

Mama ta sake fusata matuƙa ta ce, "Bazan amince da auren nan ba wallahi, bazai yu na haifawa wata banzar yarinya ɗana ba. Tun yanzu yana rawar ƙafa da rawar kai a kant, ina ga an yi auren?. Wallahi Allah, In Saheer ya auri yarinyar nan sai na tsine masa alabrka!."

Baba Yayan Baffa da yake tsaye, sun shigo tare É—aukar goro da alewaya ce, "Subahanallahi! Me ya yi zafi haka?."

Baffa ya ce, "ni kuma sai na aura masa Islaha a yau, in kin tashi tsinuwar ki haÉ—a har ni ki tsine, amma babu abinda zai dakatar dani daga bawa Islaha auren Saheer a yau."

Mama ta girgiza kai ta ce, "Mu zuba mu gani" ta faɗa tana fita cikin takaici da ɓacin rai.

Baba ɗan uwan Baffa ya kalli Baffa ya ce, "Hakan bai kamata ba Mustpaha, kar a yi abinda za a zo ana danasani. Tunda har ta yi wannan furucin akansa, ka yi haƙuri a bari zuwa gaba, kar a yi abinda zai lalata rayuwar Saheer. Uwa ce, ko ya ta yi nasa bakin sai ya bi shi, in aka bari ta furta, duk ƙanƙantar abinda ta furta sai ya taɓa rayuwarsa."

Ran Baffa a ɓace ya ce, "saboda ita sai na fasa abinda na yi niya kenan?."

"Ba saboda ita zaka fasa ba, saboda shi zaka fasa. In aka yi auren ta tsine masa wa gari ya waya? Kwata kwata baza a ga albarkar auren ba, tunda akwai tsinuwar uwa a cikinsa. A bi komai a hankali, islaha matarsa ce in sha Allah, amma a bari a daidaita komai sai ayi auren."

Baffa ya sauke numfashi ya ce, "Itace zata juya ni kenan?."

Baba ya dafa Baffa ganin ya fusata da yawa, daga ganin yadda ya fusata ya san an kai shi bango, dan Baffa ba mutum ne mai saurin ɗaukar zafi ba, tunda ya ga ya fusata sosai ya san abin ya taɓa ransa.

Ya ce, "ba juya ka ta yi ba, hankali da nutsuwa ka fita. In aka yi auren nan rayuwar Saheer a gaba za ka duba, tsinuwar uwa ai ba abin wasa bane. Kai ka fita hankali, bai kamata ka biyewa zuciya shaiɗan ya zuga ka ba. A yi haƙuri, abar maganar ɗaurin auren nan a yau, in Allah ya kaimu lokaci sai a yi, amma yanzu a dakatar dashi."

Baffa ya ce, "Baza a fasa auren Saheer da Islaha ba, bata isa ta saka na fasa abinda na yi niya ba, akan Zulaiha bazan fasa aurawa Saheer Islaha ba. Akan auren Saheer da Islaha, zan iya sakin Zulaiha!."

Nana Haleema.
[7/17, 11:50 AM] KRBBK: RDB2P62
Nana Haleema.

Saheer ya kalli Baffa da sauri jin abinda ya ce, Baba ya kalli Saheer sannan ya kalli Baffa ya ce, "Haba Mustapha, wannan wacce irin magana ce mara kan gado?. Zulaihan za ka saki??."

Baffa ya ce, "A kanta aka fara?."

"Ba a kanta aka fara ba, kuma ba a kanta za a gama ba. Shi kansa Saheer ɗin ya kalle sa ka gani, ai bazai so ace ta silar aurensa auren mahaifiyarsa ya ƙare ba. Shaiɗan ne yake zuga ka, ka kwantar da hankalinka, Allah zai nuna mana gaba." Baffa ya shiga ɗaki bai ce komai ba.

Baba ya riƙe hannun Saheer suka fita daga falon, dan ya ga yadda Baffa ya fusata sosai bazai yi magana a gabansa ba.

Baba ya kalle Saheer ya ce, "ka yi haƙuri ka bar maganar, zuwa gaba sai ayi auren ai ba gagawa ake yi ba. Na san baza ka so auren babar ka ya lalace saboda auren ka ba."

Ya É—an É—aga kai ya ce, "haka ne Baba, Allah ya kaimu lokacin."

"Amin. Ka cigaba da yi mata biyayya, ka cigaba da tausarta har ta amince da auren. Kar ka yi abinda bata so, kar ka yi abinda zata yi maka baki a kai, dan baza ka ji daɗinsa ba. Ka cigaba da addu'a, in alkhairi ce Allah ya zaɓa maka, sannan ita ya saka mahaifiyar ka ta amince, in ba alkhairi bace Allah ya canja maka da mafi alkhairi." Ya amsa da amin suka nufi masallaci don yin sallar juma'a.

A gidansu Safeera ƴan uwan Baba mata suna nan, dan ranar za a ɗaura auren Baba kuma ranar zata tare. Suna gidan sun zo karɓar amarya, dan ba ƙaramar murna suke yi da auren ba. Ita kanta Safeera tana murna da auren, dan tana son kwanciyar hankalin mahaifinta sosai.

Daga cikin falon Umma suke zaune, Gwaggo Yayar Baba ta ce, "ni na ji daÉ—in haÉ—in nan wallahi, ko babu komai Maimuna zata san ta tafka kuskure, inda ta bari saboda abin duniya aminiyarta ta shigo."

Ɗaya daga ciki ta ce, "Maimuna bata da matsala fa Gwaggo, matsalar ta ɗaya, shine zaɓar abin duniya akan yaranta da mijinta da ta yi, itace matsalar da aka samu da ita. Amma bayan wannan tana da kirki kowa ma ya shaida."

Ɗaya ta ce, "Kuma na ji labarin an ce wahala take sha a can ƙasar, duk ga rame ta damu ta dawo."

Gwaggo ta cs, "To ko haƙƙin mai gidan nan zai barta ne? Barin auren ta yi ta tafi wata ƙasa aiki, ai ko wuƙanata aure da ta yi sai Allah ya hukunta ta. Yanzu ga amarya zata shigo, Kowa yana yabon halin Atika na kirki da dadtaku. Na ji daɗi wallahi, Allah ya saɓa halaye." Suka amsa da amin suna cigaba da tattauawa.

Safeera tana ɗaki duk tana jinsu, bata ji rashin jin daɗi ba kaɗan, dan ta san gaskiya suka faɗa ba ƙarya ba, da Umman bata aikata ba da hakan bai faru ba. Sai da ta ji dawowar Baba, su gwaggo suna ta yi masa Allah ya sanya alkhairi da addu'a sannan Safeera ta yi murmushi, ta ɗauki waya ta kira Islaha.

Islaha tana kwance akan gado, lokacin la'asar ya kusa a Saudi, tana jiran kiran Saheer amma shiru. Jin kiran Safeera sai ta tsorata, ta miƙa hannu a sanyaye ta ɗauko wayar daga gefenta ganin Safeera ce sai ta ɗauka.

Islaha tana saka wayar a kunne Safeera ta ce, "Islaha an É—aura auren."

Ƙirjin Islaha ya buga dummm, ta ji wani irin abu zuuu yana yawo a jininta, ta ji wani shock kamar jan wutar lantarki, wani irin ɗumi mai kama da zazzaɓi yana lulluɓe ta, zuciyarta ta tafi tunanin yanzu kenan ta zama matar Hamma? Ta zama mallakin Hamma halak malak, ta zama matarsa ta sunnah, ko yanzu akace babu shi sai ta yi masa takaba?. Sai ta kasa magana, bakinta ya yi nauyi sosai, ta riƙe waya a kunne tana jin sautin bugun zuciyarta a kunnenta. Bawai auren Hamma ne bata so ba, gaggawar da aka yi a ɗaura auren ne bata so.

Safeera da zumuÉ—i ta ce, "Yanzu Baba ya dawo, an É—aura aure yau."

Islaha ta ja numfashi mai ƙarfi bata ce komai ba, Safeera ta ce, "Ya dai?."

Islaha ta ce, "Nima ban sani ba Safeera, haka kawai nake jin bana murna da auren."

Da mamaki Safeera ta ce, "meyasa bakya murna?."

"Wallahi ban sani ba, ni kaina bazan ce ga dalili ba. GabaÉ—aya ji nake kamar a warware auren nan, bazan iya zama da aure a kaina ba."

"auren Baban?."

Islaha ta buɗe ido tana miƙewa zaune ta ce, "Wanne Baba kuma?."

Safeera ta ce, "ke akan auren wa ki ke magana?."

Islaha ta ce, "Shekaran jiya Baffa ya kira ni, ya ce za a É—aura aurena da hamma a yau, dan É—azu ma ya kira ni akan hakan, yana ta shirin tafiya masallaci za a É—aura. Shine gabaÉ—aya jikina ya yi sanyi, ko ke na kasa faÉ—awa maganar É—aurin auren."

Safeera ta ce, "tabɗi! Wai da sai dai na ji an ɗaura auren ki? Na rantse da Allah sai na yi miki abinda ba ki taɓa tunani ba."

"Wallahi ni nauyi maganar ta yi min, sai nake ji gabaÉ—aya bana son a yi aurensa yanzu, bana murna da auren gabaÉ—aya."

"Auren Hamman ne bakya so ko son Hamman ki ka daina?."

"Ina da wanda zan so in ba shi bane? Ina son Hamma sosai, kawai dai aurensa a yanzu ne bana so."

Safeera ta ce, "Yanzu an É—aura auren?."

"Ban sani ba wallahi, amma tabbas yau za a É—aura sai dai in an fasa."

"to meyaasa za a yi auren yanzu?."

"ina zan sani? Baffa ne ya yanke hukunci."

Safeera ta yi dariyar shaƙiyanci ta ce, "ki ce amarya ce da kanta, tunda an sakko daga masallaci na san kin zama matar aure."

Islaha ta ce, "hmm Safeera kenan. Baba ya auri Mamansu Kausar ko?."

"Wallahi fa, an É—aura auren."

"Ke kamar bakya ta ya Umma kishi."

"Kishin me zan ta ya ta? Ba fa matar Baba bace."

"Amma Maman kausar aminiyar Umma ce, komai tare suke yi. Dan kawai Umma bata nan sai ta aurar mata mijinta maye gurbinta?. Ni fa haushin ki nake ji akan hakan, sai rawar kai ki ke yi."
Chapter 86 · 0% Book details