← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 133

Sashe 61

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babban meeting room ne mai É—auke da table da kujeru masu yawa, su bakwai ne a zaune a ciki, har wanda ya fita bakwai, ko wanne sanye da transilater a kunnensa dan wani baya jin turanci.

Rehaan yana tsaye a jikin kujerar CEO, yana kallon wani da yake tsaye tsaye shima yana abinda za a yi a projector.

Tana shiga duk suka zuba mata ido, har shi Rehaan ɗin sai da ya juyo yana kallon ta, kafin ya ɗauke kai yana jira ta ƙaraso.

Gajiya kallon nasu ta yi ta tako ciki a hankali, suna ganin uniform É—inta suka san housemaid ce, amma duk da haka kallon ta suke yi.

Wani irin sanyi ɗakin yake yi, ita bata san meyasa suke saka ac mai hawa kai haka ba, sanyi zaka ji kamar ka buɗe fridge, sanyi mai ratsa ƙwaƙwalwa da ƙasusuwan jiki. Haka gidan Maleek yake, kamar ka shiga cikin ƙanƙara.

Sanyin ya buge ta, ta ji kamar numfashinta zai ɗauke, ta ƙarasa a hankali ta ajjiyewa kowa a gabansa. Bata ce komai ba sai su da in ta ajjiye zasu ce sun gode, Allah Allah take ta bar wajan kafin ta samu attack, dan sanyin ya yi mata yawa sosai, yanzu numfashin ta zai fara sarƙewa, ƙirjinta ya fara ciwo.

Tana gama ajjiye musu da sauri ta juya ta fita daga wajan, ta tsaya a falon da yake da ɗumi tana sauke numfashi har ta ɗan nutsu snanan ta sauka ƙasa a hankali tana sake ƙarewa ko ina na gidan kallo.

Tana shiga kitchen kiran Hajiya Shafa ya shigo wayarta, ta É—auka ta saka a kunne da sallama, jin Hajiya Shafa ta fara larabci sai ta ce, "Sunana Islaha, don Allah ina so ki haÉ—a ni da Hajiya Maimuna da ki ka kai wajan aiki. Tare mu ka zo nan da ita, ni Æ´arta ce, ina garin Jeddah, tunda mu ka zo bamu yi magana ba."

Hajiya Shafa ta ce, "Shikenan, zan haÉ—a ku in na shiga wajen ta." Islaha ta yi mata godiya ta kashe wayar.

Islaha ta yi ajiyar zuciya tana kallon kitchen ɗin har lokacin ƙhamshin tea ɗin yake yi, ga ƙhamshin turarensa da ya cika ko ina.

Hijjab É—inta ta mayar, ta fito falon kenan shi kuma ya sakko yana amsa waya kamar baya so, tafiyar ma a hankali yake yu kamar mara lafiya, komai nasa a sanyaye kamar nata laka.

Islaha ta yi kamar bata gan shi ba, har zata wuce ta fita ya ce, "go and take the used cups from the meeting room, then go into my bedroom and clean it up."

Islaha wani juyo ta kalle sa, sai ta ga shi ba ita yake kallo ba, wani wajen daban yake kallo kamar ba shine ya yi magana ba. Ta maimaita gyara masa É—aki a ranta, ta bi sa da kallon up and down har ya É—ago ido suka haÉ—a ido, ya sake É—auke kansa daga kallon ta.

Islaha ta ce, "ba fa baiwa bace ba ni, girki aka ce zan dinga yi ba aikin gyara É—aki ba."

Bai kalle ta ba balle ta saka a ranta ya ji me ta ce, ko kaɗan bai nuna mata alamun ya ji ba, shiyasa bata yi tunanin ya ji ɗin ba. Islaha ta ce, "ban san ƙaddarar da ta sake haɗa mu yanzu ba, na so sai wani lokacin ba wannan ba. Na so sai lokacin da zan nuna maka kuskuren ka muka haɗu, na so sai lokacin da zaka yi danasani sannan zamu haɗu da kai. Amma yanzu ma bata ɓaci ba, zaka san wacece Islaha."

Rehaan tsaf ya gano wacece, yana kuma jin duk abinda take faÉ—a, yana murmushi a ransa dan shi baya yi mata kallon mai hankali. Daman shi tun a Yola ya lura kamar bata da hankali, yanzu da ya ganta a Jedda ya tabbatar da babu hankalin ko kaÉ—an, dan gashi nan sai magana take yi ita kaÉ—ai babu mai ta ya ta. Bai damu da tunanin abinda ya kawo ta Jeddah ba, ko kaÉ—an bai ji yana wannan tunanin ba, dan ko a jikinsa rayuwarta ce ba ta sa ba.

Maimakon ya kalle ta sai ta ji yana waya ya ce, "Mamy i'm so tired, i need rest."

Yadda ya yi maganar ya bawa Islaha mamaki, ta bisa da kallo jin yadda yake shagwaɓa kamar yaro ƙarami. Kai ko ƙaramin yaro baya irin wannan shagwaɓar, sai wani narke fuska yake kamar mai. Babban abin haushin ma wai ya gaji, ko me ya yi da ya gaji oho masa.

"Mamy I've been in a meeting with a guests for 30 minutes."

Islaha bata san ta buÉ—e baki ba ta ce, "ji wai minti talatin, ai daga ganin rariya ka san zata zubar da ruwa. Kallon farko da nayi masa nasan wannna maza ya rako duniya. Gashi nan kamar ruwa, sai aukin kwanciya. Wannan in waje É—aya muke wata ran sai na yi masa dukan tsiya, bazan iya É—aukar wannan abubuwan ba" ta faÉ—a tana kallonsa.

Rehaan ya tsaya da wayar ya kalle ta, shi fa ta fara bashi tsoro, dan ya fara tunanin mahaukaciya ce. In ba mahaukaci ba waye zai dinga magana shi kaÉ—ai? Har yana faÉ—a yana nuni da hannu.

Suna haÉ—a ido ita ya ce, "what are you waiting for?."

Ƙasa-ƙasa ta ce, "takaici nake ji in ina kallon ka, nan ba Yola bane balle ka hanani fita" ta faɗa tana wuce sa ta hau sama. Ya kalli inda ta bari ya ɗauke, kai kafin ya fita daga falon gabaɗaya.

Islaha tunda ta shiga meeting room É—in take ta mita, "Aikin banza, wai ya gaji. Gaskiya na jima ban ga ragon maza kamar wannan ba. To daman wannan me zai tsinana? Abu kamar fulawa saboda laushi. Mtsw! Haushin namiji mai yanayin mata nake ji, shiyasa na tsani wannan mutumin da ko sunansa ban sani ba."

A haka ta kwaso cups É—in ta ajjiye a falo, ta shiga tunanin ina ne kuma bedroom É—in nasa da ya ce ta shiga.

Ta ja tsaki ta bi hanyar corrior ta buɗe ƙofar farko ta shiga. Ƙhamshi mai sanyi ya shiga hancinta, ta dinga takawa a hankali kamar mai jin tsoro dan ta ɗauka wani falon ne saboda girman ɗakin.

"ma sha Allah!" ta furta tana kallon É—akin cikin yanayi na burgewa.

"Wow!"

Ta furta lokacin da ta juya bayanta ta ga lafiyayyen ocean kana hangonsa ta glass.

Ta taka a hankali tana kallon wajan ganin mutane suna ta harkokinsu a waja, ga ruwan mai daÉ—in kallo.

Islaha ta ce, "gaskiya ya yi kyau sosai wajan nan, ya burge ni."

Sai ta bar wajan tana kallon ɗakin, ita bata ga me za a gyara ba, duk da komai na ɗakin fari ne amma babu alamun dauɗa, komai neat. Ta ƙarasa ta ɗauki cups guda biyu, sai kuma ta haɗe rai ta ce, "ɗauke cup ɗin ma bazai iya ɗauka ba, mtsw! Me ake da ragon namiji don Allah."

A haka ta sakko tana ta masifa akan abinda bai shafe ta ba, ta shiga da cups É—in ta wanke su ta goge sannan ta mayar dasu wajansu.

Ta fito daga kitchen É—in ya sake shigowa falon still waya yake yi.

Bata kalle sa ba, zata wuce ta fita kenan ta ji ya murza yatsunsa sun bada sauti alamun yana yi nata magana.

Islaha saboda ƙarfin hali sai ta yi banza kamar bata san da ita yake ba, gab da zata ƙarasa wajan ƙofar ya ajjiye wayar ya ce, "ki dawo, ki haɗa min loaded fries irin na jiya."

"Kan bala'i! Wai wannan mutumin me ya mayar dani ne?" Ta faÉ—a a hankali tana juyowa a fusace.

Karaf suka haɗa ido, sai ta ji gabanta ya faɗi dan gabaɗaya ya zaro idonsa a kanta yana kallon ta. Duk da faɗuwar gaban da ta ji tsiwar tana nan bata saduda ba, zata yi magana ya miƙa mata kuɗi ya ce, "take it."

Ta harari kuɗin kamar baza ta je ba, shi kuma ya zuba mata ido yana so ya ga ƙarshen gudun ruwan yarinyar nan. Ya ɗan kalle ta ta ƙadan ido, ya ga ta ja ta tsaya tana hararar gefe. Sai ta bashi dariya, ya ɗan murmusa dan da gaske baya yi mata kallon mai hankali, so yake ya ga zata karɓi kuɗin ko baza ta karɓa ba.

Nana Haleema.
[7/7, 10:22 AM] KRBBK: RDB2P42
Nana Haleema.

_Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments É—in ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link É—in ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode É—in baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/S0HoWfmkTOI?si=vJKdn7h8rPpmDhS5

•••••••••••••

Islaha ta juyo ta kalle sa, suka haɗa ido ta ɗauke ido, ta ɗan yi ajiyar zuciya sai kuma ta tuna aiki nake yi saboda ki biyasa kuɗinsa, ta rarrashi zuciyar ta ta ƙarasa ta karɓa. Ya wani kalle ta ganin ta karɓa, ya yi tunanin rashin jin ta ya kai ta ƙi karɓa.

Riyar dubu bakwai ta gani a hannunta, daga zaman ta a ƙasar zuwa lokacin tana fahimtar kuɗin ƙasar sosai, farin ciki ya mamaye zuciyarta, ganin ta fara tara kuɗin da ta zo nema. Dan kuɗin da ya bata masu yawa ne sosai, a kuɗin nigeria sun tafi miliyan biyu da wani abun, amma a ƙasar kamar dubu bakwai suke, duk da kuɗi ne masu daraja ko a can ɗin, dan zaka yi siyayya mai matuƙar yawa.

Lokaci É—aya fuskarta ta washe, farin jinin zaya sauke nauyin bashi ya mamaye mata zuciya, ta É—an ja baya daga wajan ta ce, "na kusa biyan bashin da na É—auko in sha Allah, da na tara na biya sa zan kama gabana ka koma gida, nima na gaji."

Bayan ta gama bayaninta sai kuma kalle sa ta ce, "Thanks."

Hannunsa ya ɗaga mata kawai bai ce komai ba, ta harare sa ta ce, "ɗan wulaƙanci, zan rama ne."

Ta wuce ciki ya bita da kallo bayan ya É—an tafi tunani, indai ba tana da matsala ba to gaskiya daman mahaukaciya ce. Bai amince da lafiyar ta ba, dan mutum mai lafiya bazai dinga magana sakaka haka ba.
Chapter 61 · 0% Book details