← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 133

Sashe 70

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Alhamdu lillah! Ina ki ka shiga kwana biyu? Wayar ki bata zuwa sam sam."

"Na É—an yi tafiya ne, kuma zan É—an kwana biyu."

"Zuwa ina kenan?."

Ta ɗan yi jim sannan ta ce, "ina ƙasar Saudia, a garin Jeddah."

"Lallai Islaha, shine ko a faɗa min? Ko a waya ki ce min zaki yi tafiya ki ka ƙi?."

"Tafiyar ce ta zo bazata wallahi, shiyasa ban faÉ—a maka ba."

"Allah ya taimaka."

"Amin. Ina son magana dakai ne" ta faÉ—a tana katse maganar zuwan Jeddah.

Suraj ya fahimta hakan ya saka ya ce, "ina jin ki."

"zan tura maka wani recording yanzu, in ka ji sai mu yi magana."

Ya amsa ta kashe wayar ta tura masa, sai da ta tabbatar ya gama ji sannan ta kira sa.

Yana É—auka ya ce, "na ji Islaha. Hakan yana nufin zargin ki gaskiya ne ko?."

Ta sauke numfashi ta ce, "har yanzu bamu kama su red in hand ba, ka ga baza mu tabbatar ba. Shiyasa na tura maka ka ajjiye, kaga haka aka goge hotunan Hafsa a wayata, shiyasa zan tura maka kaima ka ajjiye min wanann."

"Hakan ya yi kyau. Yaushe za ki dawo? In baki dawo an yi komai ba rayuwar Zainab zata iya lalacewa."

"Shiyasa na tura maka, na san zaka yi komai ko bana nan. Don Allah Hamma ka bincika, ka tabbatar ka fitar da maganar nan ta je kunnen gwamnati, don Allah ka taimaka min."

"Eslaha ai ko baki faɗa ba zan yi, nima a gidan na tashi, duk wani ɗan gidan ɗan uwana ne. Amma kin san sai an haɗa hujjoji masu ƙarfi kafin a kai ga tuhumar su."

"Zan yi ƙoƙarin haɗa wani abun daga nan, sannan kaima ka taimaka min ka yi wani abun daga inda ka ke."

"Baki da matsala, in sha Allah i will try my best."

"Na gode Hamma, na gode sosai."

"My pleasure. Kin wuce komai a wajena."

"Sai na ji ka."

Daga nan suka yi sallama ta kashe ta kira Hamma Saheer. Shima irin bayanin da ta yiwa Suraj ta yi masa, ta tura masa recording ɗin just for evidence, ta ce ya ajjiye ko da na wajen ta zai ɓata. Bayan sun gama waya ta yi shiru tana tunani, bata taɓa jin hankalinta ya yi gida ba sai yanzu, gabaɗaya zaman Jeddah ya fita daga ranta, hankalinta ya yi kan Zainab, tana so ta san asalin abinda yake faruwa....

Mu je zuwa🤭😂
[7/10, 11:05 AM] KRBBK: RDB2P49
Nana Haleema.

Mamy da Mummy suna zaune a falo suna hira cikin raha da wasa da dariya kamar yadda suka saba. Mummy ta ce, "yaushe Rehaan zai dawo ne?."

Mamy ta É—an yi murmushi ta ce, "wani lokacin dawowar ta sa babu notice, sai dai kawai ki gan sa."

Ta yi dariya ta ce, "Ya batun aurensa da Daada zata yi masa? Yana nan ko kuma an fasa?."

Mamy ta taɓe baki ta ce, "Yana nan, babu batun fasawa. Kuma ko, wallahi dani dashi duk ba ma son auren nan, shi kansa Abban ba son yake yi ba, kawai dan babu yadda zai yi da mahaifiyarsa ne shiyasa. Amma kwata kwata babu mai goyan bayan auren nan."

Mummy ta ce, "to wannan aure waye zai so shi? Aure ba a san mata ba ai dole baza a so ba. Amma wataƙila sai ki ga ya zama alkhairi."

"ina wani alkhairi? Ni wallahi bana so, shi ba ya so, babansa ba ya so, ta ya zai zama alkhairi?."

"Ba ki san me Allah ya ɓoye ba, wataƙila ta zama matar so a gare sa."

"Bana wannan tunanin Mummy, Rehaan bazai taɓa son yarinyar da za a bashi ba. Saboda ya san bana so, shina kuma baya so ɗin.

Mummy ta yi dariya ta ce, "To yanzu ya za a yi?."

"Ba dan na ga idon ki ba ko, amma ni Ikram nake yi masa sha'awar ya aura. Na san halinta, itama ta san na sa, na san ba dan kuÉ—i ko É—aukakar da yake da shi zata aure sa ba."

Mummy ta yi murmushin jin daɗi, tana ganin kamar maganin damuwar Ikram ya zo. Mamy ta ce, "To kin san mutumin na ku, ya ƙi, wai shi kallon ƙanwa yake yi mata bazai iya aurenta ba. Ranar da zai tafi Jeddah sai da muka yi maganar, Amma Rehaan ya ce shi dai kallon Riyya yake yi mata, bazai iya auren ta ba.

Mummy ta murmusa ta ce, "haka halinsu yake shi da Jafar, Jafar É—in ma ai haka yace, amma daga baya ya canja, ya zo ya ce shi fa Riyya yake so, gashi kwanaki kaÉ—an ya rage."

"Haka nace masa, sai cewa ya yi shi ya ga zai iya auren ƙanwarsa, amma shi bazai iya ba. Amma har cikin raina ina yi masa sha'awar auren Ikram sosai."

Mumny ta yi murmushi cikin jin daÉ—i ta ce, "sai mu dinga addu'a, duk abinda ya kasance alkhairi Allah ya tabbatar mana. Itama wannan É—in bamu sani ba ko tana da nata alkhairin."

Mamy ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Haka ne. Amma ko ya aure ta akwai zaɓina da zai aura, ina so ya samu kwanciyar hankalin da ya rasa a cikin gidan nan. Kuma ni a ɓangarena ban amince da ko wacce yarinya kamar Ikram ba, akwai mata kala kala da ake kawo min na haɗasu, haka ɓangaren mahaifinsa da ƴaƴan abokansa, dana ƙawayena, dana ƴan uwa kamar sun gaji da yaransu."

Mummy ta yi dariya ta ce, "ba gajiya suka yi da yaran ba, Rehaan É—in ake kwaÉ—ayin samu."

"Akwai wata ƙawata da za ki ji su Ikram suna ce mata Ammi, matar former deputy gov of Adamawa state. Tana da ƴa mai suna Zuhra, age mate ɗin su Riyya ce, ko zata girmi su Riyya da kaɗan ne. Ammi ta dage akan a haɗa auren ta da Rehaan, har deputy gov sai da ya yiwa Abba maganar."

Mummy ta ce, "shiyasa na faÉ—a miki, kwaÉ—ayin Rehaan É—in ake yi."

Mummy ta girgiza kai ta ce, "Ni kuma bazan bada goyan baya ba, dan ina son wacce zata zauna dashi tsakani da Allah, ba dan yana da kuÉ—i ba."

Mummy ta ce, "Allah ya zaɓa abinda ya fi zama allhairi." Ta amsa da amin suka cigaba da tatttaunawa, Mummy dai bata faɗa mata ƙudurin Ikram akan Rehaan ba, amma ta ji daɗin abinda Mamy ta ce, da alama haɗin zai iya yuwa nan gaba.

Bayan Mummy ta tafi Mamy ta kira Jafar a waya, yana É—auka ta ce, "Jafar ya aiki?."

Daga cikin wayar ya ce, "Alhamdu lillah Mamy. Ina yini?."

"Lafiya lau, kana lafiya?."

"Lafiya lau."

"Za ka shiga Jeddah wajan Rehaan ne?."

"Yes Mamy, ina tunanin cikin week É—in nan zan je in sha Allah."

Mamy ta sauke nuɓfashi ta ce, "Jafar da gaske har yanzu babu macen da Rehaan yake so da aure? I mean so na aure?."

Ya É—an yi murmushi ya ce, "Gaskiya babu."

Ta ce, "ka tabbatar?."

"i'm very much sure Mamy."

Ta sauke numfashi ta ce, "ina da wacce nake so na zaɓa masa, bana so ya ga kamar na takura masa ne, shiyasa na tambaye ka in akwai na sani kafin na kai ga furtawa."

"Babu kowa Mamy, da akwai da zan sani, kuma zan faÉ—a miki. Sai dai akwai wata baturia Alma, ta dage sosai akan sai ta aure sa, yarinyar nan zata iya yi masa komai dan ta mallake sa."

Mamy ta yi tsaki ta ce, "i'm here for him, ina faÉ—awa Allah ya basa kariya a ko yaushe, babu wata baturiya da zata yi tasiri a kansa in sha Allah."

Jafar ya ce, "in sha Allah."

"Mamy ta ce, "Jafar ina so Rehaan ya auri Ikram."

Da mamaki ya ce, "Ikram Mamy! Which Ikram?."

"Your junior sister."

"Ikram!" Ya maimata cikin mamaki.

Mamy ta ce, "ba na faɗa maka a matsayin ka na yayan Ikram ba, ina faɗa maka ne a matsayin ka  na abokin Rehaan kuma ɗan uwansa. Ina so ka yi convencing Rehaan akan Ikram, ka saka ya sota har ya amince da auren."

Jafar ya ce, "Mamy ba ƙi bane, amma Rehaan bazai amince ba, ko yaushe a ƙanwarsa yake kallonta."

Mamy ta ce, "munafurci ne fa, kaima haka ka dinga faɗa sai gashi Riyya she is your fiancés. Kuma kai dashi duk bakin ku ɗaya, abinda ɗaya ya yi shima ɗaya zai yi."

Ya yi ƴar dariya ya ce, "Mamy a wannan ɓangaren Ray bazai hau layina ba, bashi da ra'ayin auren cousin sisters at all."

"Ka saka shi ya yi ra'ayi. Ka san ba son auren nan na wajan Daada muke yi ba, kawai an fi ƙarfinmu ne. Dan haka nake so na haɗasa da wacce in ya aure ta zai zai samu peace of mind. Bana so Rehaan ya sha wahala bayan wacce yake sha a yanzu, ina so ya samu kwanciyar hankalin da ba ya samu in ya zo ƙasar nan. Kuma ni kaf garin nan ban ga wacce na yarda da ita kamar Ikram ba. Zata so shi tsakani da Allah, zata kula dashi, zata bashi duk wani abinda ya rasa a gidan nan. Shiyasa na kira ka dan ka taimaka min."

Jafar ya sauke numfashi ya ce, "Shikenan Mamy, in sha Allah zan yi abinda zan iya. Amma ninety percent out of hundrend bazan amince ba, ten É—in shine amincewarsa."

Mamy ta ce, "ka dai gwada É—in, na baka dama."

Ya yi murmushi ya ce, "in sha Allah." Daga nan suka yi sallama Mamy ta kashe wayar.

Mama tana zaune a falon Daada suna tattaunawa akan binciken da ta saka ta yi mata akan Islaha. Daada ta ce, "ina jin ki Saddiƙa, wanne bincike ki ka yi?"

Mama ta gyara zama ta ce, "Daada akan yarinyar da Rehaan zai aura ne."

Daada ta washe baki cikin jin daÉ—i ta ce, "to me aka gano?."

Mama ta murmusa ta ce, "Ai Daada baza ki taɓa zaɓo abu mara kyau ba, Allah ya yi miki baiwar da ba kowa ya yiwa ita ba. A kan ido kawai, kina fahimtar abinda yake daidai da ba daidai ba."
Chapter 70 · 0% Book details